Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

wani ne zai kwace mishi. "Bintu.... Bintu Allah yayi miki albarka yanzu wannan duka a dalilin 'yar albarka na samu dama ai wannan yaron kana ganin shi kaga dan albarka shima, ko ba shi bane na gan su tare kwanakin baya?" Ya tambaya yana ta washe baki. "Shine mana ma'aikacin hukuma ne ai, ni ko soja tace min ne ko d'an sanda, na manta dai" Inna ta bashi amsa ta kauda kai kada dariya ya sub'uce mata ganin yanda nan da nan Baba fuskar shi ta canza ya koma kalan fargaba da tsoro. "Oho ashe hukuma ne, toh yayi kyau madallah da har ina cewa in naga ya dawo zanje in mishi godiya kuma muna gaisawa ashe yafi karfina". Baba ya fad'a bakin shi na rawa. Inna had'iye dariyar ta tayi ta juyo tana kallon shi can ta ce," haba Mallam wani irin magana ne wannan, uhum sirikin naka shine yafi karfin ka?" "Kema dai Bintu da son jan zance kike kin san bana shan inuwa d'aya da hukuma, Allah yajikan Baban ki ai ta nan ya rinjaye ni nayi ta bashi kud'i mudin in ya tambaya ko a wani waje sai naje na ciwo bashi na kawo mishi duk da shi na san yayi ritaya amma nake tsoron sa balle wanda yake saurayi mai jini a jika? Hmmm ke dai kawai ki cewa 'yar albarka ta mik'a godiya ta a wajan sa". "Toh shikenan Mallam zan fad'a mata" Inna ta bashi amsa. Tun daga wannan rana Baban mu shima ya koma d'an gaye daga ya canza wannan sai ya cire wancan har a majalisan su yanzu shi yake mulki kowa so yake ya zama makusancin shi, maimakon kud'in nan daya samu ya juya su a kasuwanci suyi albarka ya rike gidan sa kaman kowani magidanci saima lalacin nasa ya karu d'an masarar da yake sayowa ma yanzu ya daina ba abinda ya shafe shi da lamarin cikin gida illa ya d'au wanka ya shigo d'akin mu yayi breakfast ya tura kud'i a aljihu yayi ficewar shi. Aike kuwa Yaya na bai daina yi mishi na kaya dana kud'in duk bayan kwana bibbiyu yake aikowa, ranan da ya rasa na kashewa kuwa ni yake tambaya in bashi dan ya san ko ya tambayi Inna ba bashi zatayi ba. Wahalar da muke ciki yanzu ya dawo kan Inna Asabe dan itace mai yara dayawa a gidan ga babu abinci babu jari balle ta daurawa yara sana'a, kananan yaran ta kullum a d'akin mu suke cin abinci. Rannan Gwaggo Aisha bata gida Inna ta fito ta kawo mata rabin bugu na shinkafa da kuma carton na taliya sannan ta bata dubu goma tace tayi jari ita mai yara kanana zama haka ba zai yiwu ba. Kuka wiwi ranan Inna Asabe tasa tana Inna ta yafe mata abubuwan da tayi mata a baya gashi wacce ta biyewa sukayi mata rashin mutunci yanzu babu ruwan ta da ita koda zasu wuni su kwana basu ci ba kuma basu sha ba ko a kwalar rigar ta sai wacce suka wulakanta itace yau ta mutumta ta haka? Inna Asabe tun daga wannan rana ta samu abinyi itama kuma tun daga wannan rana ta fita harkan gwaggo Aisha tsakanin ta da Inna ta kuma sai mutunta juna. ********************************** *Rubby private school* makaranta ce mai matukar tsada ta 'ya'yan masu kud'i ko manyan 'yan kasuwa, anan Yaya na ya nemo min gurbin karatu na fara fita ss1 abina kuma ya ajiye min mai napep da yake zuwa ya kaini kullum da safe kuma ya d'auko ni in an tashi, wata nayi kuma ya biya shi kud'in sa. Maryam Alhaji idris itace seat mate d'ina tun ranan mu na farko da had'uwa muka kulla k'awance da ita domin Allah ya had'a jini mu sosai. Kasancewar Maryam tana kusa dani yasa al'amarin makarantan yazo min da sauki, sosai take taimaka min kana ganin ta kaga wayayyiyar yarinya 'yar gayu tsabanin mu namu wayewar kauyenci ne a wajan su. Ba'a magana da hausa sai turanci a makarantan abinda ya fara bani matsala kenan sannan kuma in ana koyarwa shima sai turanci ko kad'an basa d'an sirka hausa yanda irin mu zamu fahimta sai dai in an gama koyarwa Maryam ta kara wayar min da kai. Term d'aya kawai mukayi na canza nayi wayewan 'yan gayu ga turanci ya fara zama a bakina domin makarantan ba wasa. A wannan lokaci ne kuma aka saka bikin Hajara da Alhaji data samu ,wata biyu kawai aka saka Gwaggo Aisha sai habaice-habaice take 'yar ta zata je gidan hutu gidan kud'in halal bana yankan kai ba, wai kud'in Yaya nane na yankan kai. Suna ta shirye-shiryen bikin su mu kuma muna shirye-shiryen walimar saukar mu a islamiya dan haka kona dawo daga makaranta banida lokacin zama sai na islamiya dan hadda muke kuma abinda ya rage mana bai fi izu biyar ba gashi har kuma date d'in da aka saka na saukan ya kusa shiyasa muka bada himma sosai, a yanda aka saka date d'in in anyi bikin Hajara da sati zamuyi walimar namu. A boye Gwaggo Aisha filin ta na gado ta sayar tayiwa Hajara kayan d'aki dashi wai 'yar ta zata shiga babban gida kada su raina ta, ba laifi kaya kam sunyi kyau dan a bakin Dije nake jin wai Italian bed 'yan dubu dari uku ta saya mata da kujeru dubu dari da hamsin, Allah ya sanya alkhairi nayi na shi a wajan toh me zance ? Nida anko ma sunce kada na kuskura inyi na bikin d'akin su. Ina gani su jamila suna ta rawan kai a shiga a fita sai shirye-shirye take itama wai zatayi nata shagalin daban dan haka ankon ma nata kala daban ne da k'awayen ta. Ana saura sati d'aya gidan mu ya fara cika da baki 'yan uwan Baban mu da nasu Gwaggo Aisha ga hayaniya ga rashin zaman lafiya saboda kullum sai an raba fad'a, ba shiri na tattara kaya na zuwa gidan Maa ko zan samu natsuwa in ida hadda ta kuma a zuciya ta na kuduri sai sun gama bikin su zan koma gida. Ana gobe daurin aure da yamma Yaya na yazo amma ya kasa parker motan shi inda ya saba saboda jama'a sunyi yawa anata shiga da fice sai gaba da gidan Maa yayi sannan ya kira ni a waya na fito wajan shi. "Meke faruwa a gidan naku ne naga jama'a haka?" Ya tambaya ko gaisuwan kirki ba muyi ba. Turo baki nayi ina mai jin haushi dan duk wanda zai min zancen auren nan haushi yake bani tayaya za'a ce wai ana biki a gidan ku amma ace wai an hana ka yin anko wani irin kiyayyane, me nayi musu da zafi haka?? Ina aiyana haka a raina naji hawaye ya zubo min wanda ya tayar da hankalin Yaya na ya shiga tambaya ta meya faru cikin damuwa. Maimakon in bashi amsa sai na fashe mishi da kuka tsakani da Allah, nan ya kara ricewa yana tambaya ta amma na kasa magana sai shassheka nake. Da kyar nayi shiru shima sai da naga hawaye a idon shi ba shiri na had'iye kukana na fara goge hawaye na da hijab. Sai da muka natsu sannan ya ce," in ba

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99