Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
Download Book

Gwaggo Aisha na cewa taji tsoro da ta tsaya mana taga yanda zatayi da ita. ************ Haka rayuwar gidan mu ya cigaba da tafiya babu wani canji saima kullum kara gaba yake na yanda suke mana a gidan,shi kuwa Baba bayan wancan girkin Inna daya fita yanzu tayi kusan girki uku amma ya rasa taya zaiyi ya shawo kan ta a rinka cin dad'in nan dashi. Kullum in Inna tace da girki tun daga zaure zaka fara shak'an k'amshi mai saka yawu tsinkewa,haka Baban duk magariba zai dawo yayi ta b'uda hanci yana shak'an wannan kamshin yana," ikon Allah wai yau Bintu ce ke irin wannan girke-girke a gidan nan,da zan samu shawo kanta har na aljihu zan samu kashh Allah kawo hanya" haka zai zauna yayi ta sumbatu shi kad'ai kuma kullum cikin tsammanin zai ganni da tiren abinci yake. Kusan sati na 2 kenan a makaranta hankali na kwance nake zuwa, Alhamdullilahi karatun ma yana shiga k'wanya ta sosai tsab'anin da,ko assignment aka bamu da kaina nake yi in na dawo gida. Makaranta yayi min dad'i sosai dan yanzu har k'awaye gare ni,na murmure nayi kyau na k'ara haske abina yo kullum sai naci nayi nak abina,wani lokacin na saka Inna ta zubo min abinci na in tafi dashi makaranta kasancewar yanzu banda mu cikin way'an da ake rabawa abincin makaranta daga primary 6 ne zuwa kasa mu kuwa yanzu muna j.s.s1. Abdulbasit tun ranan daya tafi bai k'ara dawowa ba yau kusan sati uku kenan,kayan abincin mu sun fara d'an yi k'asa kad'an saboda yawanci Inna in tayi girki ko ba ranan girkin ta bane sai ta zubawa k'ananan yaran gidan sun ci,albarkacin wannan abincin da suke samu sun daina mata rashin kunya ko iyayen su sun nemi suyi kememe suke k'i. Ko aike zatayi in ni ina makaranta har rige-rigen karb'a suke suyi mata hankali kwance. Ranan wani asabar bayan sallah la'asar ina zaune a d'akin mu ina duba English textbook na kasancewar yau babu islamiya ana auren wani Malamin mu Inna kuma tana gefe tana ninke mana kayan mu data wanke muka ji sallaman wani yaro a k'ofar d'akin mu Inna ta amsa tana tambayan waye ne,ya amsa mata da shine Alai gana yaron Yakura dama wani ne a mota yake k'iran zareefa a waje. Kallon Inna nayi da sauri zuciya ta tana bugawa kaman ta fito ina jiran inji tayi min fad'a amma naji tace inje mu gaisa ince itama tana gaishe shi amma kada na dad'e. Ni dai mamaki ya hana ni tashi dan sam bata tab'a gaya min yanda sukayi dashi ba dan haka ban san komai akai ba. "Wai bada ke nake magana ba" ta fad'a a d'an tsawa ce tana ajiye kayan hannun ta, jiki a mace na tashi na saka hijabi na na fita, tsakar gidan mu babu kowa sai k'ananan yara da suke wasa iyayen su sun tafi biki can gaba da layin mu. K'ananan kaya ne a jikin shi yau wandon jeans baki da riga t shirt fari sol sai takalmin sa shima baki yana tsaye hannayen shi duka biyu cikin aljihun wandon shi. Ina fitowa muka had'a ido ya sake min murmushin sa mai kyau ni kuwa had'a rai nayi ina turo baki na tsaya d'an nesa dashi kad'an. "K'anwata babu gaisuwa ne?" Ya tambaya yana murmushin. Cikin turo baki na ce," ina wuni" bana buka rik'e kayan ki tunda sai da na rok'a". Yace Shiru nayi bance mishi komai ba. "Bud'e seat d'in baya yayi ya ciro wasu manyan shopping bags guda uku yace biyu nawa d'aya kuma in bawa Aunty wai yana sauri ne shiyasa ba zai samu su gaisa ba kuma in bata hakuri yayi tafiya ne shiyasa taji shi shiru. Ido na cike da hawaye na ce," in na karb'a fad'a Inna ta zata min kuma aini ban san Auntyn naka ba ta ina zan kai mata" na karasa hawaye na zubo min. Murmushi yayi yana ," cry cry Baby,ke sam ba kya gajiya da kuka ne?" Nan ma ban kula shi ba ya cigaba," ammm Innar ki babu abinda zata miki saboda last time da nazo ita ta yarda in dinga zuwa muna gaisawa nd Aunty na kuma ba kowa bace Innar kice". Sai a lokacin naji hankali na ya kwanta duk da dai ban yarda da abinda ya fad'a ba. "Ki shiga gida ina jiran ki anan in tayi miki fad'an sai ki dawo min da kayan,kin ji ko?" Yace min ganin har yanzu ban yarda da maganan shi ba.qa Da toh na amsa mishi na d'auki kayan da kyar saboda nauyin su na shiga gida zuciya ta cike da fargaban me Inna zata ce. Kayan na ajiye ina kallon idon ta bayan na shigo da sallama ta amsa min. "Har ya tafi?" Naji ta tambaye ni. Da eh na amsa sannan na fad'a mata abinda yace sai banga wani tashin hankali akan fuskar ta ba saima cewa da tayi tana amsa gaisuwan shi. Cire hijabin nayi na koma kan takardu na na cigaba da abinda nake ba tare da nabi ta kan kayan da na shigo dasu ba. Sai da Inna ta gama abinda takeyi sannan ta bud'e jakan daya ce nata ne, turmin zani masu kyau guda 2 da lace guda d'aya sai kuma dubu ashirin a k'asan kayan ta gani. Shiru Inna tayi tana kallon kayan cikin wani yanayi na damuwa da tsoro,ita in ba dan Maa tace mata bakomai ba data taka mishi brick. A hankali kuma ta jawo nawan ta bud'e shima 'yar kantuna ne masu tsananin kyau da d'aukan hankali kusan su biyar riga da skirt biyu sai dogagen riguna biyu da kuma riga da wando irin wanda rigan yake sauk'owa har guiwa shi kuma guda d'aya da katon baby na a k'asan. Shima ta dad'e shiru tana nazari sanna ta bud'e na karshen, roban ice cream manya biyu da sauran tarkacen su biscuit da chocolates sai kaji gassasu har biyu suma a kulle a ciki. Yanzu kam tagumi ta zuba tana tunani anya akwai wanda zaiyi maka haka saboda Allah babu komai a zuciyar sa, zamani ya lalace dole tayi shakkan wannan al'amari. Sanin gidan babu kowa yasa tace inje in kira mata Maman Dije ince tazo yanzu dan Allah. Matan k'anin Baban mu ne,tun fil azal a wajenta Inna ta ke samun sauki dan ita babu ruwata da haukan su sai kishiyarta ce bakin su d'aya dasu Inna Asabe. Batayi nawa ko gardama ba muka taho tare amma sai Inna ta ta dakatar dani shiga d'akin tace inje inyi wasa zasuyi magana. Ina jin haka ni kuwa na fice daga gidan zuwa gidan kakata nayi zama na acan. Inna tun daga farkon had'uwa ta da Abdulbasit har zuwa yau ta bata labari tare da fad'a mata abinda Maa tace da kuma yanda ita hankalin ta yaki kwanciya akan lamarin,dubu ashirin fa banda sauran sayayya da yayi gaskiya abin abun dubawa ne. Bayan d'an nazari itama exactly kusan abinda Maa ta fad'a shi ta fad'a mata tare da cewa ta rike Allah ta kuma rike addu'a insha Allah babu abinda zai faru. Godiya Inna tayi mata tare diban mata kayan makulashen tace ta bawa yara karb'a tayi tana godiya ta koma b'angaren su.

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99