Chapter 70
Chapter 70
abinda take fad'a wai Baban mu ne mayen kud'i, toh ita fa in banda ance laifi tudu ne yanzu bata ganin laifin munanan ayyuka da take sai na Baban mu wanda ta tabbata da wata akasa dan bai aikata abinda mutane suke cewa ba. "Ke ina tambayan ki kin min shiru, nace dai yauma aikin ya tafi yanda ya kamata ko?" Ta katse ta cikin tsawa. Gyad'a mata kai kwai tayi dan wani malolon bakinciki ne yazo ya tokare mata wuya, washe hakora tayi cike da farin ciki tana ," Alhamdulillah hankali na ya kwanta amma ya ban ganki da kaya irin na jiya ba, saboda na saka rai zaki kawo mana kayan dad'i ko girki ban daura ba na zauna jiran ki". Daki kawai ta nufa ta san in ta tsaya takaici ne zai kashe ta, saida ta kusan shiga daki sannan tace mata " mahaifiyar shi ta kira shi ya tafi" "Uwar shi? Dan uwar shi ta kira sai ya tafi ya bar ki, lalle muna da sauran aiki a gaban mu dole ne mu raba shi da ita in ba haka ba zata kawo mana barazana cikin aikin mu".ta fad'a a masifance ita dai Hajara bata kara kula ta ba ta ida shigewa ta bar ta da kumfan baki. *************************** Tunda Hajara ta tafi ban kara jin motsin sa ba ina ciki duk haushi ya ishe ni sai kunci nake ni kad'ai, koda naga zaman kuncin ba zai fishe ni ba fitowa nayi na kama dan aikace-aikace na ko zan ragewa kaina damuwa, cikin ikon Allah ko Ina farawa na mance da abinda ya faru. Kitchen na shiga na had'a kayan da b'ata ina wankewa naji a jiki na alamun ana kallo na da sauri na waiwaya na gan shi tsaye yana karewa baya na kallo, yana ganin na juyo ya basar yayi kaman yanzu ne zuwan shi, karasa shigowa yayi cikin kitchen din ya bud'e fridge ya d'auko malt mai sanyi ya koma bakin kitchen din ya bud'e ya fara sha. Ban kara juyowa ba amma ji nake kaman na juya nayi ta kallon shi dan ba karamin kyau yayi min ba, kama gulman shi nayi a cikin zuciya ta ina mutum kaman wani aljani ko wani Kaya ya saka sai yayi mishi kyau dubi dai singlet ne da 3 quater a jikin shi amma sai ya zama kaman wani dressing yayi na gani na fad'a ga kamshin sa kuwa duk inda zai je kamin ya isa kamshin ya riga shi isowa haka kuma ko ya tafi zai dad'e a wajan. Ta kasan ido na kara kallon shi yana tsaye a inda yake bai motsa ba gashi ni kuma na gama wanke-wanken ina son fita amma na rasa yanda zanyi saboda duk ya tare hanya yayi bake-bake babu wajan wucewa ni kuwa bana son yi mishi magana dan har yanzu haushin shi nake ji. Wasu ayyukan na shiga kirkira wai ko zai gaji ya bar hanyan amma saima gani nayi ya gyra tsayuwar shi ya jingina da kitchen cabinet din ya cigaba da kurb'an malt din yana kara tsare ni da ido, gajiya nayi da kirkire kirkiren nayi shahada na nufo kofan wai ko in yaga nayi niyyan fitan zai bani hanya amma ga mamakina ko motsawa baiyi ba balle ya matsa. "Zan wuce" nace ba tare da na kalle shi ba. "waya hana ki wucewa?" Yace shima yana wani d'aure fuska " naga ka tare hanya ne"... Dan matsawa yayi gefe ya bar wani karamin hanya,ta gefen ido na kalle shi naga har yanzu yana rike da malt din a rai na ina mamakin wani irin kurb'a ce yake mata tun dazu ace bai kare ba, sauke ido na nayi cikin sauri nazo zan wuce amma sai yasa hannun shi na dama ya tare hanya. Dawowa nayi da baya zan koma kitchen d'in nan ma ya jefar da empty tin na malt din ya kara tare min hanya ya zamto ina tsakiya hannayen shi ya zuba min wayan idon shi mai rikitar dani, cikin azama nayi kasa da nawa idon dan ba zan iya jure kallon nashi ba. "Da kike wani neman guduwa cinye ki zanyi?" Ya tambaya cikin wani irin murya da ban san yana da ita ba, ban iya bashi amsa ba na kara yin kasa da kaina, ina jin yanda zuciya ta take zillo kaman zata fito saboda kusancin namu yayi yawa. "Hmmm na gane duka gulma ne u just want me to repeat what we did in d morning" yace yana bina da wani irin killer smile. Cikin zaro ido na d'ago kai na da niyyan yi mishi masifan sharri daya lak'a min amma mukut na had'iye kaya na saima zaro ido da nashiga yi sakamon tattausan bakin shi da naji akan nawa. Kiciniyar kwace kaina nake amma bai bani daman hakan ba, sai kara manne min yake tun inada karfin kokuwa har karfi na ya kare wani irin kasala na sauko min tare da hawaye kaman an bud'e famfo. Jin hannuwan shi sun fara min yawo a jiki yasa na tattara sauran courage daya rage min na ture shi ya kuwa tafi da baya har yana bigewa da cabinet din bayan shi ni dai ban juyo ba balle in san halin da yake ciki na fad'a daki tare da rufo kofa na jingina ina maida numfashi. "Ouch " yace yana rike bayan shi inda ya bugun ya shafawa yana murmushi tare da jin kaman ya bini ,shi dai wannan sabon jaraba daya same shi a kaina bai tab'a shiga irin wannan yanayin ba dan ko lokacin da yake karatu a kasar waje ga dai mata birjik suna yawo half nacked wasu har tallahn kan su suke kawo mishi amma koda wasa bai tab'a jin kwatancin abinda yake ji game dani ba akan su. "Why! Why her?" Ya furta can kasan makoshi ganin babu mai bashi amsa yasa ya koma cikin parlour ya zauna ya dafe kai yana neman mafita. Na dad'e jingine da jikin kofan ido na rufe ina wani irin murmushi da yake fitowa daga karkashin zuciya ta, me ya faru tsakanin mu yanzu? Na tambayi kaina. "He just kissed me" nacewa kaina ina rufe fuskata da tafin hannaye na duka biyu ina kara fad'ad'a murmushin da nake saboda ina ayyanawa a raina cewa yana sona, yes yana sona in ba haka babu abinda zai saka yayi kissing na. "BA SONKI NAKE BA, ZAN AURE KI NE DAN IN KAUCEWA AUREN DA ABBA NA YAKE SON YI MIN....." Hannuwana na saka na toshe kunnuwa na dasu saboda yanda nake jin wa'yan nan munanan kalamai suna min amsa kuwwa a kunne na kaman an kawo loudspeaker saitin kunne na ana min magana dashi. Girgiza kai na na fara yi Ina hawaye kada in yaudari kaina Zafar ba zai tab'a so na ba yasha furta min haka da bakin sa sannan ya tabbatar min da ba zai tab'a sona ba zai sake ni ne in time din alkawarin mu yayi. Na tabbata yanzun ma haka take kawai ya tsiro da wata dabara ce yanda zai yaudare ni ya gama dani kamin mu rabu , dole ne inyi taka tsantsan domin tsira da mutunci na duk da yanzu ni da Kai na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99