Chapter 65
Chapter 65
damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *41&42* Bakomai ne yake raina ba sai yanda zan rama zalunci da yayi min, domin na yarda da maganan Yesmin da take fada min na cewa yana matukar tsoron Abban shi saboda nima gauce yanzu ba jiyau ba, ya wani natsu sai abubuwan mutanen kirki yake alhali kuwa mugu ne na bugawa a jarida. Har muka karaso gida ko ci kan ki bai kara ce min ba nima na share shi na wuce d'aki na, kayan jiki na na fara ragewa sannan na shiga na watsa ruwa na fito nayi shirin bacci na kwanta amma sai na kasa samun baccin, tunanin wannan company da Abba ya bani shi ya fad'o min a rai toh ni ya zanyi da companyn nan? kawai bari in bari in an kwana 2 sai in fad'awa Inna inji me zata ce. Lumshe ido nayi da niyyan bacci haka kawai Yaya na ya fad'o min a rai, ko a wni hali yake ciki, ko meyasa ya guje ni?? Tunanin hakan da nayi yasa na fara hawaye sosai harda shasshek'a dan ji nayi abin ya dawo min sabo fil zuciya ta sai kuna yake, duk halin da nake ciki a yanzu shine sila da bai guje ni ba da wannan mugun ko kallo na ba zai samu daman yi ba balle har in shigo gidan shi. A wannan dare da kyar na samu bacci ya d'auke ni mai cike da mafarkai kala-kala. Ko dana farka da safiyan nan sai naji duk raina a cunkushe yake fuskata babu walwala sam, iya d'aki da parlor na kawai na share nayi kwaciya ta ko kitchen banida niyyan lekawa balle inyi batun girki. Zuwa kaman karfe 10 naji yunwa na neman hallaka ni dole yasa na fito main parlour na had'a tea mai kauri akan dining na d'auki mug d'ina da niyyan komawa d'aki naga mutum a zaune yana waya ko kallon inda yake banyi ba nayi wucewa ta na bar shi baki bud'e cike da mamakin abinda nayi yake bi na da kallo har na shige. "Toh wai me ya hau kan yarinyan nan yau? Zaman da nayi anan ya kusa 1 hr ina jiran inga ta girka wani abu in samu inyi breakfast in fita shine taki yin komai saima tea da ta had'a ta wuce ko gaishe ni batayi ba, ko dai ta gane bana iya cin abincin kowa yanzu sai nata?" Zafar kenan shi kad'ai yana sumbatun sa a cikin ran shi. Zuruf ya mike yana cewa naga kwana 2 yana d'an sake min shiyasa na fara kawo mishi raini bari ya shiga ya gyara min zama, yana maganan ne tare da nufan d'aki na. Hankali kwance nake sipping tea na naga mutum ya shigo min babu sallama sai wani had'a fuska yake wai shi ala dole zai tsoratani. "Ke tsaban kin raina mutane shine har zaki shigo ki fita ba zaki gaida mutane ba?" Ya fad'a cikin tsawa. Sai da na turo baki na dan kalle shi na watsar nace" ni dai banga mutane ba,mutum daya na gani a parlorn". Mamakin da yake fuskar shi kasa boyuwa yayi yana bina da wani irin kallo, had'iye abin shi yayi ya Kara wani tsare gida yace" ohk in ma mutum dayan kika gani ba zaki gaida shi ba kenan, nd what do you mean by ki shiga daki ki zauna shan tea sauran mutanen gidan ba zakiyi musu girki bane?" Sai da na kuma kurban tea na hankali kwance sannan na bashi amsa " I don't feel like cooking today" "What!! Ni kike fad'awa u don't feel like cooking, kin ga ina bin ki a hankali shiyasa ko jira ni ina zuwa zaki min bayanin yanda ya dace" yana fad'an haka ya fuce fuuu kaman zai tashi sama, tab'e baki nayi na raka shi da ido wai ni zai rainawa hankali wai mutanen gidan me zasu ci, yace min dai me zai ci?. No Abba da tun jiya nayi saving a wayata na kira na saka a handsfree na ajiye kusa da ni muna gaisawa Ina karasa shan shayi na daya rage ya shigo dakin a zafaffe da belt a hannun shi har zai bud'i baki yayi magana jin muryan Abban shi yasa yayi tsit yana zare ido, kallon up nd down na mishi ina murmushi Abba yace" da fatan kin tashi lafiya my daughter" Kara kwantar da murya nayi sannan na amsa mishi da" yau na tashi da jiri da amai da zazzab'i Abba ko tashi bana iya yi shine na nemi alfarman ba zan iya shiga kitchen ba yau amma yake ta min fad'a" "Mene! Yana ina, ki bashi wayar in yana kusa" Abba ya karasa a d'an zafaffe. Ina kif-kifta ido kaman da gaske nace " gashi nan Abba" tare da mika mishi wayan, sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya saka hannu ya karb'a yana min mugun kallo, ni kuwa ko a jikina saima murmushin mugunta dana bi shi da ita. "Assalamu alaikum Abba barka da safiya" yace cikin sanyin murya. " Wa'alaikum salam son me nake ji haka kada ka kasance cikin mazan da basa kyautatawa iyalin su mana kayi koyi da manzan Allah dan ya kasance mai kyautatawa iyalan sa,ko kaga haka muke da Momyn ka?" Bai iya bude ya bashi amsa sai girgiza kai da yayi kaman yana gaban Abban. "Kada in kuma jin irin haka try to be a good husband ok, nd get something for her tayi breakfast". Insha Allah Abba" ya amsa cikin sanyin murya sannan ya katse kiran. Ina jira inga ko zai hau kaina da wannan masifan nashi amma ga mamamki na sai ajiye min wayan yayi ba tare da yace komai ba ya fita daga dakin, murmushin nasara nayi tare da gyra kwanciya ta kan kujera na d'auko wayata na shiga watsApp. Bayan fitan shi kaman da minti 30 sai gashi ya kara shigowa da sallama da wasu shopping bags a hannun shi ya ajiye min harda na pharmacy a ciki da alamu magani ya sayo. "Ga breakfast dinki da drugs ki sha bayan kin gama nd pls next time in baki da lafiya let me know" yana gama magana ya fita, ni abin ma sai naji shi wani bambarakwai wai yau Zafar ne yake min magana a nitse babu tsawa harda wani pls? Hmmm tab na yarda da maganan Yasmin da tace yana bala'in tsoron Abban shi daga waya sau 1 har ya sauya. But sai nake jin kaman ban kyauta ba da na had'a shi da mahaifin shi har yayi mishi fad'a, wani bangare na zuciya ta na kara ingizani cewa sai me ai shima lokacin da yake takura ni bai tausaya min ba. Bud'e ledan eatary nayi naga manyan package na take away guda 2 na farko cike da chips da kwai sai na biyun kuma cike yake da pepped chicken sai kamshi suke ba b'ata lokaci na d'iba na fara ci ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99