Chapter 73
Chapter 73
mai tada hankalin ko wani lafiyayyen namiji daya shaka. Cikin fitan hayyaci ya fara shashhafa duk inda hannu shi ya kai a jikina tare da kissing duk inda bakin shi ya kai yana shinshina ni kaman wani maye, cikin bacci na rinka jin bak'on al'amari mai rikitarwa da farko na zata a mafarki ne dan haka gyara kwanciya nayi na bashi access mai kyau yanda zai ji dad'in sarrafani. Shi kuwa ganin haka yasa ya kara kaimi dan ya zata ido na 2, kwanciya da na gyara yasa botiran gaban riga na wasu suka bud'e har ana iya hango farin fatan jiki na da kuma kirji na a sarari, wani irin wahalallen numfashi yaja ya sauke yana kare musu kallo , damka da yayi musu na fitan hankali yasa na bud'e ido na babu shiri. Mutum na gani mak'ale dani sai wasu abubuwa take min wanda suka girmi tunani na, kara na saka na ture shi da dukkan karfi na sannan na wani irin hansulowa na koma can karshen gado na kankame jikina Ina karkarwa tare da hawaye da suka fara ambaliya kaman an bud'e famfo. Rub da ciki ya kwanta yana maida numfashi kaman wanda yake jinya idon shi kuwa a kulle suke gam, bai min magana ba nima banyi mishi ba sai kuka na da nake yanzu harda shasshek'a, munfi minti 5 a haka sannan ya yunkura da kyar ya tashi zaune ya d'ago idanun shi da sukayi wani masifan ja yana kallo na sannan ya bud'i baki da kyar ya fara magana da muryan shi da bata fita sosai. "Meye haka wai, ya kamata ki tsaya ki nutsu muyi magana yau kwana nawa Ina binki muyi magana amma kin ki sauraro na at least ya kamata ki bani dama ko?" Ya dan yi shiru yana jiran in bashi amsa yaga ko dagowa banyi ba balle in bashi amsa hakan yasa ya cigaba da magana. "Na san abinda nake miki kwana 2 nan baya cikin agreement d'in da mukayi tun farko, but ba yanda zanyi ne saboda its beyond my control , abinda nake ji akan ki ban tab'a jin shi akan kowacce mace ba anytime I feel like..... Huuuh no need to explain everything to you" yace yana shafa goshin shi. " But abinda nake so dake just name any amount da kike ganin zai miki ni Kuma nayi miki alkawari zan ninka miki duk abinda kika bukata, just once ki yarda in kasance dake sau d'aya tak kawai besides ba zina muka aikata ba kin ga time da mukayi alkawari ya kusa I can let u go sai in nemi luv of my life, so ya kika ce?" Tunda ya fara magana na tsaida kukana thinking of Allah ya amsa addu'an na hasashe na ya zama gaskiya kan shima ya fara sona, sai dai me kalaman sa na karshe su suka kusa tarwatsa min zuciya, dama nima yaudaran kai na nake tayaya mutumin da ya sha nanata min baya so na zai soni rana tsaka?...... Gutun hawaye da suke fuska ta na goge ina kallon shi da murmushi akan fuska nace " do you think I'm that so cheap da har kake ganin kana da dukiyan da zaka bani dan kasancewa dani...... Ni ZAREEFA" girgiza kai na nayi ina hana hawaye na zubowa na cigaba " a duk fad'in duniyan nan babu mai wannan dukiyar da har zai iya sayan martaba ta kaima sanin kan kane ko auren Baba nane ya tilasta ba wai wani abin hannun ka yasa na amince maka ba. Mutum daya yake da wannan daman shine masoyi na mai sona tsakani da Allah ba wai sura ta ko sha'awa ta ba dan haka this should be the last time da zaka shigo min d'aki cikin dare or try something stupid with me and see wallahi zan kira Abba in sanar mishi duk abinda ya faru tun daga farkon auren har zuwa yau". " Shut up just shut up ke har kin isa ki bani rules in my own house' who do you think you are?" Ya katse ni cikin tsawa da har saida na firgita na d'an ja baya. "Ni zaki kalla kiyiwa maganan wani katon banza da aure na akan ki, how dear u?" Yace yana zaro min ido yana huci kaman zai buge ni. Nuna ni da yatsa yayi cikin dacin rai kaman zai ce wani abu kuma naga yayi hanyan waje fuuu tare da banko min kofa kaman zai b'alla ta, dabas na zauna kan rug dake shimfid'e gaban gadon ina mai fashewa da kuka mai cin rai shikenan ni kuma haka tawa kaddarar take daga wanda ya gudu ya barni da syayyar sa sai kuma mai gasa min aya a hannu saboda skyayyar sa, a yau na gama tabbatarwa Zafar ba zai tab'a Sona ba kaman yanda ya sha fad'a min. Kaico na inama zai iya sona koda rabin yanda nake son shi ne da na more rayuwa amma da alamu banida sa'a a rayuwa haka zan mutu ina dokon soyayyar shi a zuciya ta. Da kyar naja jiki na zuwa kan gadon na cigaba da kuka na , shima tunda ya fita a d'aki na yake hawaye dan wani irin kuna yaji zuciyar shi nayi mishi zai iya ratsewa da Allah ba'a tab'a fad'a mishi kalma mai d'aci da k'ona zuciya irin wannan ba. Da auren nashi akai na har nake iya kallon tsaban idon shi in mishi maganan wani katon banza can, wani wawan naushi ya kaiwa bango kaman shine yayi mishi laifin yana cigaba da hawayen takaici. A wannan daren babu wanda yayi wani baccin kirki tsakanin mu kowa da abinda yake tunani har gari ya waye. ************************ A b'angaren Baban mu kuwa tunda suka had'a shi da ruwan sanyin nan sukayi tafiyar su suka bar shi cikin azaba tun yana sanin inda hankalin yake har ya suma ya zama bai san a Ina ma yake ba, sai bayan awa daya sannan ruwan ya daina zuba sannan suka kunna wata na'ura Mai feso mishi da zafi, nan da nan d'akin ya kuma d'aukan zafi wanda ya haddasawa Baba farkawa babu shiri. Sunayan Allah yake ta ambata yana jin shi kaman a cikin wuta yake ya rasa ta inda zafin yake shigowa shi dai bai ga wuta a d'akin ba. Wata murya yaji ya cika wajan ana " ka shirya gaya mana gaskiya ko har yanzu baka horu ba" " Wallahi zan fad'a...zan fad'i duk abinda kuke son ji dan girman Allah ku cire daga zafin nan kome kuke so zanyi muku na rantse muku..." Baba ya amsa musu cikin tsananin azaba. Wani irin dariya yaji an kece dashi sannan kaman da wasa yaji zafin yana raguwa zuwa kaman minti goma yaji zafin ya ragu sosai, haske suka Kara kunnawa yanzu ma daidai wajan shine kad'ai hasken ya tsaya baya iya ganin su sai haske da yake jin yana saka idon shi zugi da rad'ad'i, mutum daya yaga ya ratso ta cikin wani glass sannan ya shigo inda yake amma idon sanye da wani bakin glass hannun shi rike da bakin kyalle yana zuwa kusa da Baba ya d'aure mishi idon sa sannan ya finciko hannun shi ya fara Jan shi suka fara tafiya. Saida sukayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99