Chapter 68
Chapter 68
ya kamata ya fad'a mata nan yace mata sunan shi Amadu. Tashi tayi zuwa bedroom d'in su ganin Gwaggo Aisha ta ishe ta da waye ya kira ko Zafar ne? Da kai kawai ta amsa mata ta karasa shigewa daki ta barta tana ta murna. ***************************** Da daddarem ma kin girkin girka komai nayi na kwanta Ina kallon wani series da nake matukar so a zee world ya shigo min da sallama na amsa mishi ciki-ciki kaman yanda shima ya min, tsaye yayi kaman me son cewa wani abu ko me neman wani abu ni dai bance mishi kala ba na mayar da hankali na kan tv. "Ya jikin naki?" Naji muryan sa kaman daga sama. " Na warke" na bashi amsa ba tare da na kalli inda yake ba. Bai kara cewa komai ba ya fita nabi bayan shi da harara, a raina ina wa zai kara kula ka kaci zalin shi ko ka mishi mugunta da ka saba. Shirin bacci na nayi bayan na gama kallon, na sha bacci cikin kwanciyar hankali sab'anin Zafar daya kwana cikin wani yanayi da shi kan shi ba zai ce ga inda ya dosa ba shi dai kawai so yake ya zauna kusa da ni ko kuma inda zai samu yayi ta kallo na, tun yana d'aukan abin da sauki har ya fara jin haushin kanshi wai me yasa ya damu da wani lamura nane? in ya kalle ni uban me zan bashi illa ma in b'ata mishi rai da sabon rashin kunya da na samo, bayan wannan ma tun lokacin da ya d'auke ni ya fito dani parlor jiki na da nashi da ya had'u yake kewar d'umin jiki na tare da kamshin jikina mai sanyi da tsayawa a rai sai dai dole ya matse gudun kada raini ya shiga tsakanin mu. Ya san bakomai yasa ya damu da lamurana ba maybe tausayi na da ya fara jine kawai dan yaji bani da lafiya, " hakane ma" ya furta a sarari yana mai kara bawa kanshi karfin guiwa da kyar dai ya samu bacci yayi nasaran sace shi a wannan daren. Da washe gari na tashi da sauki dan wannan nauyin da zuciya ta yayi jiya yayi sauki hakan ne ya bani daman fara aiyuka na kaman yanda na saba, bayan na gama share ko ina tass na gyara sannan na shiga wanka ban dad'e ba na fito light make-up nayiwa fuskata na shirya kaina cikin English wears riga da skirt pink color anyi mishi ado da flowers blue hakan yasa na yane kai na da blue vail, kayan bai wani matse ni ba amma ya zauna das a jikina ya min kyau sosai. Zagewa nayi ina girki sanin cewa Hajara zata iya zuwa at any moment,kayan dad'i nake dafawa dan haka gidan ya cika da kamshi masu dad'in shaka,kamshin nan shi ya fito da Zafar daga d'akin shi sai bud'e hanci yake yana lumshe ido tsohon yunwar shi ta jiya na dawowa sabo fil. Kofar kitchen d'in yazo ya tsaya yana kallon yanda nake aiki gaba daya hankalina yana kan aiki ban san ma da zuwan shi ba,shi kuma controlling d'in kan shi yake akan abinda zuciyar shi take ingiza shi ya aikata dan ji yake kaman yaje ya rungume ni yaji wannan d'umin jikin nawa da wannan daddadan kamshin mai sanyaya zuciya amma ya daure yayi gyaran murya Wanda ya d'an firgitani na juyo a d'an razane na ganshi tsaye cikin kayan baccin sa farare kal da alamu tashin sa kenan ko wanka baiyi ba. Kaman ana min dole nace mishi" Ina kwana" saboda ganin babu wasa a fuskar shi, maimakon ya amsa min sai cewa yayi " ki tabbata kinyi da rabon masu aiki tunda kin samu lafiya" sai da na turo baki sannan na bashi amsa da cewa " ni bada su nayi ba dan Hajara zata zone shiyasa nayi girkin". Kara had'a fuska yayi yace" try anything stupid and see"Yana gama fada ya juya ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba, " zaka gani kuwa ai ka daina cin abinci na a gidan nan tunda kai d'an wulakanci ne"nace ina cigaba da aiki na. Bayan kaman 30 minutes na kammala komai na jera su kan try na fito na wuce parlour na ba tare da nabi ta kan shi da na gan shi zaune a main parlour ba, shirya su nayi anan tsakiyar parlour na tare da kara saka turaren wuta na dawo inda na shirya kayan abincin kenan sai gashi nan ya shigo da fuska kaman an aiko mishi da sakon mutuwa. "Ina na masu aikin da na gaya miki?" "Banyi dasu ba na amsa mishi ina kara gyara zamana a gaban warmers d'in, bai saurare ni ba direct kai tsaye ya karasa shigowa da niyyan zai d'auke warmer d'aya, cikin azama na kai hannaye na duka biyu na rungume su a kirjina tare da turo baki ina " ni wallahi ka bar min kayana". Bai saurare ni ba yana zuwa yasa hannu ya d'agani cid'ak kaman wata karamar yarinya zai ajiye ni a gefe na rike shi gam ina "wallahi ba zaka d'auka min ba ni banyi da rabon ka ai na san cewa kai kake cinyewa ba wasu masu aiki da kake bawa". Yanayin yanda na cukuikuye shi na rike sai ya haifar mishi da kasala kuma dama abinda tun jiya zuciyar shi ta kwad'aitu da shi kenan,da gangan yayi fara kiciniyan kwace kan shi ni kuma ina kara rike shi akan ba zai d'auka ba kan kace me kokuwa ya kaure tsakanin mu anan yayi amfani da wannan daman hannayen sa babu inda basu je ba a jiki na, ni kuma a hauka na ban kawo komai a raina ba na zata duk cikin kokarin kwace kan shi yake a hannu na. Sallaman Hajara ne yasaka shi saki na cikin sauri ya tashi itama Hajara cikin sauri tayi hanyan parlour dan tunanin ta wani abu daban ya bata, murmushin mugunta shimfid'e a fuskar shi yace " ga tsaraba nan kin tari yayar ki dashi,sai ki san bayanin da zaki mata "sai a lokacin na fahimci abinda ya faru duk sai naji kunya ya rufe ni me ko zan cewa Hajara ai babu abinda zan fada in wanke kaina,dafe kaina nayi cike da takaicin abinda ya faru tare da dana sanin me yasa na biye shi dana sani da barin shi nayi ya d'auki abinda yake so. Plate ya d'auka ya bud'e warmers d'in ya d'ebi abinda yake so ya fita abin shi ba tare da na sani ba domin nayi nisa cikin tunani,ita kuma Hajara bata tsaya a main parlour ba direct fita tayi ta zauna a inda ta zauna jiya tare da dafe kai duk Gwaggo Aisha taja mata wannan abin kunyan asuban fari ta taso ta kan ta shirya tazo kada ya fita aikin su ya koma baya. Hankalin shi kwance yaci abincin sa yana ta sakin murmushi shi kad'ai kaman wani sabon kamu,he really enjoys what happened between us now, fitowa nayi main parlour ganin zaman ba zai fice ni ba . Wani tukikin bakin ciki ne naji ya tokare min wuya ganin yana ci min abinci,duddubawa nayi ko zanga Hajara amma ko alamarta ban gani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99