Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

da yunwa na shigo kin ganni nan har wani juwa nake gani, Allah yasa da akwai abinci d'akin nan" yace yana faman tsid'e yatsu. Girgiza kai Inna tayi sannan ta ce," babu abinci Mallam ba muyi girki ba sai...." "Inna ki bashi nawa da kika ajiye min yaci dan ni nasha ice cream ba zan ci ba". Na katsewa Inna hanzari. "Yauwa 'yar albarka, Allah sarki yarinya mai tausayin Baban ta" Abba yace cikin jin dad'i yana washe baki. Inna tsuke fuska tayi tana jin kaman ta kamo ni tayi ta kirb'a sai yau ya san dasu a gidan a baya in ta aika mishi abinci kora ta yake hmmmm sai yau, ba dan taso ba ta tashi ta d'auko mishi hadaddiyar warmer sabuwa da ta sayo mana muke zuba abincin mu a ciki ta ajiye a gaban shi. Cikin sauri Baba ya bud'e warmer, ba shiri ya lumshe ido saboda kamshi mai dad'i daya bugi hancin sa, yana bud'e ido sai da ya had'iye wani yawu ganin shinkafa da miyar kaza , ko ruwan wanke hannu bai nema ba ya tsoma hannu ya fara aikawa cikin sa hannu baka hannu kwarya. Ni kuwa duk dad'i ya cika ni yau muma Baban mu ya shigo d'akin mu kaman sauran 'yan gida har yaci abincin mu tsab'anin Inna da duk zaman shi a d'akin namu ya takura ta saboda bata saba ba kuma ta san ba wai matsayin ta da yake kiran ta dashi a baya ba son ta yake bane ya canza a'a sai dan kwad'ayin abin hannun ta wanda ita kuwa ba zata so ya shiga jikin ta b sam.. Yana cikin cin abincin naje inda Inna take ajiye min juices da bobo na d'auko mishi orange juice na ajiye a gaban shi. "Ikon Allah shi kuma menene wannan 'yar albarka?" Ya tambaya cikin matukar farinciki. "Lemon kwali ne Baba" na bashi amsa nima cikin jin dad'in sabon sunan da yake kira na dashi. Balle murfin yayi ya kafa kai ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusan shanyewa sannan ya ajiye yana tsid'e baki ya ce," wai..wai...wai.... Ikon Allah wai lemon kwali kika ce ko?" Ya kara tambaya bayan ya d'auko katon chicken breast a cikin abincin ya fara figa. Ina dariya na amsa mishi da " eh Baba" Inna dai ko kallon mu batayi ta cika tayi fam jira kawo take ya fita tayi magani na. Baba bai bar d'akin ba sai da ya gama cinye abincin harda lashe warmer sannan ya mike yana kallo na ya ce," 'yar albarka kada ki manta da Baban ki, ki rinka tunawa dani in kin samu kayan dad'i kinji ko?" Cikin jin dad'i na amsa mishi sannan yayiwa Inna sallama ya fita. Yana fita muka ji muryan Gwaggo Aisha tana shewa ta ce," ahaiyye nanaye yau me nake gani jama'a kuzo ku tayani duba ko dai ido na ne yake min gizo?" "Ba gizo idon ki yake miki ba nine nan Mallam Hassan kuma daga d'akin Bintu na fito ko kina da magana ne?" Baba ya b'ata amsa yana cire nama daya mak'ale mishi a hakori. A yanzu yana dai-dai daya b'ata da kowa a gidan in dai akan Bintu ne, haba yaushe rabon daya ci kaza ko shinkafa da miya ita in banda aukin shinkafa da wake me take bawa mutum ko naira d'ari ko d'ari biyu amma ga Bintu kwanaki bashin dubu biyu ta biya mishi a take,gaskiya dole ne ma ya mak'ale a wajan ta. Yana gama bata amsa yasa kai ya fice abinsa ya bar Gwaggo Aisha da ihu tana," aikin banza aikin wofi wato ta nan kika biyo dad'in abin kowa ya san dai sunan ki a gidan nan ba sonta nake ba, shine dai sunan ki". Inna tana jinta bata tanka ba saima kamo ni da tayi zata daka akan abinda nayi Allah ya taimake ni ya jefo Maman Dije ta kwace ni tare da nuna mata kada tayi haka saboda koma ya yake ba'a tab'a canzawa tuwo suna ba, duk abinda zasuyi suyi tsakanin su amma kada ta sakani a ciki. Da wannan nasihan Maman Dije na tsira ba'a jibge ni ba. Tun daga wannan rana Baba ya maida d'akin mu wajan hiran sa duk da yanda Inna take tsuke fuska baya damun sa in dai zai shigo ya samu abin tab'awa, ni kuwa duk dad'i ya cika ni yanzu Baba na shigo mana kuma ya daina hantara ta saima sabon suna daya lika min wai 'yar albarka. Inna kuwa duk rawan kafar da yake yi akan mu ba wani burge ta yake ba domin ta san dan abinda yake samu shiyasa har yake ihu da 'yar lelen shi wato Gwaggo Aisha, ta ina ma zata manta abubuwa da yayi mata na shekara da shekaru dad'in bakin sa na lokaci kad'an d'in nan ba zai tab'a goge tabo dake cikin zuciyar ta ba. Abin takaici ma har yau bai tab'a yunkurin tambayan ina Inna ta ya take samun kud'i da har take wayan nan abubuwan ba, kuma wani ikon Allah bai tab'a had'uwa da Abdulbasit ba dan haka bai san daga inda muke samun kud'i ba. Tsakani na da Abdulbasit kuwa wani shakuwa ne na ban mamaki ya shiga tsakanin mu ada yana kaiwa sati ko fiye kamin yazo gidan mu amma yanzu baya iyawa dan ana kwana 2 zai zo mu sha hiran mu yana sai dai mafi yawan hiran tsokana ta yake wai ya ganni da saurayi da sauran su ni kuwa insha kuka na in more daga baya kuma mu shirya abin mu ya tafi. Rayuwa yanzu tayi mana dad'i sosai dan bamu da maraba da masu kud'i tunda duk abinda masu kud'in suke ci suke sha suke sakawa muma haka ni da Inna ta duk mun murmure harda d'an kumatu mukayi. Gwaggo Aisha da Inna Asabe kuwa duk hankalin su a tashe yake ba ma kaman Gwaggo Aisha dan kiri-kiri ta rasa matsayin ta ya koma kan Inna tayi duk abubuwa da zatayi amma duk a banza dan gwara da yana d'an sauraron ta amma tunda ya shigo d'akin mu ranan ya tarar da Inna tana kirga kud'i sun kai kusan dubu hamsin a hannun ta tun daga wannan rana ya kara haukacewa kasancewar ko shi da yake d'a namiji bai tab'a rike irin wannan kud'i ba. Ganin duk ya rikice yasa Inna ta bashi dubu biyar a ciki a ranan kaman yayi mata sujada haka ya kwantar da murya yana mata godiya. Daga wannan ranan mulkin gidan ya koma hannun Inna ta dan Baban mu ya zama kaman wani bawan ta duk abinda tace baya musu balle ya karyata ta cin mutuncin kowa yake a gidan saboda mu. . Mun koma makaranta mun shiga jss 2 cikin farincikin sabon uniform da Abdulbasit ya d'inka min dasu sabon jaka da sauran kayan amfani na makaranta, tsab dani na koma kowa ma sai sha'awa ta yake masu tsokana ta da kuma yanzu sune suke bi na wai suna sona da k'awance. Na biye musu nima duk abinda na kai makaranta na kayan kwalama ina basu ko in sun ce in saya musu wani abu bana kyashin saya musu amma fa ba wai na manta abinda suka min bane

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99