Chapter 69
Chapter 69
ba. Komawa nayi cikin Ina ta kumbura saboda haushi na san kila ta koma gida shikenan ya rusa mana budget ina ta murna yau ma zamu yini muna shan hiran mu sai gashi ko gaisawa bamuyi ba ya kore ta. Zaman ta kaman da 15 minutes sai ga Amadu yazo yin aikin sa, maimakon yayi aikin suka bige da hirar su cike da son junan su har Zafar yazo ya wuce da mota bai gama aikin ba ganin sa ne yasa ya maida hankali kan aikin sa,tana zaune ya kammala itama ta mike tace zata koma gida tare suka fito ya rako ta har gida sannan suka rabu cike da kewan juna. Baba Yana zaune a majalisar shi tare da 'yan maula daya samu yana d'an miko musu da na cefane,daga nesa suka hango motocin sojoji har guda 2 sun nufo su, Baba Yana ganin su cikin sa ya murd'a ya mike jiki na b'ari yace "yau kuma me ya kawo wa'yan nan azzaluman cikin anguwan nan" yana magana ne yana nufan hanyan gida amma ko ten step baiyi ba motocin suka karaso tun kamin motan ya tsaya suka fara durowa daga ciki tare d'aga musu tsawa "kada wanda ya motsa daga nan". Cak Baba ya tsaya yana tsiyayen gumi duk ya firgice. "Waye Mallam Hassan a cikin ku?" Suka tambaya. A tare mutanen wajan suka nuna baban mu da yake tsaye yana karkarwa. "Kai ne Mallam Hassan ?" Kai kawai Baba ya iya gyad'a musu. " Common my friend oya! oya! shiga mota mu tafi"wani daga cikin motan ya fad'a, wasu guda hud'u nufo shi fuska a murtuke babu alaman sun tab'a koda murmushi balle dariya, hannu Baba ya shimfid'a yana kokarin rokon su tare da basu hakuri , d'ayan ya d'aga katon bindigan hannun shi yace yana musu gardama wallahi zasu harbe shi a wajan su wuce kuma sun harbe banza. Gudu-gudu Baba ya nufi wata bakar mota da sai yanzu ya lura da ita suka hankad'a shi ciki babu b'ata lokaci suka fice daga anguwan da matukar gudu. " Allah ya kiyaye mu da basu d'ubi kowa daga cikin mu ba sai shi kad'ai suka nema" inji wani dattajo cikin 'yan zaaman majalisan. "Ni dama wannan kud'i na Mallam Hassan akwai ayar tambaya ace mutum yayi kud'i lokaci d'aya"? Wani ma ya kara nashi. " Ai ko yanda suka ciko motoci saboda shi kad'ai kuma kun san abin azimun ne" " Kunga yanzu ba lokacin wannan bane mu watse kamin su canza ra'ayi su dawo su had'a da mu" fad'an hakan ke da wuya duk suka watse cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, nan da nan labari ya cika anguwa cewa sojoji sun kama Baba sun tafi dashi. [12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *45&46* A guje Ibrahim ya shigo gida har yana fad'uwa kasa Inna da take tsakar gida ta nufo shi tare da d'aga shi tana karkad'e mishi jiki tace " toh d'an tsokana wa ka tsokano ya biyo ka, ka shigo a guje haka?" Yana haki irin na alamun ya sha gudu yace yana nuna mata kofan waje " Baba ne..... Baba ne sojoji suka tafi dashi". "Wani Baban kuma Ibrahim"?" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "Baban mu, Baban mu na gidan nan" ya amsa mata tare da fara kuka. Salati Inna ta fara tana tafa hannu cikin tashin hankali murya na rawa ta d'aga murya tana " kuna ina matan gidan ku fito dan Allah kuji abinda yaron nan yake fad'a" Inna Asabe ce ta fito da gudu har tana tuntube bakin ta d'auke da salati itama nan suka kacame dasu da sauran yaran suna ta cacekuce dan sun rasa ta ina zasu fara kasancewar kowa ya san harkan sojoji wuyan sha'ani ne dashi a nan maiduguri. Duk hayaniyar nan daya cika gidan mu har makota sun shigo 'yan jin gulma da da masoyan gaske ana ta jajantawa amma gwaggo Aisha bata leko ba balle asan tana gidan ko bata nan a wannan yanayin Baban Dije ya shigo shima hankali tashe amma ganin su Inna a wannan yanayin yasa yayi kokarin boye nashi tashin hankalin ya shiga kwantar musu da hankali kan cewa kada su tada hankalin su su bi komai a sannu insha Allah Baba zai dawo gida tunda ko makiyin sa zai bada shaida akan sa baya aikata wani mummunan abu shi dai bar shi da son kud'i. Da wannan bayanan ya samu suka d'an natsu kowacce ta koma daki makota kuma suka koma gudajen su da addu'an Allah ya sauwaka. Hankali tashe Hajara tayi sallama ta shiga cikin gida dan saukowan ta kenan daga napep 'yan suka tare ta da mummunan labarin nan, ganin babu kowa a tsakar gidan yasa ta nufi d'akin su tana kwad'awa Gwaggo Aisha kira kaman zata tsaga gidan amma bata ji muryan ta amsa mata ba, a zaton ta bata gidan ta fita ko sun fita da sauran matan gidan. Turus tayi fuskarta cike da al'ajabi ganin mahaifiyar nata kishingid'e tana cin gyad'a mai gishiri hankali kwance, d'ago kai tayi ta kalle ta sannan tace meya faru kike ta kwala min kira kaman zaki tsaga gidan nan ko dai yauma kin zo min da labari me dad'i ne?" Had'iye mamakinta tayi tace umma ni ba dan wannan nake kiran ki ba yanzu ina saukowa a napep naji ana ta kananan maganganu a anguwa wai sojoji har mota 2 sun zo sun tafi da Baban mu?" Tab'e baki tayi tare da watsa gyad'an hannun ta a baki ta fara taunawa tana hararan ta tace" toh sai akayi me ko ni na aike shi yin mummunan aikin da zasu kama shin, kema kin san Baban ku da shegen son kud'i kinga kuwa wani ta'asan yaje yayi musu, tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan zai doka". Tunda ta fara magana Hajara take kallon ta cike da takaicin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99