Chapter 33
Chapter 33
da ban tab'a ji ba a rayuwa ta, ina ji motan ya fara tafiya amma na kasa bud'e ido na can naji Sadiq d'in yana tambaya ta wani anguwan zasu sauke ni? Sai da naji a jiki na alaman ana kallo na ban damu da in bud'e ba saboda nasan sunan anguwan mu da na fad'a ne ya bashi mamaki kasancewar duka gidajen talakawa ne a anguwan. "Sai ki nuna mana inda zamu bi mun shigo anguwan naku" muryan Sadiq ya katse min tunani, a hankali na bud'e ido sannan na nuna mishi hanya da zamu bi can nesa da gidan mu nace ya sauke ni anan. Parking yayi daga gefe na bude kofan na sauka sauka a hankali cikin muryana mai sanyi da baya fita sosai nace " nagode jazakallahu khairan" na kama hanyan gida ina layi,da ido Sadiq ya rakani har na shige ciki. Gyaran murya Zafar yayi wanda ya dawo da hankalin Sadiq ya juyo yana kallon shi yace" sai ka gaya min ma'anan kawo ta gida sannan dan wulakaci kaja baki kayi shiru na tabbata bata san mu 2 muka kawo ta ba. "Mu tafi Mallam ba wai ka kama min tambayoyi ba" Zafar yace hankalin sa na kan wayan shi, girgiza kai kawai Sadiq yayi yaja motan suka fita daga layin dan wannan halin abokin nashi ya ci ace ya saba. Da kyar na kai kaina d'akin mu na zube a gefen Inna da take kwance a kan gado,a firgice ta tashi zaune saboda ta fara bacci kuma bata ji shigowa ta ba. "Wani irin rashin hankali ne wannan zaki shigo min d'aki ba sallama sannan kuma ki fad'o min a ka sai kace wata 'yar maye, ko daga wajan bikin kika koyo ne..." Shasshekan kuka na da taji shiya dakatar da ita daga fad'an da take min cikin fargaba ta d'ago ni ta fara dudduba jikin na tana tambaya ta meya faru??? "Inna Yaya na yau kusan sati da yin tafiya amma har yanzu babu labarin shi ga wayar shi bata shiga, Inna tsoro nake ji anya yana lafiya kuwa? Yaya na ba zai tab'a mantawa dani ba har na tsawon sati ba tare da yaji lafiya ta ba Inna kin..." Rufe min baki da Inna tayi da hannun ta yasa nayi shiru ina kallon ta hawaye na bin fuska ta. "Babu abinda ya same shi insha Allah yana cikin koshin lafiya,bana son kina sawa kanki damuwa dayawa ki bari zuwa gobe da safe sai mu san yanda zamu bullowa lamarin" duk cikin rarrashi take min magana hannun ta kuma na kaina tana shafa gashina daya sha gyara ya kwanta yayi lub. Jin ina sauke ajiyan zuciya kuma numfashi na fita d'aya-daya yasa ta gane nayi bacci, gyara min kwanciya tayi tare da zuba tagumi ta zauna tunani yanda zata bullowa wannan al'amarin domin babu abinda yake d'aga mata hankali kaman ganin tilon 'yar ta cikin tashin hankali, balle ma wannan na soyayya. Kusan raba dare Inna tayi kan sallaya tana nafilfilu tare da kai kukan ta wajan Rabbi izzatti ya shiga lamuran 'yar ta ya zaba min abinda yafi alkhairi. Koda gari ya waye da kyar na tashi daga kan gado nayi sallah na kara komawa na kudundune cikin bargo ina rawan dari saboda sabon zazzab'i da ciwon kai daya tsanan ta min, cikin matukar damuwa Inna ta had'a min tea mai kauri ta lallab'a ni na sha kad'an sannan ta b'allo paracetamol 2 ta bani tace in sha zuwa azahar in babu sauki sai mu tafi asibiti. Cikin ikon Allah ina kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba dani sakamakon jiya ban samu ishasshen bacci ba, gaba d'aya fita daga d'akin Inna tayi wai kada tayi wani babban motsi ta katse min bacci anan ta cigaba da ayyukan ta cikin dauriya. Kaman a cikin mafarki naji waya ta tana ringing, da kyar na bud'e ido na da suka min matukar nauyi. A zabure na tashi na zauna ganin sunan da na gani yana yawo kan screen d'ina, a hanzarce na d'aga kiran na kai kunne na kamin ya min magana na fashe mishi da matukar kuka kaman zan shid'e. "Ki fito ina waje" yace min cikin wata murya da ban san shi da ita ba, amma duk da haka ban tsaya b'ata lokaci ba na diro daga kan gado dama da hijabin da nayi sallah asuba a jikina na kwanta dan haka takalmi kawai na zura na fito kofar gida ko lura da Inna dake tsakar gida banyi ba burina shine inje in saka shi a idanu na ko zanji sanyi a cikin raina. Inda ya saba parking anan na gan shi tsaye ya juyawa kofar gidan mu baya haka kawai sai naji jikina yayi sanyi sosai a haka naja kafa na isa inda yake cikin murya na daya dashe saboda kuka da nasha nayi mishi sallama. Amsawa yayi yana juyowa muka fuskanci juna, kasa tsaida hawayen ido na nayi ina kallon fuskar shi mai sanyaya min rai nace" barka da zuwa Yaya na aikin ne ya rike haka, wannan karon ka dad'e sosai har ya saka ni cikin matukar damuwa ga number ka bata shiga". "Lafiya lau mana, hmmm kema dai Zareefa meye abin damuwa anan kin san in nayi tafiya bana saka miki ranan dawowa balle kice har kwanakin sun wuce ban dawo ba sannan tun a baya na gaya miki wajan babu network shiyasa bana iya kira ko a kira ni". Ya bani amsa hankali kwance. Amsar yasa duk naji wani iri amma na daure tare da share hawayen fuska ta da gefen hijabi na ina sakin mishi murmushin da nasan yana saka shi farinciki nace" hmm ka gama komai ka yanzu dan wallahi in akayi mana aure ba zan yarda kana tafiya kana bari na ba kafar ka kafata". Sun glasses na fuskan shi ya gyara yana kallo na ta ciki yace" Zareefa kenan kin ga matsalar ki kenan wanda yasa nake ganin ba zamu iya zama inuwa d'aya ba". Rass-rass naji zuciyata ta wani irin bugawa da har sai da na kai hannu na kan tsaitin wajan ido a waje nake kallon shi dan na rasa bakin magana, can dai nayi dariya kad'an ganin bai kara ce min komai ba nace " Allah Yaya na ka bar min irin wannan wasan zaka saka zuciya ta bugawa wallahi". "Wasa!! Wasa fa kika ce, u see kina da matsaloli dayawa a rayuwar ki da in mutum ya duba koya auna ba zai fara ma kusantar inda kike balle maganan aure ya shiga tsakani, ke ko irin kunyan nan da aka san mace dashi baki da ita kullum maganan ki d'aya aure-aure mtsw..." Yaja dogon tsaki yana kawar da kai gefe kaman yaga abin kyama. Ko kifta idona na kasa yi balle in iya cewa wani abu kawai ji nake wasa yake min jira nake in ga ya juyo yace min wasa yake amma ko kallon inda nake bai kara yiba. Murya na rawa da son kara tabbatarwa kai na ba mafarki nake ba nace" Yaya na kaine kuwa ,nice fa kanwar ka Zareefa". "Zareefa my foot me mutum zaiyi da macen da bata kamun kai, tunda can daure zuciya ta nake tare da saka ran zaki canza wata rana sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99