Chapter 81
Chapter 81
dashi sai ya nemo wanda a baya yake jin haushin sa ko kuma Wanda ya tsaya mishi a rai ya mishi cune , baiji ba kuma bai gani ba za'a je dashi a rufe shi, wani shikenan mai kara jin labarin shi saboda bashida gata ko kuma a kashe shi gaba d'aya a shafe labarin shi amma insha Allah zamu samo bakin zaren tashi muje barracks d'in su Dady muji kasancewar shi baya yarda da zalinci kuma baya yarda ayi a gaban shi sai dai in a rashin sani, shiyasa ko wani case in ya shigo hannun shi sai yayi bincike sosai kaman wani police kamin ya yarda a yanke hukunci" ya karasa yana mikewa tsaye yana kwalawa matar shi kira. Fitowa tayi da sauri tana karasa daurin dan kwalin ta yace mata "zamu d'an fita ne da Zafar " D'an Bata fuska tayi alamun bata ji dad'in hakan ba cikin lallashi yace " don't worry I will not stay long yanzu zan dawo". fuska ta sake tana murmushi tace " shikenan my love sai kun dawo Allah ya tsare" da Ameen" ya amsa Yana kissing goshin ta sannan ya juyo ya kalli Zafar da ya tsaya musu kallon sha'awa yana ji inama haka zaman mu yake a gida. Maimalari barracks suka nufa bayan sun fito suna hirar su jefi-jefi a cikin motan har suka iso bakin gate da sojoji suke birjik suna binciken ababen hawa da zasu shiga ciki, suna duba motan su ganin Hamis ne yasa suka basu hanya suka wuce, haka sukayi ta wuce gates sun kai 4 kamin su shigo ainihin inda office d'in Baban Hamis yake... Basu karasa ciki ba saida akayi musu iso sannan suka shiga katon office d'in nashi daya k'awatu da kayan alatu sai kamshi da sanyin ac ke tashi, da murmushi ya tare su yana daga ina suke haka yana nuna musu wajan zama. Zama sukayi a inda ya umarce su sannan suka gaishe shi ya amsa kamin su fara koro mishi bayanin suka ji knock a kofan office d'in wani soja ne ya bud'e ya shigo da wasu files a hannun shi ya kame a gaban shi tare da salute sannan ya ajiye files d'in kan makeken table dake gaban su ya kara salute ya fita. Jawo files d'in yayi ya fara duba su a tsanake yace " uhum ina jin ku ". Hamis shi ya korowa Baban shi bayanin da Zafar ya mishi tsab ba ragi ba kari, shi Kuma Zafar shiru yayi har ya gama fad'a mishi komai amma bai dago ya kalle su ba ya cigaba da duba files na gaban shi har zuwa wani lokaci mai dan tsawo sannan ya ajiye su a gefe ya d'ago ya zubawa Zafar ido yace " menene sunan nasa kuma yaushe hakan ta faru?" " Mallam Hassan sunan shi kuma yau kwana 3 da kama shin". Gyad'a Kai yayi cike da gamsuwa yace" muna da similar case da wanda ka fad'an nan amma shi ba yanda ba muyi dashi ya gaya mana gaskiya ba yaki cewa komai , so mun had'a su waje d'aya sannan an saka musu cctv camera a d'akin da suke dan mun san dole sai sunyi magana a tsakanin su". Duk shiru sukayi suna sauraron shi ya koma ya jingin da kujeran da yake kai yana jujjuya da shi yace " wannan files d'in ma na bayanan su ne bari mu tabbatar da abu d'aya zuwa gobe sai in neme ku ko?"yace yana duban su. Godiya sosai Zafar yayi mishi sannan sukayi mishi sallama suka shiga mota suka kama hanyan gidan Hamis sai dai bai shiga ciki ba a bakin gate d'in gidan shi Zafar ya sauke shi da yake a motan shi suka tafi shima ya nufo gidan mu . A can barracks din kuwa bayan fitan su Zafar Baban shi ya kira wayan da suke aikin tare kan su same shi a office d'in shi, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba suka taho su 3 kowanne su sai da ya fara mika gaisuwan shi gare shi wanda hakan yana nuna cewa shine babban su, gyad'a Kai yayi tare da yi musu alaman da hannu kan su zauna ba musu suka nemi waje suka zauna . "These are files about those people case yanzu sergeant Ibrahim ya kawo min su " yace yana ciro wata 'yar karamar memory card a cikin gidan ta ya saka a system dake gaban shi yayi wasu latse-latse sai ga shi ya fara nunawa ta can gefe kaman tv dukan su kuwa suka maida hankali kan screen d'in ga su Baba sun fito b'aro-baro a jiki suna zaune da kumburarrun fuskokin su. Shiru ranan da aka Kai su basuyi wani magana mai mahimmanci ba sai da washe gari da yamma sannan suka zo inda suka ga sun fara magana a tskanin su.. " Wai kai har yanzu saboda dakikancin ka baka gane ni bane bayan duk bayanin da nayi maka?" Cewar wanda ya kira kan shi da Abulbasit ma Baban mu. Murmushin takaici Baba yayi mishi yace" in nagane ka da ban gane ka ba duka d'aya ne tunda har ka iya min irin wannan kazafin ka kawo ni nan, ban san me nayi maka ba kake son ganin baya na......" Dariya da Abdul basit ya kece dashi shi ya hana Baba karasa maganan da yayi niyya ya zuba mishi ido kawai yana bin shi da ido dan shi bai ga abin dariya a cikin wannan halin da suke ciki ba. "Bani kad'ai ba kayiwa ba hatta iyalan gidan ka sun matukar cutu da mugun halayyarka, tayaya Allah zai baka mata da yaya ka mayar dasu abin wulakancin ka, ko abinci baka basu sun ci ba balle aje ga wasu abubuwan rayuwar na yau da kullum. Ko a yanda na shigo rayuwar Zareefa na d'auki nauyin karatun ta da sauran su amma a matsayin ka na mahaifin ta da Allah ya daura maka alhakin kiwon su baka tab'a damuwa ka san wanene ni ko kuma ka damu ka san a ina suke samun kudin ba saima nuna zalamarka da kwad'ayin ka akan abinda suke samu , farkon zuwa na da niyyan cutar da ita nazo domin kuwa mai gida na yana safaran yara kanana sai dai yanda naga rayuwar da take ciki da kuma yanda mahaifiyar ta ta nuna min ita ba mai son abin duniya bace duk da talaucin da suke ciki, ba karamin burge ni tayi ba sannan ta goge bakin niyya dake zuciya ta Allah ya darsa min tausayin su a raina tun daga wannan rana nake taimaka musu da zuciya daya. Ni maraya ne na taso banida kowa Kuma wannan rashin gatan shi ya jefa ni a halin da na tsinci kaina a ciki, ni dai na taso na ganni Ina garari a gari ban san kowa nawa ba cikin yawon da nake Allah ya had'a ni da Emeka shi ya kasance uwa da uba a gare ni ya saka ni makaranta kasancewar shi Christan bai sa ya canza min suna ko addini na ba hakan ya sa nima na rike shi da hannu 2 inayi mishi biyayya kaman shi ya haife ni" dago kai yayi yaga Baba ya zuba mishi ido yana sauraron yayi lakwas
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99