Chapter 84
Chapter 84
kujera tare da dafe kan shi da hannu 2 yana mayar da numfashi dan ya rasa kalan tunanin da zaiyi. Sai da yayi sallah la'asar sannan yaji zuciyar shi tana mishi sanyi kad'an-kad'an sakamakon tunanin da yayi na cewa yanzu fushi ba nashi bane dole yabi komai a hankali domin babu abinda fushin zaiyi saima kara jagula al'amura, sabon wanka yayi ya canza shigar sa zuwa shadda gezner armyn color d'inkin zamani kayan sun zauna sosai a jikin shi sai maiko yake amma bai saka hula ba sai lallausan gashin kan shi daya sha gyara yana d'aukan ido. Cikin takun sa na cikakken namiji mai ji da class ya fito ya nufi motan shi bayan yayiwa kanshi wanka da turarukam shi masu dad'in kamshi, bai tsaya b'ata lokaci ba ya nufi gidan mu yana kara tausan zuciyar shi kan ya kau da idon shi kan duk yanayin da ya gan Ni a ciki saboda wannan kidnapper. Ni kuwa a gida sai da Inna ta nuna min jan ido sannan na had'iye sauran kuka na ba dan raina yana so ba, nasiha tare da fad'a tayi min sosai akan kada In kuskura in kara nuna damuwa ta akan wani d'a namiji bayan miji na hakan zai iya haifar da babban matsala balle shi da kowa ya san munyi soyayya a baya. Shiru nayi ina sauraron ta ba tare da nayi magana ba domin duk abinda zan fad'a ba lalle ne ta gane ba, ni ba kukan rabuwa da shi nake ba kawai dai ina kukan tausayin sa ne da kuma halin da yake ciki yanzu wanda nasan da kyar in za'a mishi sassauci a kotu, koma menene Allah yasa ayi mishi saukin. Bayan munyi sallah la'asar muka ji sallaman Zafar a nan bakin parlour Inna, cikin azama Inna ta amsa tana gyara hijabin dake jikin ta dama bata cire ba ni kuwa ina kan sallaya ina ta rokon Allah ya fitar da Yaya na, sai da Inna tace mishi ya shigo sannan ya shigo kan shi a kasa kamshin turaren shi duk ya cika parlour. A nitse ya kara gaishe ta ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa ya amsa yana tambayan ya jikin Baba ta amsa da sauki ta tashi ta fita zuwa d'akin Baba dan dubawa ko ya tashi. "Let's go home" yace yana leken fuskata dan naki dagowa in kalle shi duk da ina jin yanda Inna ta zungure ni da kafa kamin ta fita sarai na gane nufin ta cewa in gaishe shi amma sai nayi kaman ban fahimci me take nufi ba na watsar dashi, " hello " yace yana shafa min gefen fuskata. Cikin sauri nayi baya dan ban san lokacin da ya iso gaba na ba sai jifa na yake da tsadadden murmushin sa mai kara mishi kyau, Ni bai san duk haushin sa nake ji ba kan me yasa ya dawo yanzu dan nafi son in kai dare kamin ya dawo. "Let's go home Baby yanda zan ji dad'in rarrashin ki kinga nan gidan Inna ne I will not be comfortable to do....." "Ni ban nemi rarrashin ka ba pls leave me alone" na katse shi sabin hawaye na taruwa a ido na, zai kara yin magana muka ji muryan Inna tana sallama cikin sauri ya koma inda yake zaune da farko nima nayi saurin share hawayen fuskata tare da fara magana bayan na amsa sallamn Inna kaman tun farko hira muke. "Eh ai tunda muka fito Baba yake ta bacci ban kara komawa wajan shi ba" na karashe da murmushi a fuskata, shima murmushin ya min yana kara tsunne kai ganin Inna ta shigo. "Muje mu kara duba jikin nashi sai mu wuce gidan tunda kince kina son mu isa da wuri" yace da d'an muryan da Inna zata iya jinsa domin da ta shigo direct tayi hanyan d'akin ta ba tare da ta kalli inda muke ba, takaici naji ya cika min ciki Ni yaushe nace zan tafi har yake min sharrrin wai ina son mu isa da wuri?" kanne min ido 1 yayi yana dariya kasa-kasa, Ni ko baki na murkuda mishi ina hararran shi ta gefen ido. Nuna kan shi yayi da yatsa yana kallo na alamun dashi nake, maimakon in bashi amsa sai kara murkuda bakin nayi murmushi yayi tare da cizon lip d'in shi na kasa, duk abinda muke akan idon Inna da take hango mu daga can cikin d'akin ta zuciyar ta fari ka ganin ma kwantar da hankalina. "Zareefa"! Naji muryan Inna tana kwala min Kira, amsawa nayi tare da nufan d'akin nata cikin natsuwa. "Ki tashi ku tafi kada dare yayi muku, ku biya kuyiwa Baban ku sallama sannan ku wuce" tace min lokacin da na karaso inda take zaune a bakin gadon ta. B'ata fuska nayi kaman zanyi kuka na bud'i baki zanyi magana ta katse ni da " bana son jin komai wuce ku tafi". Dole na fito ina kara b'ata fuska alaman saura kiris in fashe,yana ganin na fito shima ya mike yazo kusa dani ya durkusa kasa yayi mata sallama ta amsa da mu gaida gida, fuuu na fice na bar shi a baya zuwa sashen Baban mu na same shi zaune akan sallaya da carbi a hannun shi yana ja, kallon mamaki na bishi dashi wai yau Baba ne da carbi?. Da sauri na shanye mamaki na tare da dukawa kasa muka fara gaishe a tare da Zafar da shima shigowar shi kenan, amsa mana yayi da kulawa kaman ba Baban mu da na sani ba a baya daga nan godiya ya kara yiwa Zafar shi kuwa yana kara tsunne kai yana babu komai saboda kunya wasu kalaman Baban ke bashi. Abin mamaki dai baya karewa a duniya dan Baban mu ne ya maida hankalin shi kan mu kacokan yana mana nasiha akan hakuri da zaman duniya sannan yace mu tashi mu tafi gida kada dare yayi mana. Godiya muka mishi muka mike muka fito ni duk jikina yayi sanyi akan yanda Baban mu ya dawo lalle ba karamin wuya ya sha a hannun su ba daya canza farat daya. Shi ya bude min motan na shiga na zauna sannan shima ya zagaya ya shiga ya zauna yana kallon yanda na dawo so cool, marairaice fuska yayi kaman zaiyi kuka yace " Allah sarki ni,i na rasa ya zanyi komai nayi banyi daidai ba" Ban san lokacin da nayi murmushi har hakorana suka bayyana saboda salon da yayi amfani dashi yayi maganan dole yasa mutum dariya, dariyan shima yqyi ganin ya saka ni murmushi sannan ya ja motan muka hau hanya. [12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99