Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,308 words 0 views Progress saved
Download Book

irin na d'azu,yana saka kafa a gidan kamshin abincin ya mishi maraba wanda sai da ya had'iye yawu yana bin tsakar gidan da kallo,yaji tsit kaman babu kowa a gidan saboda kowacce tana d'aki da yaran ta suna kwasan gara. Da gangan ya d'aga murya wai dan Inna taji ta aiko mishi nashi ya hau fad'an an watsar da kaya a hanya amma aka rasa wanda zai kula shi. Yana nan tsaye yanayi Ibrahim d'an gidan Inna Asabe ya fito da kwanukan da suka ci abinci yana kokuwa da kashi tare da tand'e yatsu. "Kai zo nan,zo ka kwashe kayan nan" ya yafito Ibrahim da hannu yazo yasa hannu ya kwashi kwanuka guda biyu da suke gefe har ya juya zai tafi ya rike shi murya kasa-kssa ya ce," kai yauma Bintun ce tayi girkin" gyad'a mishi kai Kai yayi dan santin kashin ya hana shi magana. Maida hankalin shi yayi kan d'akin mu da muka sauke d'an yalolon labulen mu, juyawa yayi ya shiga d'akin shi ya zauna jiran ko yauma za'a kawo mishi. Ya kai kusan rabin awa zaune yana kallon k'ofa amma ko motsin mutum bai jiba balle yaga mutum,tsaki yaja a karo na ba adadi ya mike ya fito tsakar gida tare da kama hanyan waje,bukutin roba na Maman Dije da yake ajiye a gefe akai ya sauke haushin sa sannan ya fita,ji kake kararass ya fashe sakamakon harbi daya kaiwa bucket din da k'afa. Fita yayi yana ta zage-zage shi kad'ai dole ne yasan yanda zaiyi ya shawo kan Inna ta kamin girkin ta ya zagayo. Da washe gari ba girkin Inna ta bane d'an haka indomine ta girka min na karya dashi ta bani talatin kud'in tara na fita makaranta cikin tsantsan farinciki domin haka naga sauran yara ake musu nima yau anyi min. Sosai a ranan na mayar da hankali na nayi karatu tsabani da,karfe d'aya dai-dai aka tashe mu na kama hanyan gida. Tun daga zaure na fara jin muryan Gwaggo Aisha tana zagina tare da aibata ni ga dukkan alamu kuma Baban mu take fad'awa,a jikin bango na makure naki karasowa sanin halin Baban mu ya kware a rankwashi. "Munafuka daina kallo na da shegun idanunki kaman na mujiya" cewar Gwaggo Aisha tare da aika min mugun kallo. "Ke Aisha ba kya kula da lokacin daya kamata ki tari mutum da magana,ni yanzu a gajiye na shigo hutu nake nema" yana gama fad'a kuwa yayi hanyan d'akin shi ya shige ya bar Gwaggo Aisha baki bud'e. Kuyi manage ba yawa *Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 500 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*. 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Addu'a Idan Mutum Ya ga wani abu mai ban Mamaki, ko na farin ciki* سُبْحَانَ اللهِ! Subhanal-lah!. Tsarki ya tabbata ga Allah. اللهُ أَكْبرُ! Allahu akbar Allah ne mafi girma. *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._ *6* Yanda Gwaggo Aisha ta bud'e baki ta kasa rufewa saboda mamaki kowa a wajan sai da ya wangale baki muka bi Baba da kallo har ya shige d'akin shi abin sa ko waigowa baiyi ba. Wata wawiyar Ajiyar zuciya na sauke na samun tsira daga rankawshin Baba, kasancewar a tarihin rayuwa ta yau shine karo na farko da Gwaggo Aisha ta kawo kara ta yaki fad'a ko kuma duka na dan haka cikin jin dad'i fuska ta d'auke da murmushi na wuce d'akin mu. "Ni kikewa dariya dan uban ki,toh ba dani kike ba da lusarar uwar ki kike " cewar Gwaggo Aisha cikin matukar fushi. "Ni wallahi Inna banyi mata magana" na fad'awa Inna cikin marairaicewa saboda ganin irin kallon da take bi na dashi. Kwafa kawai tayi ta cigaba da d'inkin hular ta da take,cire uniform na nayi na saka kayana na gida har mukayi sallah Gwaggo Aisha nata bala'in ta babu wanda ya kula ta sai can Inna Asabe ta saka baki. "Kema dai Aisha akwai ki da son surutu,kullum Mallam yana biye miki ya zane 'yar nan amma dan yau kad'ai ya fad'i haka kika tashi hankalin ki,ya kamata ki mishi uzuri ki...." "Eh lallai Asabe kike kowa kin samu kaina har ni kika kalla kike cewa ina son surutu saboda wuyan ki yayi k'wari, ba surutu nayi ba uban surutu nayi sai inji bugu ga uwa ta nan" tana yi tana kara matsowa kusa da Inna Asabe wai tana jiran taji bugu. "Hmmm Allah ya tsari gatari da saran shuka kema kin san inda kika baro ta bani ba" cewar Inna Asabe tana kawar da kai gefe. Wannan kalaman sun fi k'ona mata rai akan na farkon nan da nan taci d'amara da d'an kwallin kanta suka fara zagin juna,har baka jin me suke cewa tsabar ihun da suke. Cikin tab'e baki na kai loman abinci na baki na kalli Inna da hankalin ta yake kan hular ta naja tsaki na ce," ni wallahi ihun nan ya ishe ni har ciwon kai na fara ji". "Ina ruwan ki da ihun su ko akan ki suke" da sauri na girgiza mata kai. "Toh kiyi abinda yake gaban ki" da kai na amsa ina jin haushin su suna da daman suyi ta zagin mu son ran su suyi mana abinda suka ga dama amma ko da wasa ita Inna ba zata bar mutum ko d'an gulman su yayi yaji dad'i ba. Basu fasa ba sai da suka tsinci muryan Baba yana magana," ni ban tab'a ganin fitina irin wannan ba,mutum ba shida daman hutawa a gidan shi saboda bala'in ku,mtswww sai ku cinye kan ku na bar muku gidan tunda zama nawa ne ba kwa so" yana gama maganan shi yasa kai ya fice. Duk takaici ya gama rufe shi dama ya dawo gida ne ko zai samu d'an abin sakawa a bakin salati amma hakan ya gagara saima kara mishi tension da sukayi. Majalisan nasu babu dad'i yau yana gani kowa ya sayi abu kiri-kiri suke hana shi dan yau ba shida ko ta sayan soyayyiyar gyad'a ne. Inna Asabe ita ta hakura taja tsaki ta shige d'akin ta ya bar

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99