Skip to content

Chapter 79

Chapter 79

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,282 words 0 views Progress saved
Download Book

suma a gaba na sannan ya durkusa Yana leka fuskata. "I'm very sorry for what happened yesterday dan Allah kiyi hakuri na miki alkawari hakan ba zai kara faruwa ba ki bar komai ya wuce let's be friends for the rest of the time we will spend 2geda" yace cikin sanyin murya. Ban iya d'agowa ba nayi shiru ina sauraron shi dan na rasa a wani mizani zan auna maganganun nashi, dan sun dan sanyayya min jiki kamin in samu abin cewa waya ta da na bari a kitchen ya d'auki kara, kamin in mike har shi ya rigani mikewa kitchen din naga ya koma sai gashi ya dawo da waya ta a hannu ba tare da yayi magana ba ya miko min.. Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama maganar shi a zuciya ta na cewa ba girki da d'auko waya zai rinka yi ba ko menene zaiyi ba zai tab'a cin nasara a kaina ba tunda na riga da na gane manufarsa a kaina. Hannu na saka na karb'a daidai wayar ya katse duba sunan nayi naga Dije ce babu bata lokaci na kira ta kaman kuwa jira take bugu daya kawai ta d'aga cikin ihu tace " kaji matan mayan Alhazawa basa d'aukan kira sai dai su kira mutum". Murmushi kawai nayi dan yanda yake zaune kusa dani yana jin abinda muke cewa ba zan iya sakewa inyi magana yanda raina take so ba nace " Dije ba kya rabo da zolaya ya kike?" " Lafiya lau Zareefa ya muka ji da wannan iftila'in daya fad'awa Baba ku?" Ta amsa min cikin sanyi. " Wani iftila'i kuma Dije?" Nima na tambaye ta cikin rashin fahimta. "Ke kuma akwai ki da wani zance, wani iftila'i kuwa banda wanda sojoji suka tafi da Baban ku" " Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!!! Kawai nake iya maimaitawa cikin mugun tashin hankali da ban tab'a tsintan kaina a ciki ba, Baban mu a hannun sojoji toh meya faru meyasa babu wanda ya gaya min a gida. Kuka na fashe da Ina" Baban mu sojoji suka kama Dije tun yaushe , meyasa babu wanda ya fad'a min" Cikin rashin jin dad'in kotobarar da tayi dan ita duk a zaton ta na sani shiyasa ta kira ta min jaje dan duk zuwanta gidan mu bata gani na ashe ban ma ji ba, maimakon ta bani amsa kawai sai ta katse kiran. Cikin tashin hankali na kara Kiran ta amma sai naji wai switch off, jefer da wayan nayi ina kara fashewa da kuka na kama jeka ka dawo a tsakar parlour na rasa ina zan saka raina inji sanyi. Kafadata naji ya riko ta baya tare da juyo dani muna fuskantan juna ya saka hannu ya share min hawayen da suke ambaliya a fuska na wasu na zubowa yace" shhhh ya isa haka kada ki sakawa kan ki ciwon kai, naji duk abinda aka fad'a miki a waya kada ki tashi hankalin ki kina da ni duk inda sojojin suka kai Baba nayi Miki alkawarin ni zan tsaya har sai naga ya fito". Kallon shi kawai nake kaman yau na fara ganin shi murna zanyi akan abinda ya fad'a ko akasin ta, duk bayan maganganun da ya fad'a min jiya why zai cigaba da nuna min kulawa haka? "Komai maza zasu iya yi dan cimma burin su " zuciya na ta kwab'e ni kamin in samu amsan bashi ya katse da " shhhhh kada kice komai kije ki d'auko hijabin ki mu tafi gidan ku muji ya maganan take"... Ban San lokacin da murmushi ya subuce min na farincikin zanje gidan mu cikin matukar jin dad'i nace " thank you Ya Zafar....." Nagode da soyayyar ku gare da wannan novel Allah ya bar kauna, nima ina muku fatan alkhairi my fans. [12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *43&44* Shiru motan ya d'auka babu mai magana a cikin mu sai dai yana tuki amma duk hankalin shi a kaina yake, ni kuma na maida kaina gefe ina kallon titi lokaci-lokaci na kan share hawaye da suke zubo min na kasa dannewa sai tunanin halin da Baban mu yake ciki nake, toh meya aikata haka da har sojoji suka tafi dashi... Sojoji bama police ba, Baba da ko police ya gani duk sai ya gigice balle ace yana barracks na sojoji ya Allah ya fitar da shi cikin sauki, duk a zuciyata nake ta wasi-wasin nan har muka iso kofar gidan mu cikin azama na fara kokarin bud'e kofan in fita naji ashe ya saka lock. Juyowa nayi na watsa mishi wani kallo da yake nufin menene haka? Bai nuna fushi ko b'acin rai ba yace " calm down pls ki bi komai a sannu insha Allah ba abinda zai samu Baban mu I promised u this, in kin shiga ciki pls ki min iso wajan kanin Baban inji ta ina zan fara" yana karasa maganan shi yayi unlocking d'in kofan jiki a mace na bud'e na fita. Ina fitowa Kuma sai naji kaman in d'iba da gudu in shiga ciki nake ji amma na daure banyi gudun ma sai uban sauri da nayi ta zubawa na tura gate din na shiga daga can na hango Inna ta da Inna Asabe suna ta kiciniya da murhun itace a tsakar gida zasu daura abincin sadaka, ai ban san lokacin da na kwasa da gudu na isa gare su sai kawai Inna ji tayi an fad'o mata akai . A zabure ta juyo muka had'a ido sai washe baki nake dan farincikin da nake ciki bai zai tab'a misaltuwa ba, itama cikin farincikin ta rungume ni fuskarta d'auke da zallan murnan gani na cikin koshin lafiya ga wani dan haske da na kara kana gani kasan ina cikin hutu. "Zareefa kece haka sulum bako waya?" Inna Asabe tace tana kallon mu cikin farinciki itama, sai a sannan na

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99