Chapter 16
Chapter 16
sai dai na barwa Allah ne. A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yanzu muna jss 3 komai na alamun girman 'ya mace duk sun bayyana a tare da ni kyawu na ya fito sosai, shakuwa da yake tsanani na da Yaya na ya rikid'e ya koma zallan soyayya, dan sosai yake nuna min abinda ke cikin zuciyar shi tun ina had'awa da kuruciya har ni da kaina na fahimci na fad'a son Yaya na sosai kullum zai zo mu sha hiran mu da kyar zai daure ya tafi, daya ga hakan ma ba zai wadatar dashi ba ya sayo min dankareriyar waya ta wanda kullum ya kasance muna cikin communicating. Wannan waya da Yaya na ya saya min gaba d'aya ya d'agawa Gwaggo Aisha da Hajara hankali harda Jameela wacce take ganin sa'anni muke da ita. Ban san ko ta yaya abin ya kasance ba sai dai gani nayi itama wani mai mota yana zuwa wajan ta hira, daga ranan da mai motan ya fara zuwa a ranan ta sallami duk sauran samarin ta dan dukan su babu mai mota a cikin su dama lallab'a su take. Tun daga wannan rana su Gwaggo Aisha suka fara d'aga murya a gidan komin kankantar abinda ya kawo mata sai an fito tsakar gida ana maimaitawa ana yi mana iyayi a gida, mu dai ko a jikin mu amma Inna Asabe duk ta damu dan tana da 'ya Hasiya kuma sa'ar Hajara ce, Allah ya jarabce ta da bakin jini babu wanda ya tab'a zuwa wajan ta . Yawanci Yaya na in zai zo wajena sai bayan la'asar yake zuwa kuma Baba baya zuwa gida a wannan lokacin amma a yau bayan azahar yazo saboda wai zaiyi tafiya amma ba dad'ewa zaiyi ba gobe zai dawo, muna cikin hira na hango Baba ya nufo gida sai gyara binjimar jikin sa yake, dum naji zuciya ta ta buga dan daga ni har Inna ta bama son Baba ya had'u da yaya na dan zai iya tafka abin kunya dan shi ba damuwar shi bane. Motan yabi da ido ya gan mu tsaye a gefe kaina a kasa dan bana son yayi min magana amma banyi nasara ba. Yana gani na ya nufo inda muke cikin sauri yana," a'a 'yar albarka kece anan?" Kamin in bashi amsa Yaya na ya durkusa har kasa ya fara gaishe shi, cikin washe baki yake amsawa yana bin katuwar motan shi da kallo . *Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*. [9/17, 9:01 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka* Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne. *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._ *Kuyi hakuri kunji ni shiru kwana biyu kun san jiki da jini sai a hankali amma yanzu Alhmdllh naji sauki, wayan da suka kira da wayan da suka turo sakonni duk ina godiya da kulawar ku Allah ya bar kauna. Nagode sosai*😘😘😘 *9* "Lafiya lau yaro.... lafiya lau" Baba ya amsa yana had'iyar yawu yana kara karewa motan kallo, ni dai sanin zai kwafsa min yasa ko d'ago kaina na kasa yi bare mu had'a ido da shi. Yayana kuwa yana gama gaishe shi bai d'ago daga tsugunen ba yayi kasa da kai yana jiran Baba ya bar wajan, Baba ba dan yaso ba yaja kafa zuwa cikin gida yaso ya samu wani abu wajan mai tsallen motan nan, amma ba komai bari yaje wajan Bintu zai ji ko wanene shi d'in. Wata b'oyayyen ajiyan zuciya na sauke ganin ya wuce gida salin-alin ba tare da yayi wani abu daya tsinka ni ba, nabi bayan shi da kallo kaman yanda shima Yaya na yabi sa da kallo sai faman gyara mayattacen binjimar sa ta tshohuwar shaddar sa fara ce amma saboda tsufa har ta koma ruwan toka . "Allah sarki Allah baiyi zamu had'u da Baba ba duk shekaru nan ba sai yau" naji Yaya na ya katse min tunanin da nake. Murmushi nayi ina gyada kaina. "Amma nima ban kyauta ba da ban tab'a tambayan shi ba all this while,wallahi yanzu dana gan shi sai naji ban kyauta ba sam" ya kara fad'a cikin damuwa sosai. "Laa! Kada ka damu Allah ne baiyi zaku had'u ba tun farkon amma yanzu daya so ba gashi kun had'u ba" na bashi amsa ina murmushi. Shiru kawai yayi dan shi a tunanin shi rashi da iyali ne yayiwa Baban yawa shiyasa ya zama haka bai san cewa duk wani yanayi da hali da mutum zai gan shi a ciki shi ya jefa kan sa ba. Har muka gama hiran mu a ranan yana cigaba da nuna min rashin jin dad'in sa ni kuma ina nuna masa ba komai da zai tafi dubu ashirin ya bani wai in bawa Inna ta ajiye min in case wai ko goben ba zai samu dawowa ba, na nuna mishi muna da komai ba sai ya bani kud'i ba amma yaki karb'a saima shopping bags daya maida farilla wajan kawo min su ya lodo min kusan su 3 yana complain wai dole ya nemawa inna fridge ko dan saboda rana irin ta yau, kasancewar na saba kullum sai ya kawo min ice cream na sha toh gashi gobe baya nan da Inna tana da fridge sai ya sayo dayawa a saka min a ciki ko na kwana nawa ne. Amma tunda ya bani 'yan canji a hannu in naga ba zan iya hakura ba sai inje today's ko sidis in sayo abina in sha tunda na saba sha. Ni dariya nayi ta masa ganin duk ya damu akan wai kawai ba zan sha ice cream gobe ba, in ba dan ba dan ba a da ina na san wani ice
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99