Chapter 57
Chapter 57
nazo zan wuce na zata zai bar min kofan in fita ne sai naga matsawa kad'an yayi yace in wuce,ban san lokacin da na daga kai na kalle shi ba naga ya wqni kankantar da Lulu eyes din shi yana kallo na. " Toh... Z...an ...wuce" nace mishi murya ta na rawa. Na hana ki wucewa ne?" Ya tambaya Yana kara gyara tsayuwar shi, girgiza kai na kawai nayi ina maida shi kasa, da hannu ya min alama da inzo in wuce. Tafiya na fara yi kaman wacce take tsoron taka kqsa ba dan komai ba sai dan sanin in zan wuce sai jikina ya gogi nashi, karkata jiki na nayi sosai yanda ba zai hadu da nashi ba, na ko yi sa'a dan ko bai hadun ba har na kusa fita naga ya saka hannuwan shi duka 2 ya tare kofan ya zama banida daman fita Kuma banida daman komawa ciki. "Ni kike guduwa da wani kazamin jikin ki, ni banyi kyaman zaki had'a jikina da naki ba sai kece zakiyi?" Jikin na karkarwa kawai yake tsaban tsoro ban tab'a samun kusanci da d'a namiji kaman haka ba sai yau so ban san ya zan kwatanta muku halin da na shiga ba a wannan likacin. Sai da yaga ya gama tsoratani sannan ya bani hanya, haba kaman in kifa haka na fara sauri na shiga d'akin na maida kofa na rufe na jingina a jikin kofan ina maida numfashi, sai da na dawo hayyaci na sannan na tsaya kallon d'akin ko ina fes yake a gyara kaman d'akin mace sai kamshi ke tashi, ajiyar zuciya nayi na wuce bathroom din shima dai fes yake. Haka dai na had'a ruwan omo da hypo na goge ko ina na bayin nan ya kara kyalli da walwali, sai da na tabbatar komai yayi na bude kofa na fito. A razane na koma baya ganin shi tsaye a bakin kofan daga shi sai dogon wando ya cire rigan jikin shi, rab'awa nayi na wuce shi Kuma ya shigah har zai rufe kofa naji shi yana cewa in tabbatar na gama gyaran d'akin ya fito. Da toh na amsa mishi yana shiga na fara gyara mishi gado da jera pillows sannan na fara mopping din d'akin inda babu carpet, har na gama zan fita wata zuciyar ta zuga ni da yanzu shikenan ba abinda zanyi in rama yaci bulus kenan?? Bakin kofan bathroom din na dawo hankali na zubar da ruwan omo kad'an yanda ba zai iya ganewa ba na fita da sauri ina addu'an Allah yasa ya taka wajan da na huta takaici da ya guma min yau. Jikin kofan na d'aura kunne na na tsaya jiran fitowan shi, aiko ban dad'e da tsayuwa ba naji karan fad'uwa muryan shi da karfi yace " ouch my back" haba da gudu na koma daki Ina dariyan mugunta raina fari kal. [6/16, 9:19 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *35&36* Zaune take kan sallaya da carbi a hannunta tana ja a hankali tare da kurawa waje d'aya ido,kallo d'aya zaka mata ka gane tana cikin damuwa kullum cikin wannan yanayi take tunda aka fitar dani daga gidan sai dai in damuwar yayi mata yawa,sai tayi nafila tana kai kukanta wajan mai kowa mai komai kan Allah ya bamu zaman lafiya mai d'aurewa. 'Yan biki duk sun watse tun ranan yini saboda an riga da an daina zaman bakwai sai dai gobe ne satin auran kuma a goben uwa take zuwa ganin d'akin 'yar ta amma ita tana ganin ba zata je ba hakan zai fi mata kwanciya hankali bata son taje ta ganni cikin wani yanayi ko kuma cikin tashin hankali hakan zai tsaya mata a rai ya hana ta sukuni, ta yanke shawaran zamanta a gida ta bini da addu'oi samun zaman lafiya. Tana cikin zancen zuci baba yayi sallama ya shigo,sallamar nashi ne ya katse ta ta juyo tana kallon shi tare da amsawa a hankali tana bin shi da kallo yanda ya sauya zaka ce wani hamshakin mai kud'i ne,duk mamaki ya cika ta dan zata iya cewa tunda bikin nan yazo sai yau ta saka shi a ido saboda taga bashi da niyyan yin komai ya zauna akan abinda Abban Zafar yace na cewa kada suyi min komai su zasu yin min. A lokacin ta nemi su zauna suyi magana ta fahimta bai kamata su sake musu komai ba kaman wacce bata da gata koda kayan d'aki daya ne ya kamata suyi min gudun gori watarana amma yaki sauraronta sam,wai tunda sunce abari a bari kawai itama tunda ta lura da takun shi ta fita harkan shi tayi duk abinda Allah ya hore mata dana 'yan uwa da abokan arziki cikin ikon Allah kuma asiri ya rufu. Zama yayi a kan kujera ya d'auki remote ya kara volume na TV data rage,kaman ta share shi sai kuma taga koma yaya ne shine gaba da ita,tashi tayi ta kowa mishi ruwan sanyi da snacks na biki ta ajiye a gaban shi ta gaida shi tana zama a gefen shi. Amsawa yayi sannan ya d'an sha ruwan da ta kawo mishi yana kare mata kallo yana murmushi yace"kinga yanda kika dawo kaman kece Amaryar gaya min menene sirrin?" murmushi kad'an tayi bata ce komai ba wai yau ita yake fad'awa haka ya manta duk munanan kalamai da yake furta mata da kuma aurar dani ga wanda ba son sa nake ba.......... "Tunanin 'yar albarka kike ne ,nima nan kullum sai nayi tunanin ta a raina toh ya za'ayi dole ne kiyi hakuri kuma kiyi murna tunda tana gidan hutu" yace yana gyara zama "Yauwa ni abinda ya kawo ni daban, kin gan ni nan wallahi bikin nan ya cinye min duka kud'ad'en hannu na shine nace bari inzo ki bani wani abu na san 'yar ki na aiko miki tunda maganan da nayi ta jaddada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99