Chapter 87
Chapter 87
ya fita zuwa dinning fuskar shi d'auke da zallan farincikin ya samu logo na. A wajan cin abincin ma haka yayi ta ja na da hira wai abincin Inna na jiya yafi dad'i wai ko dai zamu koma kai mata kwanon mu kullum tana zubo mana abinci, dariya nayi sosai dan ba karamin dariya maganan nashi ya bani ba. Sai da muka gama yace min in shirya muje gidan mu in ya ajiye ni zasu wuce barrack da Baban mu yake da Baban Dije saboda yau da safen nan aka kira shi kan suje by 12. Cikin azama kuwa na koma d'aki na fad'a bayi dan yin wanka zuciya ta cike murnan yauma zan ga Inna ta, ban b'ata lokaci ba na fito cikin shirina da nayi da wata atamfa super golden da adon fari a jiki shiyasa mayafi, takalmi da jaka da na riko duk suka zama farare, d'an kunne da sarka da na saka suma white pure gold ne dan haka ba karamin kyau nayi ba. A parlour na tadda Zafar da shima kaman had'in baki ya saka wata tsadaddiyar shaddar shi fari sol da hula kindai da akayi da zare Mai golden da fari, takalman shi da agogon hannun shi suma duka farare ne sosai muka shagala da kallon juna kowa na yaba kyan da d'an uwan shi yayi a zuciya. Da kyar na samu na janye ido na daga kan shi na mayar kasa Ina wasa da gefen mayafina naji muryan shi" let's go" yace bayan ya sauke nauyayyen ajiyan zuciya. Gaba yayi nabi shi a baya zuwa inda motocin gidan suke ya bud'e min wata sport car fari na shiga na zauna sannan shima ya zagaya ya shiga yaja muka kama hanyan gidan mu, cike da nishad'i yake tukin sai murmushi yake ta sakewa shi kad'ai nima yau ban juya kaina gefe ba amma Kuma ba shi nake kallo ba ta kasan ido nake kalon shi. A kafar gidan mu yayi parking Baban Dije da kawun su 2 da suka zo dama suna tsaye suna jiran zuwan shi, zan bud'e kofa in fita naji yauma a kulle a shagwab'e na juyo ina kallon shi tsabanin jiya da nake aika mishi da mugun kallo. D'an dariya yayi yana d'aga min gira d'aya yace " in ba dan nayi locked ba da haka zaki fita ki bar ni babu sallama" turo baki nayi na d'auke kaina toh wani irin sallama ne da sai ya wani rufe kofa, bakin nawa da yake matukar birge shi zubawa ido yana ji Ina ma Ina ma..... Jin shiru bai min magana ba kuma bai bud'e min kofan ba yasa na d'ago muka had'a ido alaman kiss ya min da bakin shi sannan ya min blowing yace " take care of yourself for me princess" duk kunya sai ya rufe ni na rasa yanda zanyi shi Kuma sai murmushi da naji yayi mai sauti sannan ya bud'e mana Lock d'in motan , shiya fara fitowa sannan nima na fito ganin iyayen nawa yasa na Kara jin sabon kunyan kaman kasa ya bud'e in shiga haka nake ji sabida dadewa da mukayi a mota kada suyi mata wata fassara. Har kasa ya duka ya fara gaishe su nima na zagayo na durkusa na hau gaishe su cike da kunya, cike da kulawa duk suka amsa sannan ni na wuce cikin gida su kuma daga nan barrack suka wuce amsa Kiran Baban Hamis. Da yake an san da zuwan su babu wani shamaki ko dogon bincike aka bar su suka wuce, direct office d'in shi wani sojan yayi musu jagora suka samu gaba d'ayan su da abokan aikin shi suna jiran isowan su. Bayan gaishe-gaishe Baban Hamis yayi musu bayanin Baban mu bashida laifin komai hasalima shi wanda suka kama da wani dalilin shi daban wajan yi mishi wannan sharri, nan duk suka hau hamdala daga baya kuma aka kunna musu video da suka d'auka ta cctv camera suka kalla, duk mamaki ya cika su Baban Dije jin wai Abdulbasit yayan Zareefa shine yayiwa baba wannan d'anyen aiki, gaskiya ba zaka tab'a shaid'an mutum ba jibi yanda wannan mutumin yake komai kaman na Allah ne shi ashe mugu ne na bugawa a jarida?. "Tun jiya mun saka shi Abdulbasit d'in gaba ya kai ma'aikatan mu mab'oyan gang d'in nasu dake can dajin mafa Kuma Alhmdlh Allah ya basu sa'an cafke su duka yanxu haka duk suna hannun mu zamu tura su Abuja inda za'a yanke musu hukunci" cewan Baban Hamis kenan, nan ma kara godewa Allah sukayi sannan suka gode mishi shi kuwa Zafar taf ya cika saura kiris ya fashe dan lokacin an tafi d'auko musu Baba suke maida labarin irin soyayyan da mukayi yayan nawa. Suna zaune a wajan aka shigo da Baba da ko mikewa baya iyayi jikin sa kuwa duka ba kyan gani saboda kumburin da yayi hatta fuskan shima a kumbure yake, da gudu Baban Dije ya taro shi dan suna zuwa tsakiyar office d'in suka sake shi suka juya abin su. Duk kan shi sukayi suna yi mishi sannu , Baban Hamis hakuri suka basu tare da cewa zasu iya tafiya dashi ,haka suka fito dashi suna rirrike dashi suka saka shi a mota direct wani private hospital dake nan wulari area Zafar ya kai Baba, nan da nan kuwa suka karbe shi su fara mishi treatment su kuma suka fita masallaci dake nan cikin asibitin yin sallah azahar. Koda suka dawo rigima suka tarar tsakanin Baba da likitocin sunce dole ne su bashi gado yayi kwana 2 har yaji kwarin jikin sa shi kuma ya ce sam bai san zancen ba shi gida zai tafi, su Baban Dije suma sun saka baki amma fa Baba ya kafe kan cewa ba zai zauna ba. Zafar ne yace a bar shi su tafi gidan in yaso zai d'auko doctor ya rinka zuwa yana duba shi kullum, su Baban Dije sun gamsu da bayanin Zafar dan haka ba b'ata lokacin suka saka shi a mota sai gida. A gida kuwa dana shiga na iske kowa na cikin farinciki kaman Baban ya dawo duk yan uwa sun taru ana taya juna murna na samun labarin sa da akayi sai sakawa Zafar albarka suke da addu'oin gama wa da duniya lafiya. La'asar dai-dai mukaji muryan su Ibrahim suna ihun murna ga Baba ga Baba, har rigen-rigen fitowa muke a tsakar gida muka gan su suna kokarin wucewa dashi d'akin shi. Duk sai murnan mu ya koma ciki ganin yanayin shi kad'ai ya tabbatar mana ba karamin wahala ya sha a hannun su ba, rufa musu baya mukayi jiki a sanyayaye suka kwantar dashi a parlour shi nan kowa ya shiga yi mishi sannu ans barka da arziki. Gwaggo Aisha da tunda abin nan ya faru bata tab'a shiga cikin mutane ayi jaje da ita ba sai kawai ganin ta mukayi sulum ta fado parlour harda kukan munafurci wai ai tunda aka kama shi ta shiga halwa tana addu'a bata fito ba sai yau da taji labarin fitowan shi. Cike da mamakin karya da ta sambad'o kowa yake kallon ta amma babu wanda yace mata wani abu sai Baban Dije da ya shiga mayar mana labarin yanda baba ya shiga hannun sojoji dalilin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99