Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

abin ya birge mutane sukayi ta mana hoto a wannan yanayin . Kawar da kai na nayi gefe ina jin kaman in tashi in gaggaura mishi maruka amma na danne zuciya ta ina hasaso yanda zaman namu zaya kaya nida shi. Ina cikin zancen zuci naji wannan mayen kamshin nashi ya kara cika min hanci wanda yake kara tabbbar min da kusancin namu ya karu, ban juyo ba balle inga wace irin zama mukayi da shi. A zabure na juyo ina kallon shi da ido na duk a waje sakamakon jin hannun shi a cikin nawa, muna had'a ido ya sake min wannan killer smile d'in nan nashi da in yayi babu alkhairi a cikin ta Aiko kamin in tantance me yake faruwa naji ya fara murza min hannu cikin kwarewa da cin zali da mugunta, a take naji kaman in saki fitsari a wajan amma da yake nima ba baya ba wajan iya basar da abu dan haka na basar kaman ba ni yakewa wannan muguntan ba. Cikin abokan shi wasu suka zo suna mu fito muyi rawa amma kememe yaki ko matsawa balle ya tashi , da suka ga bashi da niyyan tashi duk suka rufu kan mu tare da fara mana barin kud'i kaman basu san zafin su harda wasu cousins d'in shi 'yan mata da naga suna yi min wani kallon kasa-kasa ko me suke nufi oho dan ni Yayan nasu ma bai ishe ni kallo ba balle su. A cikin gida kuma iyaye na sun yiwa nashi tarba na mutunci sannan aka fara wasu events na al'ada game da wushe-wushen, dama wushe means welcome da yaren kanuri so they are welcoming them to our family wato an zama family d'aya kenan suma sun bada kayyaki na al'ada da ake bayarwa sannan su Inna ma sun mayar musu da wasu kayan suma. Sun d'auki lokaci mai tsawo sannan suka gama nasu a cikin gida suka fito gaba d'ayan su harda nawa iyayen, wata mata ce cikin 'yan uwan sa naga ta nufo mu kai tsaye tana murmushi tace " wannan wani irin Ango ne da ba zai cashe ba a ranar bikini sa?" Turo baki yayi kaman wani karamin yaro sannan ya bata amsa " Baawa ni ban iya rawa ba Kuma..." Mugun kallo da yaga ta watsa mishi yasa ya mike babu shiri da hannu na a cikin nasa wanda yanzu nake ji kaman ba a jiki na yake ba tsaban mugunta da yasha. A yanda ya mike ya tabbatar min da yana matukar shakkan matar nan jibi yanda ya mike babu shiri, a raina ina ashe duk wannan muzuran nashi na banza ne tunda da wanda yake. tsoro har haka. Yanda kika san statues haka muka tsaya musu kikam ba wanda yake da yunkurin yin motsi balle a je ga zancen rawa, iyaye na da nashi suka fure ruf sai barin naira suke mana. Ni dai duk mamaki ya ishe ni a raina yanda suke zubar da kud'i kaman basu san zafin su ba, a zuciya ta nace ina Gwaggo Aisha Mai cewa Yaya na d'an yankan kai ne tazo taga wayanan da ko ni kaina zan iya kiran su da hakan dan barnan kud'in yayi yawa. Ana cikin filin Sadeeq yazo ya fara mishi magana a kunne wanda yaja hankali shi ya saki hannu na ba tare da ya sani ba, ban san me suka tattauna ba sai dai naga yana murmushi ya juyo zai kara rike min hannu kan zamu koma mazaunin mu nayi azamar janyewa nayi gaba yabi baya na har muka zauna basu daina mana liki ba. Sai wajan sha d'ayan dare sannan taron ya tashi suka shiga motocin su suka tafi mu kuma muka koma cikin gida muka bar masu decor da tattare wajan. Muna shiga ban tsaya a ko ina ba sai bathroom na samu ruwa mai d'umi sosai nayi wanka tare da gasa hannu na da nake jin sa kaman ba a jiki na yake ba dan tsabar jin zali daya sha. Ina fitowa a wanka naji su Maryam da sauran cousins d'ina da muke mates sun zo taya ni kwana suna ta yaba mugun da basu san halin shi ba. "Wow kai Zareefa tayi babban sa'an samun hadadden miji mai iya love ga kyau ga naira ohh so romantic" cewar Zainab tana zama kusa da Maryam. "Allah ya samu a danshin ta abun yana bala'in burge ni samun classic miji haka" inji Hanan. "Ni abinda yafi birge tunda ya iso yake makale da hannun ta kaman za'a kwace mishi ita" Hauwa ta katse ta. Kallon hannun nawa nayi wanda ya koma jajawur saboda azaba su kuma a haukan su suna yabawa sun zata zallar soyayya ce, cike da jin haushin su na juya musu baya tare da jan duvet na rufe har kaina, ina jin su suka cigaba da suratan su daga baya suka hakura suka kwanta bacci. Basu dad'e da kwanciya ba duk sukayi baccin su hankali kwance, tashi nayi na zauna ina kallon su cikin sha'awa ni da nake jin ido na a bushe babu alaman d'igon bacci, ba yau kad'ai ba tunda maganan auren nan ya tabbata na rabu da bacci mai dad'i dan sai in d'auki lokaci Mai tsawo ban runtsa ba, ko kuma na samu baccin ya kwashe ni daren yana rabawa rabi sai in farka kuma wani lokacin ya tafi kenan wani lokacin kuma sai kusan asuba zai kara sace ni. Yanzu ma da naji kwanciyar ya ishe ni na shiga bayi nayi alwala nazo na tada sallah tare da neman agaji wajan ubangiji na. A b'angaren su Zafar kuwa yan uwan Abba cikin farinciki da Kuma yaba yanda iyaye na suka karrama su suka isa gida yayin da yan uwan Mom sai tab'e baki suke wai ya rasa inda zai nemo aure sai a wannan gida kaman akurkin kaji. Shi kuwa Zafar ko bai kula kowa ba ya shige part din shi ya kulle kan shi a ciki dan kowa ma haushi yake bashi, duk yanda abokanen shi suka so su gan shi bai yiwu suka wuce. ******************** Hausawa sun ce rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, toh hakane ya kasance a yau asabar itace ranar daurin auren kaman yanda naji suke fad'a kuma nake gani a yanzu duka gidan ya kaceme da hayaniya kowa sai hidiman gaban shi yake, masu gyaran gida nayi masu girke-girke nayi masu wanka ma nayi. Ni kuwa ina can kuryan d'aki abin duniya duk ya ishe ni ganin cewa fa da gaske ne auren nawa za'a daura maimakon na tsinci kaina cikin farinciki kaman kowace amarya sai dai ni a bakinciki na tsinci kai na dumu-dumu ga kewan Yaya na da ya dawo min sabo fil, na san da aure na da shine da nafi kowa farinciki a rayuwa amma sai gashi yau da wanda bai sona bai san daraja ta ba za'a had'i ni aure.dashi wace irin rayuwa zan shiga??? Kuka naji mai tsanani ya taho min na tausayin kai na, mikewa nayi ba tare da na kula 'yan mata da suke ta hayaniyar su ba na shiga bathroom dan in samu sukunin yin kuka na ko zan ji saukin rad'ad'in da zuciya ke min. Zama nayi dirshan a

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99