Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Yana kumbure-kumbure kaman karamin yaro ya shige bathroom d'in shi dan yin wankan, dariya Sadeeq yayi sai da yayi Mai isar sa sannan ya ciro mishi kayan da aka tanada mishi domin d'aurin auren. Sadeeq shiya taya shi shiryawa sunayi suna fad'a shi dai Sadeeq dariya yake ta mishi ganin yanda yake turo baki kaman wani karamin karamin yaro mai shagwab'a. Farar dok ce mai matukar tsada yasa mai d'aukan ido yasha aikin hannu wato (gatau) hula takalmi duk farare ne wrist watch na hannun shi shima na pure diamond ne sai kamshi na musamman yake kana ganin shi kaga haddaen ango, suna gamawa suka fito parlour inda abokan sa suke jiran sa. Yana fitowa ihu suka fara suna mishi kirari saura na tsokanan shi dan sake fuska yayi ya dan biye musu suka tab'a wasa sannan suka raka shi wajan Mom. Tsakar gidan babu mutane sosai dan haka basu sha wahalan karasawa cikin ba , parlour Mom a cike yake ana ta hidima suna ganin shi wata mai murya ta saki wani irin gud'a da ya cika gidan nan da nan sukayi kan shi ana ta wasa da dariya da kyar ya samu ya karasa sama d'akin Mom, tana zaune cikin kawayen ta da 'yan uwan ta suna hira. Ido ta zuba mishi har ya karaso ciki zuciyar ta kuwa kaman farar takarda yau Allah ya nuna mata auren tilon d'an ta. Albarka suka yi ta saka mishi bayan ya suguna har kasa ya gaida su, Mom harda hawayen farinciki dan yau babbar rana ce mai babban tarihi a rayuwata. Kiran da Abba yayi mishi ne yasa shi mikewa ya fita ya tarar da tawagar Abba har sun fara tafiya, ba b'ata lokaci shima ya shiga cikin abokan sa suka kama hanya. Akwai wani babban masallacin juma'a a bakin layin mu kuma a nan ne za'a d'aura auren, so duk a can wajan layin sukayi parking wasu ma ko wajan parking din basu samu ba saboda yawan motocin dan haka wasu suka fara shigowa cikin layin namu Dan samun wajan parking. Masallacin kan shi ma har yayiwa mutane kad'an wasu basu samu shiga ba ko ina ka duba taron al'umma ne, in wanda bai sani ba yazo yaga taron zai zata auren 'yar babban mai kud'i ake ba ko dan siyasa ba 'yar Mallam Hassan ba. Baba yau in ka ganshi kaman yayi hauka saboda farinciki harda su governor a daurin auren 'yar shi harda manyan kusoshi na gomnati ,ba'a tsaya b'ata lokaci ba aka daura aure na da Zafar kan sadaki naira million 2. Muryan maroki da ya fara shelan d'aurin auren har cikin gudan mu a lokacin ina tsakar gida cikin mutane dan Inna ta saka ni fitowa waje gaida 'yan uwan Baban mu, a take wajen ya kacame masu farinciki suka fara masu bakinciki ma nayi, ni kuwa ji nayi kaman an saka ni a cikin kankara haka naji jiki na yayi wani bala'in sanyi tare da zazzab'i mai zafin gaske ba shiri na nufi bangaren mu kamin na karasa d'aki na har na fara rawan sanyi ina shiga na kwanta na lullub'a da bargo ina hawaye a haka Aunty Batool tazo ta same ni cikin rarrashi tayi min nasiyan yadda da kaddara sannan ta bani magani na sha bata bar d'akin ba sai da taga bacci mai nauyi ya d'auke ni sannan taja min kofa ta fita. Anan d'aura aure su Abban Zafar gaba daya suka wuce reception da Abba ya had'a a nan cikin gidan shi, su Zafar ma bayan shi suka bi duk yanda Sadeeq yayi dashi akan su tsaya ya d'anyi pics tare dani saboda tarihi yaki ya shiga mota suma suka rufa mishi baya. Sai yamma naji d'an karfin jiki na aka kara canza min kwalliya zuwa walima cikin abaya da Inna ta siya min saboda walimar ba'a dad'e da farwa ba yan gidan su Zafar suka kawo lefe na da ya kusan haukata mutanen gidan mu dana anguwan baki d'aya, nima a yanda naji Maryam tana lissafowa ban tab'a jin labarin irin su ba. Bayan an gama cece-kucen ganin lefen suma suka shiga cikin mu akayi walimar dasu inda Mallama Falmata Zanna ta wa'azantar kan biyayyan aure ko Inna ce tace tayi hakan oho, sai kusan magariba taro ya watse bayan anyi rabon manyan jakkuna masu d'auke da Al'quran ma daidaici sai sallaya da hijabi,nayi mamakin yaushe Inna ta shirya haka ko dan ban maida hankali ga bikin bane ban sani ba. Basu bar ni nayi alwalan magriba sai da nayi wanka da ruwan turare sannan nayi alwala na fito nayi sallah ina kuka ganin cewa dai da gaske suke dan sai shirye-shiryen kai ni suke shirya ni sukayi cikin atampa super mai ratstsin silver a jiki , d'an kunne da sarka da suka saka min suma duk silver ne sannan suka nad'a min laffaya mai masifan kyau shima silver color aka fito dani wajan su Inna da yan uwan ta. Nasiha suka fara min kan hakuri d'aya bayan d'aya Inna ta dai tana gefe tana kallon yanda nake kuka kaman raina ya fita, Maa ce ta katse ta tace itama tace wani abu mana. Murmushi mai ciwo tayi muryar ta na rawa tace" me zancen Maa da ku baku fad'a ba, ni sai dai inyi mata addu'a Allah yaa...." Kukan da take rikewa ne ya kwace mata ta tashi cikin sauri tayi d'akin ta, kara kuka na nayi na mike zan bita suka rike ni ina musu magiya da roko amma basu saurare ni suka sada ni da d'akin Abba yana zaune shi kad'ai sai washe baki yake. "Sai ku fita ku d'an bamu guri ni da 'yata ko" yace musu bayan sun zaunar dani a tsakiyar parlour shi, Aunty Batool har ta tsaya da nufin gasa mishi magana Aunty Fatima ta mata alama da ido da tayi shiru kawai su fita, ba dan ta so ba suka fita tana mitan wai dama ya san ni 'yar sace? Suna fita ya juyo gaba daya gare ni yana kara washe baki yace " ke kuma in banda kuruciya menene abin kuka anan, Allah ya azurta ki da samun irin wannan mijin da babu kamar sa duk maiduguri yaushe kuka hadu dashi amma ga yanda ya sauya mana rayuwa baki d'ayan mu, Wannan ai abin alfahari ne a gare mu ba ki saki baki kina kuka ba d'aurin auren ki har da gomna fa suka zo" ya karasa feeling very proud Yana gyara Zama. "Abinda nake so dake shine kada kice zaki manta da gida dan kin samu daula ya kamata ki san yanda zaki rinka tatso wasu abubuwa daga gare shi kina aiko mana ai kin gane abinda nake nufi" ya karasa tare da zuba min ido gyad'a mishi kai nayi hawayen takaici na zubo min dan ni da yace su Aunty's dina su fita na zata zai min nasiya ko kuma ya rarrashe ni kan auren da ya d'aura min ashe shi tunanin shi daban, wai yaushe ne Baban mu zai canza?? Na jehowa kai na tambayan da babu mai bani amsa. D'aga murya yayi ya kira su Aunty Fatima suka zo suka fita dani direct sai mota suka sakani suna ta zabga guda Aunty Fatima da Aunty Batool

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99