Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

a jiki ma ya isa mutum kallo sannan ga wani karamin box da yake d'auke da wani tsiririn sarka mai d'an karan kyau da d'an kunnen shi wanda Inna tace tabbas gold ne sai kuma takalmi mai tudu da pos d'in sa suma ko makaho ya shafa su yasan naira tasha kashi wajan sayan ta. "Wannan hidima anya batayi yawa ba, yau kuma harda zinare?" Inna ke fad'in haka cike da jimami. " Yaya ne fa Inna meye abin damuwa saboda ya saya min kaya, ai ya riga ya saba yi " nace hankali na kwance kuma tsakani na da Allah na fad'a. Shiru kawai Inna tayi ba tare da ta kara cewa wani abu ba kasancewar ta gane in banda tarin kuruciya babu komai a cikin kaina, abu d'aya yake sanyaya mata zuciya shine yanda bata sakaci wajan tsayuwar dare kuma duk a kaina. A baya bata damu da lamarin Yaya na sosai ba kaman da yanzu na girma, duk da cikin hikima irin tasu ta manya tana jin yanda muke tsakani na da shi ko hannu na bai tab'a tab'awa ba. Addu'an Allah yayi jagora ya tsare daga duk abin ki tayi ta tashi a wajan ni kuwa cikin zak'uwa da zumud'i na jawo kayan na fara kallo saboda dazu idon Inna ya hana in sake in kalla da kyau har na kosa goben tayi in saka kaya na. Da washe gari da hayaniyan mutane muka tashi gidan mu ya cika ba masakar tsinke gaba d'aya sai naji na takura dan da naje da niyyan shiga bayan gida da gudu na dawo ina kakarin amai saboda yanda mutane suka b'ata shi, ba shiri na samu 'yar karamar jaka ta na had'a duk wasu abubuwa da zan bukata na zuba a ciki na wuce gidan Maa bayan na fad'awa Inna a can zan shirya sai in dawo. Ko da na je gidan Maa itama bata zauna ba gidan namu ta tafi aka bar ni kad'ai a nan Inna ta aiko min da abincin safe da akayi na d'aurin aure,da yake safe ne sai na kasa ci na fito na samu yaro a waje na aike shi wajan mai shayi ya had'o min breakfast na nayi na kwanta bacci ni ban tashi ba sai kusan sha d'aya . Ina shirin shiga wanka naga an ajiye min wani abincin bayan na safe, Allah sarki Inna ta na san wannan duk aikin ta ne, ban ci abincin ba sai bayan na fito daga wanka. Lotion kawai na shafa na saka kayan da Yaya na ya kawo min jiya da daddare, aiko ya zauna das a jikina kaman an gwada ni irin gown d'in nan da bayan yafi gaba tsayi wani sarka da d'an kunnen kira Dubai data sayo min a baya shi nayi amfani da shi dan gold din Inna b'oye shi tayi tace ba zanyi amfani da shi ba,ko minti goma banyi da gama shiryawa ba kiran Yaya na ya shigo waya ta hijabi na d'aura akan kayan na fito. Yau manyan kaya ne a jikin sa tsab'anin da ya murza hulan Ahaiyye a kan sa ya matukar kyau sai zuba kamshi yake. "Yaya naaa ka gan ka kuwa kayi kyau sosai sai kace kai ne angon" na ce mishi ina dariya. Murmushin sa mai sanyi ya yi min sannan ya ce" hmmm ke ba?" "Ni me?" Na tambaye shi ina turo baki. "Ke kanwa tace na ce". "Kanwa only?" Na kara tambaya ina fiddo da ido waje. "Baki kyauta min ba kin ki fad'a min auren nan in time balle in kawowa Baba wani abin kirki shiyasa na ki zuwa daurin auren,amma ki min magana da shi in bashi hakuri da gudumuwa na ko kad'an ne". Ya ce saboda kawar da wancan maganan da muka fara. Gyad'a kai kawai nayi na juya ina dan dariya tun kamin inga draman da zai faru tsakanin Baba da Yaya na. Allah yasa a hanya muka had'u da shi yana dawowa gida da yake ba a kofar gidan mu aka d'aura auren ba a can wani masallaci dake kan kwanan layin mu, yanzu haka suna tare da wasu 'yan uwan sa da sauran abokan shi ne a wajan bayan mutane sun watse. "A'a 'yar albarka ke ce, ina zuwa kuma?" "Baba dama wajan ka zan je, ummm...hmmmm wannan d'in nan da yake aiko maka da kaya shine ya zo yana so wai ku gaisa kuma ya baka hakuri da gudumuwan sa" na karasa kai na a kasa saboda kunya. "Wai wannan mai zuwa wajan ki nan?" Ya tambaya yana zaro ido. Danne dariyar daya taso min nayi ina gyad'a mishi kai. "Toh meye sai mun gaisa da shi,naga a baya ke yake bawa ki kawo min ba yau ma ya baki d'in mana". "Baba nima ban san dalilin da yake son ku gaisa ba yau amma tunda ya bukata kila yana da wani dalilin" na fad'a ina kallon yanda naga duk hankalin Baba ya tashi kaman ba yanzu na gan shi cikin annashuwa ba. "Ki ce ya zo nan ya same ni ina jiran sa a nan " . "Toh Baba" na ce tare da juyawa na koma wajan Yaya na sannan na fad'a mishi sakon Baba. Naso bin shi inga yanda zasu kare da Baba sai kuma naga rashin cancantan hakan na tsaya jiran shi. A nesa Baba ya hango shi yana zuwa yana saka wayar shi a aljihu wanda shi kuma Baba kallon bindinga sak ya yiwa wayan, nan da nan ko zuciyar Baba ta fara zillo kaman zata fito. Cikin matukar sauri ya juya ya fara tafiya kaman zai kifa ya nufi masallaci inda ya bar mutanen shi suna jiran shi, yana cikin tafiyan kuma wani tunani ya fad'o mishi ya canza hanya zuwa bayan layin mu. Yaya na yana zuwa wajan ya ga wayam bai ga kowa ba kaman zai koma kuma ya fasa ya karasa har bakin masallacin aka ce mishi baya nan, haka ya hakura ya dawo ya ce bai gan sa. A hanyan mu na zuwa saloon sai murmushi nake dokawa ina hana dariya ta fitowa na san Baba k'in tsayawa yayi saboda tsoro. Babban wani tsadadden saloon ya kai ni a west end wanda ba abinda basa yi na gyara da kamshi har da lalle, gefe naga Yaya na ya kira wata da alama ita ce babban su a wajan ban san me suka tattauna ba naga ya bata kud'i masu yawa ya fita, nan da nan suka shiga hidima da ni har da su drinks da snacks suka kawo min. Ba b'ata lokaci suka warware yalwantaccen gashi na suka wanke suka gyara shi nan da nan kuwa ya kara kyau sai d'aukan ido yake, wanke min kafa suka yi a wani abin wanke kafa ni dai ban tab'a gani ba sai ranan,fara ce na su ma sun gyara sannan suka yaryad'a min lalle mai ja da baki. Light makeup suka yiwa fuska ta daya kara fito da ainihin kyawu na, wani haddaden net mai kauri da yayi matching da kayan jiki na suka d'auko a shagon nasu suka nad'a min shi in a unique way. Fad'an irin kyan da nayi ma b'ata lokaci ne dan sai in rantse da Allah ban tab'a sanin ina da

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99