Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,293 words 0 views Progress saved
Download Book

da zuba musu ido ya san in har zai cigaba da nuna halin ko in kula asirin shi zai iya tonuwa. Akwai wata mata daga sudan take ta kware wajan gyaran amare Inna ta nemo kuma wai dole sai kaje gidan ta da farko ta ganki sannan zata duba gyaran daya dace da fatar ki,sun gama magana da Inna saura wai ta tura ni ta ganni, ba dan naso ba Inna tasa na kira Maryam a waya kan tazo ta rakani. Da washe gari kuwa tazo muka tafi gidan nata da yake can Shokari, koda muka je gidan ta cike yake da matan aure harda sabin amare ana tayi musu aiki dan harda 'yan mata masu taya ta tana biyan su. Tarba na musamman akay mana a babban parlour ta inda take sauke bakin ta na musamman,bamu dad'e da zama ba tazo wajan mu bayan mun gaishe ta cikin girmamawa itama ta amsa mana cikin kulawa sannan ta fara aikin ta wato rubuta duk kayakin da zasu dace da fatana da kuma gashi na sannan ta sallame kan cewa sai next week zan fara zuwa, godiya mukayi mata muka fito zuwa gida. A gajiye tibis muka dawo kasancewar Anguwan nata da nisa sosai da namu, mun shigo layin mu kenan wata had'add'iyar mota baka wuluk tazo zata fita mu Kuma muna shiga kaman ance min dago kanki ina d'agawa na tsaya cak tare da dafe kirji na da hannu biyu ina zaro ido waje duk at da same time bakina na rawa nace " YAYA NAAA..." [1/26, 7:14 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *25&26* Yanda ka san statue haka na tsaya ko motsi na kasa yi sai motan nabi da kallo da idanuwana kaman zasu zazzago kasa ga kuma zuciya ta na ta lugude kaman zai faso kirji na ya fito. " What's wrong with you Zareefa daga ganin mota sai kice ga Yayan ki, ke duk wulakanci da mutumin nan yayi miki ashe baki cire shi a ranki ba har kina tunanin zai dawo gare ki Kuma ga dukkan alamu zaki karb'e shi da hannu bibbiyu kenan...." "Maryam shi na gani fa ba imagination bane" na katse ta da muryar tausayi. "What ever, zo muje ga Inna can da kaya a hannu zata shiga gida muje mu taimaka mata ba wannan surutu mara kan gado ba" tana magana ne tare da jan hannu na muka fara tafiya ina waiwayen baya ko zan ga motan zai dawo amma har muka shiga gida banga ko kalar motan ba, kamin mu karasa Inna har ta riga mu shiga gida. A parlour muka iske ta zaune tana kallo babu lodin kaya da muka ga ta shigo dasu, zama mukayi muma anan Maryam tana yi mata bayqni akan zuwan mu gidan mai gyaran amma hankalin ta yana kai na ganin nayi shiru na zama wani iri ba kaman yanda muka fita ba. "Ke kuma lafiyan ki kuwa ana magana kinyi wani zuru dake?" Kaina na mayar kasa ina kokuwa da hawayen da naji suna son zubowa, harara Maryam ta b'alla min tana muskudawa sannan ta bawa Inna amsa. "Kyale ta Inna ni takaici ma ya hanani kula ta, muna shigowa layin nan wai kawai dan taga mota ya wuce kin ga yanda ta daskare waje d'aya wai taga wannan mayaudarin da kyar fa naja ta muka biyo bayan ki lokacin kina shiga gida ga kaya a hannun ki nace muzo mu taya ki". "Ban san meyasa taki sakawa ranta dangana ba ko kin manta aure zakiyi, haka zaki je gida wani kina wanna shirmen da shashanci? Ki kama kanki daga irin haka na gaya miki" Inna take dad'in haka cikin fushi ba tare da ta bawa Maryam amsar tambayar ta ba, nima hakuri na shiga bata ina cewa na daina ba zan sake ba Maryam tana taya ni sai da muka ga ta sauko sannan muka bari. Bayan mun huta mun ci abincin da Inna ta ajiye mana sannan Maryam ta wuce gida tare da cewa sai munyi waya. Tun daga wannan rana suka kara kaimin shirye-shirye da suke Inna ta ta zama busy sosai these days sai fita sayayya suke da Maman Dije wata rana Kuma da Inna Asabe, Gwaggo Aisha ce dai ko kallo basu ishe ta saima yad'a habaice-habaice da take. A haka satin da matan tace zan fara zuwa gyara ya zagayo na fara zuwa wajan gyaran a motan su Maryam wanda Mamanta ce ta d'auki nauyin hakan kullum driver zai zo ya d'auke ni in mun gama zuwa yamma kuma waya kawai zanyi yaje ya maido ni gida kasancewar tace ba'a son ina shiga rana saboda zai maida aikin baya. *************** A gidan su Zafar suma ba karamin shiri suke ba abinka da masu kud'i an gyara mana gidan da zamu zauna duk da sabon gini ne sai da suka Kara da d'an gyare gyare,kayan da za'a saka na cikin wannan gida Abban Zafar ne yayi order su daga kasar waje haka ma kayan lefe na suma duk a kasar waje suka had'o su, shi dai yana gefe yana kallon su yana jin ina zai iya hana su ko kuma inama zai iya fad'a musu gaskiya cewa auren da zaiyi temporary ce ba permanent ba su daina kashe kud'in su amma hakan ba mai yiwuwa bane dan yayi Imani Abban shi yaji abinda ya shirya suna iya batawa na har abada. Sadiq kuwa in ka ganshi zaka zata shine angon kan yanda ya kasa ya tsare komai yana tafiya daidai, baya ko neman shawaran Zafar yake abinsa shi kad'ai ko Kuma suyi da sauran friends d'in su saboda ko ya nema baram-baram suke rabuwa dan haka suma suka ajiye shi a gefe suke abinda ya dace. Ana saura kwana goma bikin duk an gama komai a gidan nasu had'a dasu cards da kayan da zamu saka na duk event d'in

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99