Chapter 53
Chapter 53
jijjiga kofar wai ko zan zo in bud'e ni kuwa Ina can ina ta sharar bacci na ban san ma yana yi ba. Tsaki yayi tayi yana cizon yatsa da takaicin kulle kofa da nayi,nan da nan wani tunani ya fad'o mishi ai ba za'a rasa spare keys na ko wani kofa ba, cikin sauri ya juya da nufin zuwa d'akin shi ya duba har yayi steps 2 zuwa 3 ya tsaya cak sakamakon wani abu daya fad'o mishi a rai. Kar dai ace na rufe d'aki nane saboda ina tunain zai shigo min as ango?? Hmmm inko haka ne ba zai bud'e ba balle in saka ran cewa wani abu ya kawo shi, God forbid ba zai tab'a abinda wannan kucakar zata raina shi ba, dangwaran da ledan hannun shi yayi a bakin kofan ya juya ya nufi nashi d'akin . Tun a parlour shi ya fara kunce necktie dake wuyan shi da maballan suit din shi a haka ya karasa cikin bedroom ya gama cire kayan ya shiga bathroom, wanka yayi da expensive liquid soaps da kamshin su ya cika gidan gaba d'aya bai dad'e ba ya fito sama-sama ya shafa d'an 🧴 a jikin shi ya saka white pyjamas d'in shi masu taushin gaske ya bi lafiyar gado. Tsaki yaja shi kad'ai yana kara Jan bargo ya lullub'e jikin shi da kyau yana mai jin haushin kan shi na kawo irin wannan tunanin a ran shi,wai da auren gaske yayi da yana can tare da amaryan shi " Allah ya sauwake 'yar Mallam ce fa Kuma ka aure ta ne dan gujewa Abba ko ba haka ba?" Ya tambayi kan shi yana lumshe ido saboda ya fara jin bacci " Anya zan iya bari tayi min wata 2 a gida? she have to leave within a month kamin nan na samu d love of my life". Tun yana suratai wa kan shi har bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi. Hankali kwance na sha bacci na ban tashi ba har sai da naji ana kiraye-kirayen sallah duk da naji na kwanta shiru ina jiran inji Inna ta leko ta tashe ni amma shiru, ganin kila zamu makara yasa na tashi a raina ina mamakin lafiya kuwa yau Inna bata tashi ba. Da Addu'an tashi daga bacci na tashi zaune ina murza ido, a firgice na mike tsaye ganin Ashe ba a d'aki na da na sani na kwana ba domin Ina kallon komai tar dan ban kashe wutan d'akin ba na kwanta haka saboda tsoro. A hankali na fara bin d'akin da akace nawa ne da kallo tare da mamakin irin dukiyar da aka narkar a ciki, ba komai ya saka ni mamaki ba sai dan jiya naji suna ambatar cewa Inna ce tayi min kayan d'aki. Kara kallon wannan Royal set maroon da sirkin baki nayi sai sheki suke kaman an shafa musu mai ko kuma ince kaman da glass akayi su yanda suke walwali da d'aukan ido, ko turaren wuta,humra,kulacham da sauran su da aka jera min a cikin tangamemen show glass abin kallo ne dan kwalaben kad'ai sunyi jarin wani. Jiki a mace naja kafafu na cikin bathroom nan d'in ma tsayawa nayi ina kare mishi kallo yanda komai na ciki fari ne kal kuma duk na zamani da kyar na gane wasu abubuwan na had'a ruwan zafi nayi wanka dan jiya tsoro ya hana ni yi, alwala ta na d'auro bayan na gama wankan na fito. Aunty Fatima duk ta nuna min yanda suka ajiye min kaya na duk da ba'a kawo min lefen ba na gidan mu ne da Inna tayi min, wata atamfa doguwar riga na saka wanda ya sha dinki mai kyau kuma cif na cika shi, abin sallah na shimfid'a na saka hijabi na kabbara sallah. Ban tashi a kan abin sallah ba sai kusan 6:40 domin sai da nayi azkar na safe na d'an yi karatun Qur'an sannan na mike na cire hijab na ninke su da sallaya na ajiye gefe, shafa shaffafen tommy na da yake kaman babu hanji nayi jin yana kukan yunwa dan ni kaina na manta yaushe rabo na da abinci, da fa auren gaske nayi ko kuma da Yaya na na aura I know he will pampered me yana rarrashi yana bani a baki ba zai tab'a bari in kwanta da yunwa ba, but dubi wannan mugun ko irin Kazan amarci da naji ana bada labari bai kawo ba. A take Kuma wani sashin zuciya ta ya kwab'e ni da cewa ta ina zan sammaci wani kazan amarci daga gare shi bayan ya jadda min dalilin aure na da yayi kuma baya gajiya da nanata min ba so na yake ba. "Hmmm" kawai nace a raina tare da niyyan neman abinda zan ci, kaman mai tsoron kada wani abu ya kamata na bud'e kofa na leka naga wata fitinanniyar parlour na da ya kusan saka numfashi na barin jikina. "Masha Allah " nake ta maimaitawa da jinjinawa Inna, yanda parlour nan ya tsaru koma wanene kai dole ne ya burge ka ba'a cika mashi tarkace dayawa ba but yanda aka jera komai a position din shi sai ya fito da kyan parlorn cushions labulaye duk kalan su daya wato peach nd milk color ne sai tangamemen plasma da sauran abubuwan kallo suma wajan su d'aya, abinda da yafi birge ni wasu manyan flower vase da aka ajiye a kowani angle shima ya bada ma'ana. Tafiya na farayi zuciya ta na dukan 3-3 dan ina tsoron had'uwa da wannan dodon, ina bud'e kofa wani parlour na kara gani har yafi nawa komai I mean girma da dukiya da aka zuba a ciki baya lissafuwa shi kuma nan komai na cikin sa brown nd white ne. Nan ma da naga kallon ba zai fishe ni ba na fara duba kofofi da na gani a cikin parlour dan neman kitchen na san anyi min gara ba na wasa ba so ko indomie ne in samu in dafa in sakawa cikin nan nawa da nake ji sai kara ya mutsewa yake. Babu tunanin komai kai tsaye na nufi wata kofa da hankali na ya kwanta dashi na bud'e, wani sanyi da wannan sassayan kamshin sa suka min maraba da sauri na waro ido ganin inda na kawo kaina, a can tsakiyan tanfatsetsen gadon shi na hango shi kwance yana baccin sa cikin kwanciyar hankali dan bai san ma na shigo ba a hankali na mayar da kofan na rufe kaman yanda na samu na juya cikin sauri na koma inda na fito domin har naji na daina jin yunwan. In ba dan Allah ya taimake ni yana bacci ba wani bayani zanyi mishi na kare kaina, da shikenan sai yace biyo shi nayi. Ido na rufe sai sauri nake buri na in shige d'aki na naji nayi tuntube da abu a gefen kofata, tsayawa nayi Ina kallo tambarin jikin ledan ba sai an fad'a min ba na gane kajin amarcin ya kawo min amma banida darajan da za'a miko min hannu da hannu shine ya dangwarar min ita anan? A zuciye nayi ciki tare da banko kofa Ina huci ni kad'ai lalle ya cika d'an rainin hankali, nima ban d'auka kaman yanda ya ajiye abin shi haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99