Chapter 78
Chapter 78
ya yace yana huci. "kuyi hakuri ranka ya dad'e wallahi ban san dani kuke ba " ya amsa daga kwancen sai jujjuya kai yake na azaba da yake jin tana ratsa har kwakwalwan shi. Wani irin shure shi yaji an kara yi da kafa har sai da ya mirgina gefe cikin wani irin babban murya yaji ance " kana kwance kake bawa oga amsa, sit properly my friend" yaji an kara daka mishi tsawa. Duk da ba jin turancin yake ba amma sarai ya gane me yake nufi dan haka cikin dauriya ya yunkura ya tashi zaune yana b'ata fuska alaman har yanzu yana jin zafi, a hankali kaman mai tsoro ya kalli gefen shi mutum ya gani fuska a kumbure da kayar ma ake iya kallon kwayar idon shi. Duk wannan kallon cikin second 5 yayi su ya sauke kan shi kasa ba tare da yace wani abu ba. "Ka san shi ?" Yaji babban cikin su ya tamabya, Baba bakin shi har rawa yake wajan bashi amsa dan har yanzu yana jin zugin da bayan ke mishi " ban san shi ba ranka ya dad'e" " No enough don't hit him " babban nasu ya dakatar da wanda ya dago bindigar shi domin kara kwad'a mishi . "Ka gaya mana gaskiya bana son kana b'ata mana lokaci ka gan mu nan muna da abinda zamuyi muka tsaya anan muna binka a hankali ko in kana so in barka dasu su tambaye ka toh....." " A'a wallahi Allah ranka ya dad'e ban san shi ba hasalima ban tab'a ganin shi ba. Baba ya amsa har yana katse shi jin cewar za'a bar shi da masu zallan muguntan nan. "Nd you gaya mana gaskiya kace shine shugaban nan naku amma yace bai sanka ba " ya tambaya tare da maida hankali shi kan d'ayan mutumin da aka kawo shi yanzu, cikin dashassiyar muryan shi da bata fita sosai na alaman yaci wuya a hannun su ba na wasa ba yace " shine shigaban mu Mallam Hassan" A zabure Baba ya d'ago da kan shi ya zubawa mutumin nan ido da yace shine shigwaban su kuma sai yake jin kaman ya tab'a sanin mai muryan, murmushi mai kama da kuka ya sakewa Baba da kumburarren fuskan shi ganin yanda ya zuba mishi ido yace; "Baka gane ni ba ko Mallam Hassan? nine Abdulbasit yaron ka mafi kusanci da kai cikin yaranka wanda har kayi alkawarin bani Yar ka Zareefa da aure ka tuna, kana mamakin ya akayi suka kama ni bayan tarin makamai da ka bamu toh sun kama ni ne a hanyan mu na kaduna da ka saka mu muyi kidnapping minister man fetur ashe ba securities d'in shi da muka saya bane suka rako shi wasu sabi ne daban Kuma suma dan rashin amana basu gaya mana ba sai clashin mukayi dasu, munyi yunkurin guduwa sauran Allah ya basu sa'a sun gudu sai nine kad'ai suka kama sanadiyan harbi da suka min a kafan dama " ya karasa yana nuna mishi kafan shi na dama da yake a kumbure ya sha daurin bandage. "Kayi hakuri wahala yasa na fad'a musu sunan ka da inda za'a same ka , yanzu ma tambaya suke menene Shirin mu na gaba shine nace baka fad'a mana har sai zamu fita aiki kake fad'a mana abinda zamuyi" yana gama magana ya sunkuyar da kai kasa alamun he is sorry for what happened. Baki bud'e kawai Baba ke kallon shi ya kasa gaskata abinda yake faruwa kaman a mafarki ko Shirin film, tsoro, mamaki, firgici yasa ya kasa furta komai sai kallon wanda ya kira kan shi da Abdulbasit yake dan haka ko kad'an bai ji abinda babban sojojin yace ba sai gani yayi an had'a su waje d'aya an ingiza su zuwa wani babban d'aki sai dai wannan karan ba cikin duhu bane an bar su da haske , suna fita suka kulle su ta waje aka bar su su kad'ai. ******************** Ina farkawa da safe bayan na idar da sallah ban iya tsayawa nayi azkar d'ina da kyau saboda wani irin bacci da ya cika min ido har wani yaji-yaji yake min, nan na bingire kan sallayan ko hijabi na ban cire ba bacci mai dad'i yayi awon gaba dani. A bangaren Zafar kuwa ko da safen ma kasa komawa baccin yayi zuciyar shi har yanzu zafi take mishi akan abinda ya faru tsakanin mu, sosai abin yake mishi zafi kuma yana jin dole ne ya koya min hankali but tayaya? Shine abinda yafi damun shi ya rasa ta yanda zaiyi ya hukunta ni. Dik wani hanya da yake ganin ya cancanta yabi ya hukunta ni sai ya ga ba zai iya ba saboda zan cutu ta hakan sannan deep down him kuma baya son ma ya d'auki matakin saima hanyan da zai bi ya rarrashe ni yake nema dan shi kad'ai yasan abinda yake ji game dani. Sai kusan karfe goma na farka ina mamakin irin baccin da nayi ban b'ata lokaci ba na cire hijabin jikina na nad'e sallayan na ajiye su a mazaunin su na gyara daki da parlour na tsab sannan na shiga nayi wanka da brush na fito da yake na san na sakawa kofa ta key shiyasa cikin kwanciyar hankali na shirya cikin riga da skirt na less light blue daya ji aikin stone sai walkiya suke. D'an kwalliya nayi tare da d'aura d'an kwlin na fesa turare sannan na nufo kofa zuciya ta na bugawa ban san had'uwa ta dashi ya zata kasance ba yau, parlour na na fito na bud'e kofan main parlour ina leke ganin babu kowa yasa na fito abina kai tsaye nayi kitchen Dan yunwa na fara ji sosai. Turus nayi a bakin kitchen d'in ganin Zafar a gaban coffee machine yana hadawa, jin motsina yasa ya juyo muna had'a ido na tsuke fuska ina shirin d'auke nawa idon ga mamaki na wani sasssayan murmushi ya jefo min wanda kana gani daga kasan zuciyar shi take. Saura kiris in zubda ajina da nake kokarin karewa agaban shi domin a take naji notinan kai na sun kunce saboda ban tab'a ganin yayi irin wannan murmushin ba tunda na san shi shiyasa a take naji gaba daya jikina yayi lakwas. Daurewa nayi na wuce shi zuwa wajan fridge na ciro kwai 3 da niyan soyawa sai ji nayi yana " ba sai kin sha wahalan soyawa ba, I have already made breakfast for you" yace yana nuna min wani hadadden tray mai d'auke da wani plate a rufe, d'auke kaina nayi na cigaba da fito da kayayyakin da nake bukata wajan girkin da nayi niyya. Wuka na d'auko zan yanka albasa naji karaf ya rike min hannu wani mugun kallo na watsa mishi ina mishi kallon meye haka, shi kuwa marairaice fuska yayi harda wani langwab'e kai irin pls din nan. Kwace hannu na nayi ba tare da nace mishi kala ba nayi hanyan parlour, saida yayi murmushi sannan ya biyo ni da tryn akan kujera ya same ni zaune na dafe goshi na da hannun dama dan na rasa abinyi ajiyewa yayi a gaba na ya koma kitchen din ya fito da mugs guda 2 da ya had'a coffee a ciki ya ajiye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99