Skip to content

Chapter 86

Chapter 86

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,188 words 0 views Progress saved
Download Book

Hajara dan rashin zuciya ina kanwar bayan ta shine harda karban kayan hannu na tayi min rakiya. Yana ganin fitowan mu yayi saurin bud'e min kofan mota dama yana tsaye a jikin motan ne, gaishe shi Hajara tayi tare da saka min kayan a mota sannan tayi min waving ta koma cikin gida. Tsaye nayi ina kumbura fuska da tura baki gaba dan gaba d'aya haushi shi nake ji na me yasa bai barni na kai dare a gidan mu ba, fuskar shi d'auke da fara'a yace " shigo mu tafi mana 'yan mata na?" Ko kallon shi banyi ba na shiga ina jin haushin sunan daya kira ni dashi wai 'yan matan shi ko ta ina na zama 'yan matan shi oho, rufe min kofan yayi ya zagaya ya shiga mazaunin driver yayi reverse muka kama hanya har sannan naki kallon side d'in da yake kacokan na maida hankali na kan hanya shi kuwa sai juyowa yake yana kallo na . A wani restaurant ya tsaya yana kallo na nima jin mun tsaya kuma bamu kai gida ba yasa na juyo na dubi side d'in shi caraf ido na cikin nashi ya wani kashe min ido tare da daga gira daya alaman ya dai? Kawar da kaina nayi ina kara turo baki , da san irin wannan kallon yake min da ban juyo ba na kalli inda yake ba dan sosai ya kashe min jiki da salon shi. "I will be right back wifey" yace min cikin wani husky voice sannan ya fice na bi shi da ido har ya shige ciki, ajiyar zuciya na sauke mai karfi ina kara jin son shi na ninkuwa a zuciya ta " how I wishh......." Nace Ina lumshe ido tare da fad'awa duniyar tunani har ban san lokacin da ya dawo ba sai lallausan tafin hannun shi da naji akan fuskata yana shafawa a hankali yasa na bud'e ido na a zabure ina watsa mishi mugun kallo d'an dariya yayi yana d'aga hannun shi sama alaman surrender. "Tunanin me kike haka da har ba kiji shigowana ba" yace yana juyowa gaba d'aya shi gare ni bance mishi komai ba na sunkuyar da kai na kasa hawayen da ban san na menene ba suka fara sauko min. "Ohh shiitt me yasa kike min asaran hawayen ki masu tsada da darajan nan, in maganan Baba ne I promised you babu abinda zai same shi kuma soon zai dawo gida pls ki kwantar da hankalin ki kinji " yace yana miko min tissue . Banyi gardama ba na karb'a na goge ido na tare da gyad'a mishi kai a hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana "good girl" sannan yayiwa motan key muka mike hanyan gida, koda muka iso gida ya hana ni d'aukan kayan yayi shi ya shigo mana dasu duka har parlour na ya kawo min kayan sannan ya ce in fito muci abinci. "Ni na koshi "nace ina cire hijabin jikina tare da nemawa kaina wajan zama, marairaice fuska yayi yana kallo na can kuma sai ya zauna kusa dani yace " haka mukayi da ke, i thought mun riga da munyi solving komai before mu fita, meyasa kike son maida mu baya pls ki bar komai ya wuce kinji we are now good friends uhum?" Ya karasa cikin rarrashi ya kama hannu na ya mikar dani muka fito, bai saki hannu na ba kaman yanda nima na kasa yi mishi musu har muka isa dinning. Kujera yaja min na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fara firfito da kayan kwalama da ya sayo mana a restaurant " zabi abinda zaki my babe" yace yana turo min su gaba na. Tsam na mike ba tare da na bashi amsa ko na kalli tullin abincin da ya turo min ba na wuce ciki abina, da kallo ya bini zuciyar shi na mishi wani irin share shi da nake yi, kasa tab'a komai yayi shima ya ture su gefe ya zuba tagumi yana zurfafa tunanin ta ina zai b'ullo min ya shawo kaina, yaga na dawo da warmer da Inna ta zubo min abincin a ciki na ajiye sanna na zauna ina kokarin bud'ewa . "Wow ashe kayan dad'i kika kawo mana daga gida" yace yana kallon yanda na cika plate d'ina kuma bani da niyyan zuba mishi, amma jin yanda yayi maganan cikin natsuwa da danganta gidan mu da masu yasa shima na zuba mishi na tura gaban shi ba tare mun had'a ido dashi ba. Kara jawo plate din yayi gaban shi ya saka spoon ya cika da jallof din shinkafan da yayi shar dashi da tarin nama a ciki kaman ba abinncin sadaka ba ya kai bakin shi a take ya lumshe yana " hmmmm ashe a wajan Momyn mu kika koyi daddadn girki nan, sai dai ita nata yafi naki sau goma kullum Ina santin naki ashe ga original din nan naki photo copy ne". Ban san lokacin da na d'ago kai muka kalle shi ba fuskata d'auke da murmushin jin dad'in yanda ya yabi Inna ta for the first time naji ya burge ni ban san lokacin da na fara bashi labarin yanda yan gidan mu suke santin girkin ta kullum manya da yara duka. Cikin jin dad'in yanda na saki jiki muna labari dashi ya rinka ja na yana yabon gidan mu daya lura shine abinda nafi so kuma yake sakani farinciki, sai gashi mun cinye abincin tas harda karawa da fruit sauran kayan kuma na Kai kitchen na ada na su. Har dare muna tare yana cigaba da jana a jiki babu laifi nima na sake sosai tare mukayi kallo na kawo mana su alewan madara dasu gulli shiwa da Inna ta had'a min acikin ledan dana taho dashi harda su tsumi a ciki sai dai su can cikin drower na bud'e na adana su cos ban san amfanin su a yanzu ba ,har zuwa goman dare muna tare sannan na mishi sai da safe na shige d'aki na bar shi zaune yana jin kaman ya biyo ni mu kwana tare amma ya daure shima yayi d'akin shi yana ganin nesa tazo kusa tunda har ya gano abinda yake saka ni farinciki lokaci d'aya. Da washe gari haka na taso cikin walwala dan kasncewar mu tare jiya yasa na rage damuwan da yake zuciya ta sosai, kitchen na shiga na fara nema mana abu mai sauki da zamu yi breakfast dashi bayan na gama kimtsa gidan tsab sai kamshin turaren wuta yake tashi ta ko Ina. Na gama komai cikin kankanin lokaci na jujjuye su a warmers ina cikin juye tea da na dafa da kayan kamshi a flaks naji numfashin mutum dab dani a tsorace na juyo saura kiris ruwan shayin ya zube a kafana yayi saurin tarowa ya rike yana " hey be care full zaki kona wannan kyakkyawan kafan naki ki min asara" bance mishi komai ba sai zamewa da nayi na bar mishi shayin na koma gefe shi kuma ya cigaba da juyewan. "Ina kwana " nace mishi a hankali Ina kallon kasa. "Da fatan princess d'in Inna ta tashi lafiya" yace yana murmushi. Nima murmushin nayi jin ya Kira ni da princess d'in Inna, d'aukan tryn dana jera kayan Karin a kai

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99