Skip to content

Chapter 60

Chapter 60

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

take kusa da ita ta dago suka had'a ido, alama tayi mata da ido cewa kada ta tada hankalin ta sai sunje gida zasu nemi mafita. Wani ajiyan zuciyan ta sauke tana mai lumshe idanun ta alamun ta fahimta, a bakin kasuwa mafi yawancin matan suka sauka kowacce zata nemi motan da zai Kai ta Anguwan ta sai su Inna, Maa, Maman Dije dasu Inna Asabe sune kad'ai aka karasa dasu kofar gida. Maa bata shiga gidan mu ba ta wuce gidan ta su kuma suka shigo gida, a tsakar gida suka iske Gwaggo Aisha tana wanke wani abinta cikin bucket, sallama kawai sukayi kowacce ta wuce bangaren ta ba tare da sun tanka mata ba domin habaice-habaice take tana bin su da harara wai kwadayi yasa suka bi Inna, ita kuwa har duniya ta nad'e bata ga abinda zai sa tabi ta ba dan har abada a matar cushe matar biyan bashin take kallon ta. Wankin ta bari tana cizon yatsa dan ba haka taso ba taso koda Maman Dije ce ta tsaya acikin su ta tanka mata sanin halin ta na bata barin ta kwana sai dai yau harda itan suka ki kulatan. "Ai duk hanyan da zan bi sai nabi naga bayan ki Bintu baki isa kiyi walwala ba muddin ina numfashi a doron kasa sai nabi na kuntata rayuwar ku keda wancan kod'add'iyar 'yar taki" tana magana ne da dukan karsashi dake zuciyar ta fuskarta kuwa na nuna zata iya aikata koda kisa ne dan cimma burin ta. Hajara da shigowar ta kenan gidan tana tsaye a bakin gate kuma tana jin duk kalaman da mahaifiyar ta take furtawa akan mu, hawaye take na tausayi mahaifiyar tasu kan rayuwar da ta zabarwa kanta kullum cikin addu'an neman shiriya take mata amma da alamu tayi nisa sai a hankali, hawayen fuskarta ta goge tsab tana ayyanawa dole ne tayi wani abu na dakatar da duka Shirin ta in ba haka ba ta san halin mahaifiyar ta zata iya aikata komai da ta fada koma fima. Bayan ta tabi zuwa cikin parlour su da ko carpet din arziki babu, da tsaki ta shigo maimakon sallama ta zauna a kasa tana kara jan tsakin da karfi yanda zata ji tayi magana. " Ke kuma lafiya zaki zo ki saka mutane a gaba kina ta jan tsaki kaman wata tsaka?" Gwaggo Aisaha ta tambaya tana mata wani mugun kallo dan harda ita cikin wayan da take jin haushin su kan ko kad'an bata son taji anyi maganan mu balle a fad'i laifin mu. "Umma ki taimake ni zuciya ta zata buga, wannan kyakkyawan mijin da gida kaman aljannar duniya dani ya dace ba wannan kod'add'iyar yariyan ba" ta karasa tana kara b'ata fuska kaman zata fashe da kuka. A mamakince Gwaggo ta juyo tana kallon ta fuskarta d'auke da alamun tambaya tace " wai maganan wa kike min kuma wwni gida?" Sai da Hajara ta tab'e baki kaman abinda zata fad'a har cikin ran ta ne tace " hmmm maganan wannan kod'add'iyar yariyan mana 'yar gidan Bintu". Cikin wani irin sauri tazo gaban Hajaran ta zauna tare da kamo hannayen ta duka 2 ta rike cikin nata fuskarta cike da tsansan farinciki tace " Hajara da gaske kike ?" "Gyad'a kai tayi ta kwakulu hawaye tace" Umma kin gan shi kuwa kaman wani balarabe ga gidan ma yanda kika San a kasar waje kike, ni dai gaskiya ki taimaka in kwace su duka a hannun ta" ta karasa tana goge hawayen ta "Alhamdulillahi!!! Allah nagode maka wannan mugun asiri da matar cushen tayi miki ya karye Hajara ta ta dawo gare ni" tace tana rungume ta harda kwallan farinciki a idon Gwaggo. "Asiri gaskiya ce ni shaida ce tunda gashi nagani akan 'yata mafi soyuwa a gare ni amma kiri-kiri aka raba mu ba kya son a ambaci sunan su koda da wasa da mutum ya tab'a su gwara mutum ya shararawa uwar ki mari goma" Gwwggo ke fadin haka cikin kuka dan da gaske take farinciki dawowar tan domin tun ada baya itace abokiyar shawarar ta daga baya Kuma da ta gane gaskiya sai taja baya da ita. Ta dad'e tana da burin yin wasu abubuwa da dama akai na da Inna ta amma ta rasa dawa zasu had'a Kai suyi domin Jameela kullum bata gida koda ta dawon ma a buge take shigowa. "Kinga yanzu 'yar uwar ki halin da ta zabarwa kanta kenan bana ma samun ganin ta sai bayan satika ko kwanaki koda na ganta ma ba a cikin hayyacin ta take shigo min ba sai cikin maye dama kece kad'ai kika rage min ta raba mu da mugun asirin ta sai dai ta Allah ba tata ba gashi komai ya karye Alhamdulillahi" ta karasa cikin tsantasan farinciki da ta dad'e bata ganta a ciki ba. Mayar hawayen idon ta tayi na tausayin mahaifiyar tasu sannan ta maye gurbin da murmushi tace " toh yanzu meye abin yi Umma?" "Tun kwanaki Lantana ta min alkawarin kaini wajan wani boka da aikin shi yake kaman kaifin wuka, dama rashin ki a kusa dani yasa na bar maganan amma tunda komai ya warware zanyi mata magana mu tafi cikin kwanakin nan komai da suka mallaka sai ya dawo gare mu ". *************** Shiru gidan kake ji kaman ba shine dazu take cike da mutane ba, duk sai naji babu dad'i Ina nan zaune a inda suka bar ni na kurawa tv da yake ta karaji shi kad'ai ido kaman kallon nake amma kuma hankali na ba anan yake ba ya tafi ga tunanin haka rayuwa ta zata kasance zama da wanda bai san daraja ta ba wanda yasha fada min da bakin sa ba sona yake ba, tunda aka kawo ni gidan nan ban abu wai shi farinciki ba ina dai zaune ne kawai in mun hadu banda mugunta ba abinda yake shiga tsakani na dashi. A da nima haushi yake bani kuma in yayi min muguntan bana samun kwanciyar hankali har sai na rama amma a kwanakin nan ban san me yasa ba ko me yayi burge ni yake maimakon inji haushin sa, in yana zaune a parlor ko yana cin abinci nakan buya inyi ta kallon shi tunda ya min iyaka da inda yake yace kada in kuskura in zauna inda yake, so must time ko ina parlour in ya shigo zan tattara in koma nawa inyi ta leken shi wani lokacin nakan ji haushin kaina tare da tambayan toh me hakan yake nufi amma babu mai bani amsa. Wani abin takaici ko cikin dare na tashi wani lokacin na kan leka d'akin shi,ina iya hango shi yana baccin shi cikin kwanciyar hankali, cikin d'an hasken dim light dake bari na gefen gadon shi ba na sanin ko minti nawa nake a wajan all I is ina dadewa sannan in koma in kwanta Sallamar shi cikin azzakar muryan shi naji ya daki kunne na duk da ciki-ciki yayi ta dan na san baiyi tsammanin da mutum ba a parlorn ba, kasa amsawa nayi saima bin shi nayi da kallo har ya shige , yayi min matukar kyau cikin wani lallausan yadi maroon da ya saka anyi mata dinkin zamani irin iya cinyan nan kan shi babu

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99