Chapter 83
Chapter 83
mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wannan page din naku ne masoya na kuyi yanda ku ka ga dama dashi, ina mika godiyata gare ku kan yanda kuka nuna min kauna ba abinda zance sai dai nayi muku fatan dacewa da duniya da kiyama ina matukar alfahari daku a duk inda kuke kan jajircewan ku sai da kuka sa na dawo online, Allah ya bar kauna bounch of love*. *58&59* A baya na kulla ce shi naji na tsane shi saboda duk halin da na tsinci kaina a baya shi nake daurawa laifin domin da bai guje ni ba da ban fad'a cikin tashin hankali da nake ciki ba, saidai wannan bayanai da naji yanzu ya ruguza min lissafi yasa naji zuciyata ta karye tausayin sa duk ya cika ni na irin rayuwar daya taso a ciki da kuma halin da maraici ya jefa shi a ciki. Kuka sosai nake kaman raina zai fita yasa hankalin kowa na parlour ya koma kaina suka shiga bani baki dan sun san irin shakuwar da yake tsakanin mu dole ne inyi kuka. Sai a lokacin Gwaggo Aisha ta kai duban ta gare ni a zabure tayi baya tana kare min kallo tun daga kan kayan jikina har tsarka da d'an kunne da na saka, sosai hankalin ta yayi kololuwar tashi irin rayuwar da take burin ganin yayan ta a ciki shine na samu. Bayan an jajantawa juna Baban Dije yace mu fita a bar Baba ya huta, duk muna shirin fitowa sai ga jameela kaman an jefo ta ta fad'o d'akin tana layi, ganin mutane cike da parlour yasa ta fara bin kowa da kallo har idon ta fad'a kan Baban mu da yake kwance shima yana kallon ta, for the first time yaji zuciyar shi ta kuntata da yanayin da yaga 'yar cikin sa ta zama sanadiyan rashin kulawar shi gare mu. Zaro ido tayi harda dafe kirji da murya ta yan maye tace " lah Baba dama basu kashe ka ba suka bar ka a raye har ka dawo gida...." " Ke baki da hankali ne mahaifin naki kike fad'awa irin wayan nan kalamai” Gwaggo Aisha ta daka mata tsawa ta hana ta karasa maganar da tayi niyyan fad'a. Kyalkyalewa da dariya tayi tana nuna uwar tata da hannu tace kai Umma bayan kece kika fara d'au......." Fincike hannun ta da taji uwar nata tayi yasa bata karasa abinda tayi niyyan fad'a ba tabi bayan mahaifiyarta da take Jan ta kaman ta kife suka fita a d'akin duk muka bi su da ido kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi, Hajara kuwa duk kunya ya rufe ta ta kasa kallon 'yan d'akin. Ajiyar zuciya Baban Dije ya sauke tare da furta " Allah ya kyauta, yanzu kowa ya fita a bar Yaya ya huta...." Bai gama rufe bakin shi ba kowa ya mike ana kara mishi Allah ya sauwake sannan muka fita tare da ja mishi kofa. Maimakon Baba yayi baccin kaman yanda akace sai dai kunan da zuciya shi keyi ya hana shi jin rad'ad'in da jikin nashi ke mishi balle har yaji wani abu wai shi bacci, yanzu wannan 'yar cikin sace a haka har take mishi fatan mutuwa saboda abinda yayi musu. Tabbas ba zai taba ganin laifin kowa a cikin mu ba domin ya cancanci fiye da haka ma dama duk wanda Bai bi hanyar da Allah yace yabi ba dole zai ga sakamakon abinda ya aikata tun kamin akai ga zuwa kiyama. Sai dai shi a yanzu babu abinda zaice sai ALHMDLLH ga Rabbil Izzatti daya ankarar dashi halin da ya jefa kan shi da iyalan sa amma ta ina zai fara gyara wannan babban barna da yayi??? Kuka sosai Baba yayi kaman karamin yaro Yana yi yana kara godewa Allah har la'asar tayi bai samu ya runtsa ba. Gwaggo Aisha bata saki hannun Jameela ba sai da ta kai ta can cikin d'aki Dan ko a parlour basu tsaya ba, watsar da ita tayi a tsakar d'akin tayi taga-taga kaman zata fad'i da kyar ta samu courage ta tsaya tana auna mata harara tace" wai ke Umma meye haka ina cikin magana zaki wani jawo ni ki kawo ni nan kaman wacce ta fad'i ba daidai ba" " Eh dole kice haka mana kina can kina kokarin tona min asiri cikin makiyana, ba zaki bari komai kike son cewa ki fad'a min a d'aki ba" gwaggo Aisha ta bata amsa itama tana mata mugun kallon. "Ni ina ruwana duk inda naga dama zanyi magana ta kuma babu wanda ya isa ya hana ni, gobe zan dawo in karasa abinda nayi niyyan fad'a sai na fad'a wallahi" tace tana mai juyawa ta kama hanyar fita. Cikin sauri gwaggo Aisha ta riko ta tare da fara rarrashinta kada tayi hakan domin ta san halin Jameela tsab zata aikata abinda yafi hakan ma tunda ba tsoron kowa take ji ba, da kyar ta rarrashe ta harda bata 200 kan ta bar maganan sannan ta hakura ta fita abinta cike da murnan ta samu na cakewa. Duk yanda nake kuka Inna bata kula ni ba wucewa tayi ciki ta kama aikin gabanta, a nan parlour na zube kan kujera na cigaba da kuka na a wannan lokaci babu abinda nake so kaman in sanya shi a ido na domin akwai maganganu dayawa da nake son muyi dashi amma tayaya zan samu daman ganin shi waye zai kai ni??? Zafar gida ya wuce direct sai huci yake shi kad'ai a mota dan sosai kukan Zareefa ya tsaya mishi a rai shaid'an kuwa sai kimtsa mishi yake kan cewa kukan rabuwa da masoyin ta take, tsaki yaja tare da dukan staring da karfi Yana " da aure na akan ta take wannan kukan rabuwa da b'arawon ko kidnapper ko? Hmmmmm I will show her" yace yana dannawa mai gadi horn kaman zai cire mishi kunne. Da gudu yazo ya bud'e gate d'in yana mishi barka da zuwa, ko kallon inda yake Zafar baiyi ba balle ya amsa mishi saima jan motan yayi dagudu kaman zai bi ta kan shi Allah ya bashi sa'a ya kauce cikin zafin nama yabi motan da kallo yana mamakin yau me ya b'ata ran mai gidan nashi haka ya shigo cikin fushi haka?? Ko parking d'in kirki baiyi ba ya fito cikin wani takun da zai tabbatar maka da ran shi a matukar b'ace yake ya nufi kofan parlour ya shiga ya kama safa da marwa shi kad'ai " na san yanzu Allah Allah take in sake ta dan ta samu komawa gare shi ko??" Ya tabayi kanshi. Toh kai meye naka a ciki in ta koma gare shi ko ka manta ba son ta kake ba? Yaji zuciyar shi tana tuna mishi abinda ya manta " yes ba son ta nake ba but dole she should mind her business kamin in sa......" Yay shiru yana jin girman furucin da yake shirin furtawa kuma yana ganin abune da ba zai yiwu ba. Jagwab ya zube akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99