Chapter 75
Chapter 75
ne har kike kumfan baki akan sa, tunda aka haife ki meya tab'a tsinanana miki a matsayin sa na uba a gare ki , ina ni din nan da kika raina nice nake fad'i tashi har kuka taso. Wannan aikin da nake dan waye nake yin shi dan ke da 'yan uwan kine ku samu rayuwa mai kyau koda bayan raina amma kike shirin watsa min kasa a ido, waye wata Bintu da za'a ce ita ce mai abu a gidan nan tazo tana d'aga mana hanci, hanyan da tabi ta hau muma shi zamu bi mu hau domin kowa ya san asiri sukayi har wannan d'an masu kud'in nan ya aure ta, in zaki farka daga wannan baccin naki ki farka ki kalli abinda duniya take ciki ba wai ki tsaya yin shirme ba" Goge hawayan da suka cika mata ido Hajara tayi ta juyo tana kallon ta da kyau tace " Umma duk halin da baba na ya shiga dole ya dame ni tunda mahaifi na ne shi kuma a kowani hali yake ina son shi dan shine yayi sillan zuwana duniya kuma ina matukar alfahari dashi, sannan maganan Inna da kike cewa asiri tayiwa mijin Zareefa kema kin fad'a ne kawai amma kin san da asiri yana tasiri da kin dad'e da zama millionaire saboda haka babu inda zan je har sai naga mahaifi na ya dawo LAFIYA". Tana karasa maganar ta ta fice a dakin zuwa wajan su Inna ta kama musu suka cigaba da aikin tare. Tagumi Gwaggo Aisha ta zuba tana kallon Hajara har ta gama ficewa daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tace " Ina murnan asirin ya sake ta ashe da sauran aiki a gaba na dole in kara d'aura d'amara yaki da wannan algungumar". Hajara bata san ma tana yi ba suna can suna aikin su da sauran mutanen gida, jalof rice sukayi lafiyayye Inna ta saka yaran gida kiran almajirai suzo su karb'i sadakan abincin nan da nan kuwa suka cika gidan har da ma wayan da ba almajirai ba aka rarraba musu abincin suna karb'a bakin su d'auke da addu'a. Su Baban Dije sai yamma likis suka dawo a gajiye ba tare da wata nasara ba , giwa Barack da 3-3 Barack suka je suka sha wahalan banza dan ko bakin gate ba'a bar su sun wuce ba sun dai wuni suna zagaye bakin gate d'in daga baya ma da kyar suka kwaci kan su a wajan sojojin bakin gate dan cewa sukayi basu yarda dasu ba. Jikin kowa kara sanyi yayi jin babu wani labari gashi duk cikin zuri'ar mu babu wani mai kud'i balle mai mulki da zai tsaya mana wajan neman inda yake balle ayi maganan fito dashi. "Gaskiya talauci baiyi ba, Inna ko za'a fad'awa Zareefa ne ko mijin ta zai iya taimaka mana a fito da Baba" cewar Hajara kenan tana share hawayen fuskarta. "Kul kada inji wani yayi wannan gurguwan tunanin a cikin ku yaushe akayi mata auren da har irin maganan nan zai je kunnen mijinta, insha Allah zamu samu inda yake kuci gaba da addu'a, musamman ke Bintu kinyi tunani mai kyau da kikayi abinci kika sadakar hakan nada kyau sosai domin sadaka tana maganin musifa" Baban Dije ya karasa fada tare da wucewa bangaren shi. Kowa haka ya watse cike da jimami tare da karfafa zukatan juna kan cewa za'a gan shin a cigaba da addu'a, har a wannan lokaci Gwaggo Aisha bata fito ba tana ciki tana jin mutane Hajara da ta shiga bata ma kalli inda take ba tayi wucewar ta uwar d'akar su itama Gwaggo Aishan bata ce mata ci kan ki ba dan a cewar ta sai ta tashi tsaye har yanzu asirin da Inna tayi mata bai gama sakin ta ba. ******************* Zafar ya dad'e a dakina zaune a bakin gado yana dafe da kan shi da hannuwa duka 2 ji kaman yayi ta ihu ko zaiji saukin abinda yake damun shi dan ji yake zuciyar shi kaman zata fashe saboda azabar son kasancewa dani, ko da ba zai tab'a ni ba mu zauna waje d'aya yayi ta kallo na ma ya wadatar dashi. "Ya Allah na roke ka yaye min wannan fitinan ko zan ji sauki a rayuwata" yace yana kara kallon kofan bathroom d'in, shi kan shi bai san adadin lokaci daya bata a zaune ba ya hakura ya fita ganin bani da niyyan fitowa. Duk abinda yake ina kallon shi ta b'ulin mukulli sai dai banji abinda yake cewa kuma ko kad'an ba banji wani abu na tausayin shi a cikin rai na ba dan nasan ba abinda namiji ba zaiyi ba saboda cikar burin shi. Ina ganin ya fita daga d'akin nima na fito na murza key a kofa ta na jingina a jikin kofan Ina sauke numfashi tare da lumshe ido sauran hawaye da suka mak'ale min suka samu nasaran zubowa, Allah ya sani soyayyar shi na wahal dani amma dole in kare kaina ba zan bari yayi nasara ba. Shiryawa nayi cikin riga da skirt na wani material light blue ya min kyau sosai banyi wani kwalliya ba illah kwalli dana zira sai powder da wet lips, ina son fita amma ina gudun kada mu kara had'uwa da shi yasa nayi zama na a cikin d'akin ina chart dasu Maryam ina ce mata nayi fushi tunda taki zuwa inda nake tana bani hakuri wai zata zo kwanan nan. Kiran sallah azahar ne ya tada ni daga kwancen da nake na shiga bathroom na d'auro alwala nazo na kabbara sallah, cikin natsuwa na idar na zauna nayi addu'oi na dan haka kawai nake ta jin gabana yana yawan fad'uwa. Ganin zaman ba zai yiwu ba yasa na fito ina leka parlorn kaman wata barauniya cikin sa'a kuwa naga baya nan cikin sauri na shiga kitchen abubuwa dana girka dazu na had'a na mikawa Baba mai gadi bayan na zurmuka dogon hijabi na har kasa sannan na fita na bashi na dawo ciki. Sabon girki na d'aura ba dan Ina jin yunwa ba sai dan farantawa Zafar har cikin raina ina jin dad'in yanda yake son abinci na. Lafiyayyen white macroni da coslow nayi wanda ya wadatu da veggies sai kamshi yake, sabon warmer da ban tab'a amfani dashi ba na d'auko na zuba rabon shi na kara mishi da carrot juice na jajajjefa ice block a ciki na rufe tare da jera su akan maidaicin tray sannan na fito dashi kan dinning na shirya su a lokacin har an fara kiran sallah la'asar da alamu kuma har yanzu bai shigo gidan ba. Komawa nayi ciki nayi alwala nayi sallah , sai a lokacin naji cikina yana kukan yunwa dan tun safe babu wani abin kirki daya shiga ciki na, fita nayi na zubo abincin a plate na dawo parlour na kunna kallo na fara ci ko rabi ban ci ba naji sallaman shi da wannan sabuwar muryan shi mai sanyi ba kaman da ba da sai yaga dama yake sallaman ko zai min magana cikin tsawa yake min. Sanin muhimmancin sallaman a musulunci yasa na ansa ba tare da na kalle shi ba duk da zuciya ta tana kwad'ayin hakan amma na fuske naci gaba da cin abinci na.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99