Chapter 91
Chapter 91
yake dauke mishi hankali kullum, fuskar shi ya kawo dab da nawa ya hade goshin mu wuri daya yana goga min hancin sa akan hancina, da sauri ya dauke fuskar shi yayi baya kadan tare da rufe ido ganin nayi motsi ya zata farkawa zanyi. Murmushi ya sake yana dawo da fuska shi wajan shi na da ganin na cigaba da bacci na cikin kwanciyar hankali, brushing lips d'in shi yayi akan nawa tare da lumshe ido jin taushin labban nawa har kwanyan shi. Wani irin farinciki ya tsinci kanshi a ciki yana jim inama mu dauwama a haka, kasa hakura yayi saida ya kama lip dina na kasa ya dan tsostsa with his eyes closed.gyara min kwanciya yayi a jikinsa yasa hannayen shi duka 2 ya rungume ni tsam a jikinsa ya lumshe ido with the hope ko bacci zai iya daukan shi saboda yanda yake jin d'umin jikina da Kuma yanda yake jin kirjina ya hadu da nashi duk sai yaji ya shiga da nasani. Haka yayi ta fama da kyar ya samu bacci ya dauke shi wuraren asuba. da washe gari a makare muka tashi ni dad'in bacci ya hana ni farkawa da wuri yayin da shi kuma rashin baccin da wuri yasa ya makara. 6:20am shi ya fara farkawa cike da farincikin we slept together,ya tsaya kallon innocent face dina da nake bacci na peacefully sai yaga kaman nafi kyau a haka. Light kiss ya manna min a goshi yana murmushi sannan ya had'a fuska ya fara magana kaman gaske" ke Zareefa!! Ya haka? Daga taimako ga yanda kika wani kanainaye ni kika haye min jiki, amma da nine nayi miki haka sai kice da wata manufa nayi miki ko?" Shiru nayi naki in motsa balle in bashi amsa duk kunya ya lullube ni dan gaba daya a jikin sa nake kwance, dariya kawai yayi ya cire ni a jikinsa yayi hanyan fita yana " in kin gama likimon sai ki tashi kiyi sallah, kin sa mun makara har na rasa sallah jam'i " ina jin shi amma ban tanka ba har sai da na tabbatar da ya fita sannan na mike na shiga bathroom domin yin alwala. ************************ Gidan mu yanzu ya zama kaman bashi ba ko ina shiru hatta da yaran gida sun canza kasancewar canjin da baba yazo dashi gidan, kullum da safe ya kan tara su Inna a parlour shi ya nemi gafaran su akan yanda suka zauna ada na yanda bai damu da sauke nauyin da Allah ya daura mishi ba sannan ya kanyi alkawarin canji a zamanta kewar su Kuma yana bukatan hadin kan su domin babu abinda zai tafi daidai sai sun bashi hadin kai . Inna ta da Inna Assbe su kanyi mishi alkawarin bashi dukkan hadin kai da yake bukata yayin da ita kuma Gwaggo Aisha takan tabe baki ta dauke kai saboda ita wannan tsarin kwata kwata bai mata ba, tafi jin dad'in rayuwar gidan mu na da yanda kowa yake kara zube kayi duk abinda kake so babu mai hana ka musamman ita da take taka duk wanda take son takawa a gidan ta kwana lafiya. Kananan yaran gida duk yasa an saka su a islamiya da boko cikin ikon Allah sun natsu tare da maida hankalin su ga karatu, maganan tallah Kuma babu shi dan ya dade da soke ta wanda hakan sam Bai yiwa Gwaggo Aisha dad'i ba. Da farko taso tada masifa a tsakar gida kaman yanda ta saba yi shekara da shekaru, sai dai nan da nan Baba ya taka mata biriki ta hanyan da bata tab'a tsammani ba. Kiran su yayi parlour shi ya zaunar dasu sannan ya fara magana; "Ina son ku bani hankalin ku gaba dayan ku kuma ku fahimce ni Dan daga rana irin ta yau bana son inga kun daurawa ko wani yaro tallah a gidan nan,ina son ku bani hadin kai su samu tarbiya da karatu da suka rasa a baya.a kullum sai naji kaman in zubda hawaye in na tuna yanda gidan yake a baya sannan bana gajiya da naiman yafiya ku akan...." "A'a dakata mallam akan me zaka ce ba zamu daurawa yara abin sana'a ba sai dai mu zauna kara zube babu sana'a, kana wai su je boko da isamiya ko menene?" Gwaggo Aisha ta katse shi a hasale tana kumbure kumbure cikin fushi shi kuwa ido ya zuba mata ganin hakan kuwa yasa ta cigaba da masifarta. "Ni dama na rasa gane kan ka tunda ka dawo daga barikin sojojin nan duk ka canza ka zama sabon mutum, da farko ina tantaman abinda zuciyata take raya min game da hakan amma yanzu na gaskata tabbas Mallam wajan dukan nan da sukayi maka sun daki kan ka har ya jawo maka tabin hankali. Toh wallahi ni dai ba zan dauka ba tun wuri ka canza shawaran na fad'a maka ehe" ta karasa cikin fushi. Baba kuwa murmushi kawai yayi ya a kada kai ya tabbata da ace a can baya ne ta fad'a mishi wannan kalmar ta tabin hankali, da ya nuna mata haukan amma a yanzu kam yafi karfin wannan. Cikin natsuwa da ta fara zama jikin shi yace" ba shawara nake baku ba Aisha wannan umarni ne a matsayina na uban yaran kuma miji a gare ku". "Hmmmm su miji manya ni dai na gaya maka wannan umarnin naka ka bawa saunayen matan naka amma banda ni domin babu abinda zai hana ni yin sana'a" Gwaggo Aisha ta mayar mishi da martani cikin gadara. Zaiyi magana Inna tayi saurin cewa" toh Masha Allah Mallam munji dad'in wannan hukuncin naka insha Allah zaka same mu masu cika umarnin kane a kowani lokaci, su kuma yaran Allah yayi musu jagora ya basu ilimi mai amfani". "Ameeen " ya amsa can kasan makoshi lumshe ido yayi cikin jin dad'in kalaman nata tare da jin takaicin kan shi ta yanda ya wulkanta mace mai daraja haka a baya. "Insha Allahu kuwa Mallam ba zamuyi wasa da wannan daman da muka dade muna nema ba, zamu tsaya tsayin daka har sai sun samu ilimi mai inganci" cewar Inna Asabe domin ita har ga Allah taji dadi sosai saboda ta dade tana sha'awan taga yaran ta suna karatu kaman kowa sai dai rashin wadata da kuma rashin samun kula daga wajan mahaifin su yasa ta hakura. "Kaji munafuka mara zuciya, ke dama tun ba yau na lura baki san ina yake miki ciwo ba.in banda shashanci harda wani cewa wai irin daman kin dade kina jira, toh kin samu amma ni kam babu uban da ya isa ya hana daurawa yayana abin sana'a".cewar Gwaggo Aisha tana watsawa Inna Asabe mugun kallo. "Babu uban da ya isa kika ce ko? Toh tsaya kiji yara dai nawa ne Kuma daga yau ba zasu kara yin wani abu mai kama da tallah ba sannan duk wacce ta daurawa d'ana tallah a bakin aurenta. Zaku iya tafiya" Baba ya karasa a d'an hasale tare da kwaciya abin shi ya juya musu baya. Inna ta da Inna Asabe godiya suka mishi suka fito suka bar Gwaggo Aisha da shock ya daskarar da ita saboda ta kasa yarda wannan kalmar daga bakin Baba ya fito, da kyar ta samu ta mike zuciyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99