Chapter 74
Chapter 74
mai nisa sannan yaji an ingiza shi ya Fad'i kasa daga bays suka kunce mishi idon, farko ma hasken rana ne ya fara dallaro mishi ido yayi sauri ya runtse idon tsawa da yaji an daka mishi yasa ya bud'e ido babu shiri yana rarraba ido duk da yanda yake jin zafin ranan har cikin kwakwalwan shi. Manyan sojoji ne sun kai su goma zaune akan kujera da wani table a gaban su, gefen su kuwa hagu da dama duk wasu sojojin ne rike da bindigu sunyi layi-layi. "Ka shirya gaya mana komai Mallam Hassan?" Daya daga cikin mayan sojojin ya tambaya yana kallon Baba da yake durkushe a gaban su kan shi a kasa kaman mai neman gafara, cikin rawan jiki yace " wallahi Allah zan fad'a muku ...Allah zan sanar muku da duk abinda kuke son sani ". Gyad'a kai sukayi gaba dayan su cike da gamsuwa " yace toh menene shirn ku na gaba?" Mukut Baba ya had'iye wani bushasshan yawu na fargaba da ya tsaya mishi a makoshi ya bud'i baki yace" Shirin mu na gaba shine........". Tofa me Baban ZAREEFA yake shirin dad's🤭🤭🤭🤭 [12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *47&48* Bai san adadin lokaci da ya b'ata a cikin duhun nan ba yana nan dai zaune ne kawai amma ba zai iya cewa dare ne ko rana ne ba, addu'oi kuwa babu wanda baiyi ba yana son yin sallah amma rashin sanin inda gabar yake da kuma rashin ruwan alwala yasa ya hakura. Zuwa wani lokaci ya tuna dai ko azahar ba'ayi ba suka kawo shi nan dan haka ya tashi yayi taimama da d'an kasa- kasa daya samu ya kabbara sallah, azahar,la'asar da magarib ya sallata ya sallame saboda tashin hankali da yake ciki ko yunwa baya. Haushin karnuka da yake jine ya san cewa dare yayi nisa sosai bai tsaya b'ata lokaci ba ya kawo sallah isha'i da 'yan nafilfilu ya raya daren ko gyangyad'i baiyi ba balle bacci, rabon da Baba yayi nafilan dare shi da kan shi ya manta balle Kuma wani. Da washe gari yana zaune makoshin shi duk ya bushe saboda kishi yaji an dallaro mishi fitila a ido wanda ya haddasa mishi rintse idanun nashi babu shiri har wani radadi yaji idon na mishi ko dan ya kwana a cikin duhun ne oho. "Oga he don wake up" yaji wani kakkausar murya daga wajan ana magana,tafiya ya fara ji na mutane da bai san adadin su ba sun nufo inda yake a tsorace ya mike tsaye jikin sa na karkarwa yana jiran yaga ta ina zasu bullo dan har yanzu bakin shi da suka buge yana nan a kumbure har fuskan shi. Cak yaji kafan ya d'auke lokaci daya amma baya iya ganin su kasancewar har yanzu hasken daidai fuskan shi yake wajan su kuma duhu. "Kai ne Mallam Hassan ko?" Yaji an daka mishi tsawa, jikin shi na cigaba da bari ya gyad'a musu kai. "Open ur mouth and answer me my friend, nace kaine Mallam Hassan?" Duk da bai fahimci turancin da akayi mishi ba amma cikin sauri ya amsa da " nine...nine Mallam Hassan ranka ya dad'e". " Good bana son gardama ko taurin kai ka gaya mana menene next target d'in ku me kuke shirin aikatawa a gaba?" Yaji wani murya daban ya tambaye shi cikin gurb'ataccen hausar shi. Cikin rashi fahimta yake kallon inda yake jiwo muryan su duk da baya iya ganin su dan kwata-kwata bai gane inda zancen nasu ya dosa ba. "Ka bamu amsa ba wai ka tsaya zare Mana ido ko kuma kana so mubi da kai yanda muka bi da partner ka" wani cikin su ya kara daka mishi tsawa, Baba duk ya rud'e ya rasa inda zai saka ran shi yaji dad'i sannan ko kad'an bai fahimci tambayan nasu balle ya basu amsa kaman yanda suka bukata illah jikin shi da yayi ta b'ari kaman an jona mishi shocking. "Dole yayi mana taurin kai oga saboda babu wani criminal da za'a kawo ya amsa laifin shi cikin sauki but zamu bi dashi yanda muka bi da sauran. Step 1" yaji wani murya daban har yana amsa kuwwa, kalle-kalle ya fara yi a matukar tsorace kamin ya ankara yaji ruwan sanyi harda kankara suna zubowa daga sama daga inda yake tsaye nan da nan yaji wani irin sanyi da tunda yake bai taba jin irin shi ba ya rufe shi a take ya fara rawan sanyi hakoran shi na had'uwa da juna. "Ka huta cikin sanyin ka in ka shirya mana bayani zamu dawo" wani yace suka juya suka bar Baba cikin rawan sanyi yana son tsaida su amma ya gagara bud'e baki balle magana ya fito, yana ji yana gani suka tafi tun yana jin sawun kafan su har ya daina ji. ****************** A gidan mu kuwa babu wanda yayi baccin kirki saboda tashin hankali domin ganin har dare babu Baba babu labarin shi, masu nafila nayi masu addu'oi nayi in ka cire gwaggo Aisha da tasha baccin ta harda minshari, koda gari ya waye Baban Dije da wasu 'yan uwan Baban mu suka fita bin baracks ko Allah zai sa su dace su sami inda aka kai Baba. Bayan tafiyan su babban tukunya Inna ta daura a tsakar gida na abincin sadaka da tayi niyya tun cikin dare sanin cewa sadaka yana maganin masifa, Inna Asabe tana gani ta fito ta kama mata suka fara aikin tare. A can dakin Gwaggo Aisha kuma drama ce ta kaure tsakanin su ita da Hajara kan cewa wai lalle sai ta fita tazo gidana sun kammala aikin su da suka fara ita Kuma Hajara tace babu inda zata je ta bar ta taji da tashin hankali na rashin Baban mu. "Ke me yasa baki da wayo a rayuwar ki ne, ban san yaushe zakiyi hankali ba Hajara wani uban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99