Chapter 37
Chapter 37
zanje duk wacce tayi min itace matar ka insha Allah" Abba ya karasa hankalin sa kwance. A rikice Zafar ya d'ago da kai ya rarrafo gaban Abba ya fara magana duk a rikice" Abba wallahi ba wai nayi biris da maganan ka bane na zata kace in kawo ta yau ne shiyasa nayi shiru, please Mom kisa baki wallahi maganan da nazo dashi yanzu kenan please Abba". "Alhaji kayi mishi afuwa tunda bai fahimci abinda kake nufi ba sai yanzu ". Cewar Mom kenan da duk har yanayin ta ya canza. "Hum kuma daina b'ata bakin ku kema kin san in nayi magana d'aya bana canza ta". "Abba na sani wallahi na sani amma dan Allah kayi hakuri ba dan hali na ba" ya cigaba da magiya shida Mom Abba yana jin su bai kula su har sai da ya wana su son ran shi sannan ya ce; "Ya isa haka naji sai ka kiyaye next time 'yar waye ne ka samo mana??" Harshan sa har hard'ewa yake wajan bada amsa " sunan ta Zareefa a garin nan take 'yar Mallam....." "Mallam kuma Zafar ?" Mom ta katse shi fuskar ta d'auke da matsanacin damuwa. Kamin ya bata amsa Abba ya karb'e da cewa" ke yakewa bayani da zaki katse shi? Meye laifi a auren 'yar Mallam, so kike kiji yace 'yar Alhaji ko 'yar governor or what?" Ya karasa fuskar shi na nuna bacin rai. Cikin kwantar da murya Mom ta shiga bashi bashi hakuri bai amsa ba illa mikewa da yayi ya wuce sama tare da cewa Zafar ya biyo shi. *********** Gwaggo Aisha da kawar ta Lantana suna tattaunawa cikin farinciki a cikin motar haya suna dawowa daga kauyen Manguno inda aka kai ta wajan wani boka. Cikin annashuwa ta ce" gaskiya Lantana na jinjina miki dama kin san irin wajan nan.amma kika barni ina ta shan wahala kan kananan kwarin nan?" Cikin fariya Lantana tayi wani dariya ta amsa da " A'i kenan ai ba nan kad'ai na sani ba wajaje dayawa na sani kin san duniyan nan sai da dan shige-shigen nan zaki kwacin kanki kuma ki wuce rainin miji ko kishiya. Kin gan ni nan wallahi Mallam Ado sai abinda nace a gidan sa yake babu wanda ya isa ya tsallake magana ta har matan shi da yaran su". "Kai kawata kina wuta ina bin ki da fetir har kinsa na fara hangowa ina juya Bintu da wannan fitsararriyar 'yar ta" cewar Gwaggo Aisha cikin jin dad'i. "Ke dai kibi duk sharud'a daya kindaya miki kiga aiki da cikawa kasancewar aikin shi kaman yankan wuka yake. "Ai dole ne in bi sharud'an nashi" da wannan tattaunawan har suka iso gida. Sai bayan karfe 3 bacci yayi nasaran sace ni nan kan sallayan, kiran sallah farko Inna ta farka ta ganni kwance kan sallaya bata tashe ni ba tayi alwala ta fara nata nafilfilu kasan zuciyar ta kuwa tana mamakin kwanciya ta a nan. Sai da aka fara sallah a sauran masallatai sannan ta tashe ni na fita nayi alwala nazo na kabbara sallah, ko azkar kasawa nayi saboda baccin dake cin ido na kara bingirewa nayi na cigaba abina anan Inna ta fahimci bacci bai ishe ni ba jiya cikin tausaya min ta kama 'yan aiyukan ta nan cikin d'akin ba tare da ta fita ba, bata kawo komai a zuciyan ta ba duk a zaton ta ban dawo dai-dai daga shock na rabuwa da Yaya na ba. A wannan Gwaggo Aisha tayi bine-binne ta a mashigar kitchen d'in mu ta saka kujera a k'ofar d'akin ta tana jira mu fito mu tsallaka kaman yanda bokan ta yace. Cikin ikon Allah Inna itama baccin ta koma tunda babu wani abu na azo a gani da zatayi, cikin bacci muka ji kaman ana tonon abu cikin k'asa, ko motsi banyi ba amma na farka sai Inna tace tayi karfin halin fitowa jin muryan maza kuma bakin murya ya cika gidan. Maza tayani sun kai su biyar kowanne da abu a hannun shi yana tono Baban mu na tsaye daga gefe , kamin Inna ta bud'i baki tayi tambayi me yake faruwa suka ji muryan Gwaggo Aisha tana" kai! Kai!! Ku dakata me kukeyi haka?" Duk suka juyo suna kallon ta duk ta had'a zufa sai wurwurga ido take, Baba ne ya bata amsa da " meye naki na ihu haka sai kace gidan ki ake tono, Toh gini zanyi zan canza ginin gidan nan ya zama na zamani"..... [1/26, 7:12 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *21&22* "Haba Mallam ba zaka bari mu d'an kimtsa ba gyara da sassafe haka?" Gwaggo Aisha ke fad'an haka cikin matukar tashin hankalin gani za'a saka ta wahalan banza. "Wani irin kimtsawa sai kace daga kofar ki aka fara, ki bari in aka zo kofar ki sai ki kawo korafin naki" Baban mu ya amsa a dakile. "Ni ba wani abu nake nufi ba naga safiya ce kuma ai ko ita Bintun zata so a bar ta ta d'aura abin karyawa ita da 'yar ta, ko ba haka ba Bintu?" A zuciyar ta kuwa tana ta addu'an Allah yasa Inna ta amince da abinda ta fad'a a fasa tonon sai bayan mun shiga kitchen d'in mu munyi girki, kamin nan mun sallake abubuwan da ta binne shiyasa dama ta zab'i binnewa a kofar kitchen d'in mu sanin ba wanda zai taka wajan sai mu. "A'a in ta nine bakomai suyi aikin su, ba zamu rasa yanda zamuyi ba, wannan ai abin farinciki ne kuma cigaba ne muma zamu zama 'yan gayu" Inna ta amsa tana dariya sauran mutane da suke wajan suma dariyan sukayi suka cigaba da aikin su ba tare da sun lura da halin da sun lura da halin da Gwaggo Aisha ta shiga ba. Afujajjan ta shiga d'akinta sai safa da marwa take duk ta had'a zufa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99