Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,298 words 0 views Progress saved
Download Book

hura wuta tayi ta d'aura abin karyawa duka gidan abinda tun tasowa ta ban tab'a ganin anayi ba, spaghetti ta dafa mana harda kifin gongoni da take d'ibawa su kakata kayan a nan data bud'e wani kwali taga duka shine a ciki. Kamshin girkin yauma ya cika ko Ina har ta gama, tana gamawa ta samu tire ta zuzzubawa yaran gidan ta ce duk su zauna su karya iyayen su kuma a kwano ta zuba na kai musu suna ta cika da batsewa bakinciki kaman su mutu. Baban mu yazo fita kaman yanda ya saba yaga yara suna ta kai loman taliya baji ba gani wasun su kuma suna kokawa akan kifin da yake ciki. "Kai uban wa ya baku abinci da sassafen nan kuke mana hayaniya a gida" Baba ya tambaya yana kara matsowa kusa dan tabbatar da abinda idon shi ya gani gaskiya ne ko akasinta . "Innar Zareefa ce ta bamu" cewar Ibrahim d'an gidan Inna Asabe. "Jiya ma shinkafa da miya ta zuba mana harda nama" shima musa d'an gidan Gwaggo Aisha ya kara akai. Cike da mamaki Baban mu ya ce," ita Bintun ce tayi girki harda nama?" Yana magana ne yana kallon k'ofar d'akin mu. Fasa fitan yayi ya koma d'akin shi yana tunanin ta ina zai fara rarrashin Inna ta zuba mishi wannan kayan dad'in shima. [8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* Yin Kabbara tare Da Kowace Tsakuwa Yayin Jifan Jamra. Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana yin kabbara tare da kowace tgsakuwa idan ya jefi jamrori uku. Sannan sai ya yi gaba kadan ya yi addu'a yana mai fuskantar alkibla, ya daga hannayensa biyu yayin addu'ar. Yana yin haka ne bayan jifan Jamra ta farko da ta biyu. Amma bayan jamratul Akaba (jamra ta karshe), sai ya yi jifan kawai, ya yi kabbara tare da kowace tsakuwa, sannan ya tafi; ba ya tsayawa ya yi addu'a a wajenta. *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._ *5* Baba ya kasa zama yayi a d'aki sai safa da marwa yake,sai yayi kaman zai kira wani kuma sai ya fasa can dai yaja wani dogon tsaki shi kad'ai yana," in banda b'atawa kaina lokaci nake ba ita Bintun yaushe har tayi wani abin kanta zan tsinka kaina gaban yarinya k'arama" yana magana ne shi kad'ai tare da neman hanyan fita. Ta gefen ido yake kallon yaran da suke ta buduri da taliyarsu bakin nan duk mai yasa kai ya fice. Yana fita teburin mai shayi ya tafi kaman yanda ya saba ya bayar da naira d'ari yace a bashi shayi empty na naira ashirin da bredi na hamsin,ana bashi canji akwai mai kosai a gefen mai shayin itama ya sayi na talatin a wajan ta ya samu waje a rumfar mai shayin ya fara karyawa. A da in yana cin wannan had'in ji yake kaman mai cin kaza amma yau sai yaji babu taste sam sai tuno taliyan nan daya sha mai da kifin gongoni yake,kaman dole haka ya rinka cuccusawa har ya gama ya tashi ba dan dad'i ba. A gida kuwa muna gama karyawa da Inna ta tace mu shirya ta kaini makaranta kada wani abu yazo ya fad'awa kud'in, Muna gama shiryawa muka kama hanyan ainihin makarantan mu na da wato *YERWA PRACTICE* akwai jss a ciki daga 1 zuwa 3, cikin ikon Allah komai yazo mana da sauki ba kaman yanda Inna ta zata ba domin kud'in registration da kud'in PTA duka dubu biyu suka karb'a,daga nan uniform,takalmi,jaka,takardu duk kyauta aka bani kuma principal yace gobe in fara zuwa domin har an fara karatu. Cike da farinciki muka kama hanyan gida, a hanya sai da mukayi 'yan cefanen mu da kud'in hannun mu sai dubu uku ya rage muka dawo da kaya niki-niki a hannu. Gwaggo Aisha tana yiwa Hajara fad'a a tsakar gida kasancewar Inna Asabe ma ta fita,tana ganin mu tayi shiru sai rarraba ido take alaman basu da gaskiya,mu dai bamu bi ta kan su ba muka wuce d'aki suka bi ledojin hannun mu da kallo. Muryan Gwaggo Aisha ya cika gidan tana yiwa Hajara masifan me take bata fito ta tafi tallah ba gashi har azahar tayi,na fito da buta a hannu na dan zagawa makewayi muka had'a ido da Gwaggo Aisha ta gallah min wata muguwar harara,niko dan in cusa mata bakinciki sai nayi mata dariya dama in ina son kullar da ita haka nake yi. Ai kuwa ta hau yanda ya kamata ta hau zagina harda Inna ta da bata san wainar da ake toyawa ba,ni kuwa ko a jikina na shige bayan gidan na kama ruwa na fito tsakar gidan na fara alwala ita kuma bata fasa zagin nawa ba,dana lura bata da niyyan dainawa nayi mata gwalo amma sai na fake da cewa Jameela da take kusa da ita tayi min nima na rama. Ban gama wanke d'ayan kafa na ba naga ta rarumo murfin tukunya da yake kusa da ita ta jefi ni dashi, Allah ya taimake ni kamin ya karaso na gauce nayi d'akin mu da gudu ina dariya. Had'iye dariyan nawa nayi ganin fuskar Inna ta babu alaman wasa ta ce," wai ke wace irin yarinya ce Zareefa,ban hana ki kula su ba ko akwai sa'ar ki a ciki,bayan haka duk matan Baban kine saboda babu abokin wasan ki a cikin su tsakanin ki dasu shine girmamawa". Jiki a sanyaye na ce ," kiyi hakuri Inna ba zan sake ba dama ni bada ita nake ba nida Jameela ne" "Naji ki kiyaye bana son neman magana" ban kara cewa komai ba na fara sallah na a zuciya ta kuwa banga zan kyale ta ba in ta min wannan shegen kallon tunda ba wani laifi nayi mata ba. Da yamma Inna ta fito tayi tuwan ta na shinkafa da miyan yakuwa da yaji biscuit bone da wadacaccen gyad'an miya, jin yauma kamshi ya cika gidan yara suka fara tsallen murna suna," yauma Innar Zareefa zatayi mana kayan dad'i" iyayen su na hantaran su amma basu fasa ba. Yauma d'aki nabi su da abincin ba wanda ya kalle ni balle inji sun ce basa cin abincin da aka same ta ta haramtaccen hanya. Da wuri yau Baban mu ya dawo gida tare da tsammanin an girka kayan dad'i

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99