Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,229 words 0 views Progress saved
Download Book

sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._ *2* Kasa cire rigan nayi na zaro ido waje ina kallon Innara na ce," Inna kud'in common entrance d'in kika basu?" "Ya kike son inyi? Kin san halin Aisha sarai a gidan in ta fara fitina zata kai awa goma tana yi ba tare da ta gaji ba,ni kuwa kin san ba iyawa zanyi ba gwara in bata a rabu lafiya gobe ma idan zaki shigo gida kada ki natsu " Inna kenan ta bani amsa. Zama nayi da rigan a wuyan na ina hawaye na ce," shikenan za'ayi banda ni kenan,ko yau ina kallo akayi ta rabon abubuwa a makaranta ni ban samu komai ba akan 200 balle 1500 nasan gobe ko class ba za'a barni in shiga ba". "Haka Allah ya kaddara ba zaki rubuta ba a wannan shekaran amma kiyi hakuri zuwa shekara mai zuwa ko kuma muyi addu'an Allah ya kawo wata hanyan,kinji ko?" Inna ta fad'a min cikin rarrashi. Goge hawayen fuskan ta nayi na tashi na cigaba da cire uniform d'in na ba tare da na kara cewa komai ba. "Ki d'auki hamsin cikin d'ari ukun daya rage kije ki sayi wani abin kici" cewar Inna. Dariya na fara kyakyalewa da shi harda rike ciki sai da nayi mai isa ta sannan na ce," ai inna ciki na kaman zai fashe saboda koshi, dan lokacin da Hajara tayi b'ari almajirai suka fara wawaso nima roba 2 na wawashe na cinye tas abina Gwaggo Aisha data ji haushi kinji yanda ta zuba min dundu a baya Wallahi ko jin zafi ma banyi ba". Cikin tsuke fuska Inna ta ce," wai ya akayi kika yi musu b'ari? Kullum inayi miki fad'an ki natsu amma ba kya ji ko?" Daina dariyan nayi sannan nayi kalan tausayi na fara bata labarin abinda ya faru a makaranta har zuwa yanda mukayi karo da Hajara,ajiyar zuciya Inna ta sauke tana mai jin tausayin na ta ce," hakuri zakiyi Zareefa insha Allah wata rana sai labari,karatu kuma da yardan Allah zakiyi shi". Gyad'a kai kawai nayi na fita yin alwala zahar a lokacin duk yaran gidan anyi musu abin sana'a duk sun fita talla,ina idar da sallah na fara shirin islamiya shi kam cikin dokin zuwa nake shirin na kasancewar a can bana takura kaman boko. Akwai wani Malamin mu da yake d'aukar mu Qur'an shi ya tsaya minsosai sabo kokarin na dan har kudin wata 500 shi yake biya min domin kullum dai-dai nake kawo hadda ta yanzu haka mun bawa izufi 30 baya. Ina gama shirin na nayiwa Innata sallama na tafi. Ina fita Inna ta kwaso uniform dana cire ta hau wanke min da sauran Omo da ta rage jiya,tanayi tana jin su suna ta haice-habaicen su ta gama ta shige d'aki ta rabu dasu. Mun taso a islamiya ni da kawayen na muka nufi gida muna d'an wasan su na yara,muna zuwa dai-dai gidan mu na fara jin muryan Baban mu yana ta masifa kaman zai ari baki. Dariya sauran yaran suka fara har suna lekowa ta rububben ginin daya zagaye gidan. Jiki a sanyaye na nufi cikin gidan namu dan nasan yanda Baba yake d'aga muryan nan nasan da inna ta yake,muryan Gwaggo Aisha naji tana kara zuga Baba da fad'in karya da gaskiya. "Toh ai Mallam dan ma baka ga irin rashin kunyan da yarinyan nan tayi min a waje ba,inda zaka san da gayya ta b'arar da kayan sana'a shine,itace farkon daka wawa sannan sauran almajirai suka bi bayanta. Koda yake b'ata baki na nake ina gaya maka abinda ya faru na san babu wani hukuncin da zaka d'auka tunda 'yar amayar ka ce abin sonka". A fusace Baba ya juyo kanta yana," wannan wani irin maganan banza kike min matar da *Ba sonta nake ba* aka lika min ita dole yasa na karb'a dan kar inyi asaran kud'i na,amma wallahi Aisha kin cuce ni".. Gwaggo Aisha ta saki shewa dama Kalmar da take son ji kenan. Baba ya cigaba da fad'an shi inda yake cewa," duk kin bi kin b'ata yarinya bata ganin kowa da darajan a gidan nan da anyi magana kice wai boko take sai kace ki d'in bokon kikayi aikin banza kawai zata zo ta same ni a gidan sai jikin ta ya gaya mata" Yana juyowa muka had'a ido ina can makure karshen bango ,aiko baiyi wata-wata ba ya nufo ni zai sake min wannan rankwashin sa nan da sai yasa kullum na saki fitsari a wando. A guje nayi d'akin mu na shige kamin ya kama ni sanin cewa in ba wani babban dalili ba baya shigowa,cikin sa'a kuwa bai shigon ba ya tsaya a tsakar gida yana cigaba da fad'an,sam na daina jin me yake cewa domin ganin Inna ta na kuka abinda ban tab'a gani ba kenan tun tasowa ta dan komai akayi mata a gidan ko Baban mu ko matan gidan sai dai tayi murmushin mai ciwo tace akwai Allah. Toh tana furta wannan kalman duk yanda za'ayi da ita ba zata kuma tankawa ba na sha tambayan ta me yasa itama ba zata ke rama cin fuska da ake mata ba sai dai tayi wannan murmushin nata mai ciwo ta ce," bakomai Zareefa akwai Allah" daga nan kuma ba zata kara cewa komai ba. Zuwa nayi har gaban ta na durkusa a gaban ta tare da d'aura hannu na kan guiwoyin ta na ce," Inna kuka kike,meya same ki?" Duk na jero mata wayan nan tambayoyi a lokaci guda. Murmushin nan nata mai ciwo tayi min kana ta ce," babu komai ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga ido na". Ba dan na yarda ba nayi shiru nasan ko abinda ake mata a gidan nan dole tayi ta kuka kullum,komawa gefe nayi na zauna ina kallon ta tana dinke min wuyan uniform d'ina daya yage bata kuma yarda ta zubar da hawaye ba. Da washe gari da safe bayan na sayo alale na naci Inna ta bani 200 a cikin kudin daya saura ta ce in kai makarantan nima a bani bani sabon uniform d'in inya so ko shekara mai zuwa sai in zana jarrabawan. Cikin matukar farinciki na nufi makaranta yau nima za'a bani kyautan kayan makaranta kaman sauran d'alibai. Direct office d'in principal na wuce ina jin kaina yau kaman bani ba,bayan na gaishe shi na bashi kud'in na ce ni jiya ban samu daman zuwa ba shiyasa ban samu komai na rabo ba. Tambayan shekaru na yayi na fad'a mishi ya ko duba ya ciro uniform sabo dal ya miko min,murna fal jikina na karb'a amma sai na kasa tafiya ina jiran jaka da sauran tarkace. Ganin na ki tafiya ya ce," me kike jira kuma?" Kasa nayi da kaina na ce," Sir su jaka da takardu suma ban samu ba". "Okay toh sai gobe ko anjima dan suna store,ya suna ki kuma a wani class kike?" "Suna na Fatima Hassan,kuma ina class 6A" na

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99