Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
Download Book

rijiya da baya ashe,nan na bata hakuri tare da alkawarin bani ba wanda ban sani ba nan gaba. Daga nan hira muka zauna yi da Inna ta bayan na bud'e mana takeaway nace muci tare,kallon abincin tsaya yi kana tace,"yanzu dama irin wannan abincin ake raba muku harda naman kaza?" Dariya na kyakyale dashi sannan nace," Inna baki ga harda bobo na ba?" "Ikon Allah tunda nake ban tab'a jin labarin governor mai son talakawan shi haka ba sai akan bawan Allah nan,Allah ya kiyaye mana shi" cewar Inna . Da "Ameen na amsa sannan nace mata muci mana,amma taki ci d'an tab'awa kawai tayi ta bar min kaya na anan ne take gaya min ashe 'yar wata makociyar mu mai suna Ya'ana ita ta koya mata d'inkin hula,shikenan ta huta da zaman banza inta gama ance ana saya da kud'i da d'an yawa,murna nayi tayi muma mun samu sana'a da zamu rinka samun kud'i kaman sauran 'yan gidan mu. Tun daga wannan rana na mayar da hankali na kan makaranta islamiya da nake in kuma safiya ce Inna ta kan tura ni gidan kakanni na saboda gudun rigimar 'yan gidan mu sai lokacin islamiya yayi sai in dawo in shirya inyi wucewa ta domin Gwaggo Aisha tafi kowa iya tuggu kuma Baban mu sosai yake jin maganan ta in fact itace 'yar gaban goshin shi ba dan komai ba sai dan tafi sauran matan shi kud'i kuma tana bashi kud'i shiyasa yake ji da ita sosai. Maganan shiga secondary school mun ajiye ta a gefe kan cewa sai inna ta dinka hula 2 ko 3 sai ta had'a kud'in ayi min komai dashi. Cikin ikon Allah satin hulan 4 Inna ta kammala shi baiyi kyau irin na kwararre ba amma da yake cikin tsafta ta dinka shi babu datti ko kad'an a jiki sai ya zama abin sha'awa. Ya'ana wacce ta koya mata itama ta gama nata zata kai sayarwa Inna tace muje tare sai ta sayar a bani kud'in kasancewar ita zata wuce gidan kakanni ta daga can kuma zata kwana 2 kamin ta dawo. Bayan ta shirya ta biyo min muka tafi can London ciki wai can sun fi sayan hula da daraja, dubu da dari biyar aka sayi na inna ta ita kuma Ya'ana dubu tara aka sayi nata da saboda ita nata tangaran ne. A leda baki ya'ana ta kulle min kud'in ta saka ni a napep na zuwa anguwan mu ita kuma ta wuce,muna zuwa kusa da layin mu suka sauke ni suka wuce. Har nazo kusa da layin mu na had'u da wani mutum yace min," ke ana sadaka a wacan kwanan" kamin in bashi amsa wasu yaran su 4 suka zo wucewa ya fad'a musu ba musu suka bi hanyan daya nuna nuna musu,ganin sun bi hanyan yasa nima na bisu a guje muna shan kwanan ashe mutumin yana bin mu sai muryan shi muka ji yana cewa," kai ku tsaya in akwai abu a hannun ku,ku kawo in ajiye muku kar ya fad'i wajan karb'an sadakan". Gaba d'aya mu muka mika mishi duk kud'add'en hannun mu da alamu suma sauran yaran aiken su akayi,yana karb'a yace mana ga gidan can mu shiga shi yana jiran mu anan. Ga gudu muka shiga gidan da sunan karb'an sadaka amma me sai aka ce mana ai ba anan akeyi ba,wata da zata girme mu a ciki tana jin haka ta fita da gudu muka mara mata baya amma muna fita muka nemi mutumin nan sama ko kasa muka rasa shi,kuka ko wannen mu ya fara dan sai yanzu muka gane cewa ashe b'arawo ne yayi mana dabara ya sace mana kud'add'en mu. Gefen titi na samu nayi zama ta ina kuka na kasa komawa gida in naje me zan cewa Inna ta bayan kwanaki tayi min fad'a akan irin haka sai gashi na maimaita,bayan haka hulan nan yanda ta dage tayi ta d'inka shi ba dare ba rana dan ta samu saka ni a secondary school amma sai in koma ince mata wani ya min dabara ya kwace? gaskiya ba zan iya komawa ba. Ina zaune ina kuka na d'aya daga cikin yaran da shima an sace mishi kud'in yazo ya zauna kusa dani muka cigaba abin mu,kaman daga sama naji ance," kanwata yauma kukan kike?" Da sauri na d'aga kaina dan ganin waye sai naga wannan bawan Allah daya biya min kud'in jarrabawa ne hannun shi rike da bottle water inaga a shagon kusa damu ya saya ga mutane a wajan suna ta shiga da fita babu wanda ya kula mu sai shi da yazo yanzu. Kin kula shi nayi na d'auke kaina ina goge hawayen ido na. "Kai meya same ku kuka zauna anan kuke kuka?"ya tambayi yaron kusa dani. Shi kuwa kama jira yake ya fad'a mishi duk abinda ya faru nan ya tambayi shi nawa ne kud'in?. "Dari uku ne akace in sayo taliya da mai da maggi" ya bashi amsa. Dari biyar ya ciro a aljihu usual sabo dal ya bawa yaron,cike da murna yaron ya karb'a yana godiya ya ruga da gudu ya tafi shagon kusa damu ya sayi kayan yanda ya fad'a ya dawo mishi da canjin shi,amma sai yaki karb'a yace ya tafi ya bar mishi. Murna fal ranshi ya kama hanyan gida da gudu ya bar mu a wajan,ganin ban bi yaron ba yace min," ba tare kuke bane?" Jiki a mace na girgiza kaina saboda na zata yaron yana amsan kudin zai zama doya kaman yanda inna ta ta fad'a sai naga ba haka bane lafiya lau yayi sayayyar shi ya tafi gida. "Ke kuma nawa ya sace miki?" Muryan shi ya katse min tunanin da nake. "Kud'in hulan Inna ta ya karb'e gaba d'aya" na bashi amsa. "Stop crying kanwata kinji,gashi karb'i ki kai mata". Kallon kud'in na tsaya yi ina tunanin in karb'a ko a'a? "Karb'a mana ki goge hawayen ki" saka hannu 2 nayi na karb'a cikin sanyin murya nace," nagode!" Girgiza min kai yayi ya ce," kada ki damu tashi ki tafi gida". Da azama na tastashi nayi gidan mu ba tare da nasan nawa ya bani ba. A gida kuwa Inna duk ta damu tana tunanin me yasa na dad'e haka,tana ganina ta sauke ajiyan zuciya ta ce," zareefa me yasa kika dad'e haka?" Banyi kasa a guiwa ba na kwashe duk abinda ya faru na gaya mata,karban kud'in tayi ta kirga taga dubu uku ciff,fincikoni tayi da karfin tsiya na fad'i akan simintin d'akin na bud'i baki zanyi ihu ta ce kada na kuskura inyi mata ihu anan dole na had'iye kukana ina zaro ido saboda ganin Inna ta ta fusata yau sosai. " Wato ke ba kya jin magana ko zareefa duk abinda na gaya miki ta bayan kunnen ki suka wuce ko,baki san ki kama kan ki a matsayin ki na ya mace ba duk ko wani d'an iska ya baki kud'i karb'a kike yau kuma harda bin wani, Inna ilahi wa inna ilahi rajiun!!! Toh tunda kunnen kashi gare ki yau zanyi maganin ki wallahi" ta karasa tare da murd'e min kunne. Sosai ranan inna tayi min abinda tunda na san kaina bata tab'a yi min ba daga baya tayi min nasiha sosai mai ratsa

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99