Skip to content

Chapter 59

Chapter 59

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,290 words 0 views Progress saved
Download Book

ya fara tara mutane amma na jiki sun zo ne dan raka Inna taga gida na, su Aunty's dina sune farko-farkon zuwa amma Inna tace musu babu inda zata je bata shirya zuwa a yau ba sai wani lokacin. Ba yanda ba suyi da ita ba tace su suje kawai ta riga ta shirya duk kayayyakin da zasu kai min kaman su kayen lefe na da sauran kayan da ba'a samu kaiwa a ranan bikin ba, Aunty Batul cewa tayi shikenan tayi zaman ta tunda hankalin ta yaki kwanciya da zuwan nata. Ita kuma Aunty Fatima bata yiwa kowa magana cikin su ba ta fita a gidan zuwa gidan Yar uwar su wato Maa ta same ta zaune cikin shirin tafiya su kawai take jira, tana ganin Aunty Fatima ta mike tana nad'a latfayan ta tace " aini tun d'azu ku nake jira sai yanzu Bintun ta gama ne?" "Bintu fa cewa tayi babu inda zata je wai sai dai mu muje..." Ban gane babu inda zata je ba, zuwan uwa taga gidan 'yar ta ranan bakwai ai al'ada ce da ta kafu tuntuni balle tace akan ta za'a fara, maza wuce kice mata ta fito yanzu kuzo mu tafi".Maa ta katse ta a zafafe. Ba musu Aunty Fatima ta juya zuwa gidan mu dama zuwa tayi ta fad'awa Maa ta san ita kad'ai ce zata iya saka ta zuwa ko bata so. Masu rakiya duk sunyi jigum jin cewa uwar Amarya ba zata je ba Aunty Fatima ta shigo taja ta gefe tace mata maza ta shirya inji Maa su tafi, ba yanda ta iya haka ta shirya suka kama hanya a motoci kusan 3 da aka aiko musu daga gidan su Zafar. Ni kuwa hira sosai muka Sha da yasmeen Wanda yawanci labarin Yayan ta take bani kan yanda yake tsoron Abban shi Kuma hakan baya hana shi tsula tsiyar shi Mom tana rufa mishi asiri, sosai nake ta shan dariya harda rike ciki bamu tsagaita ba saida su Maryam suka zo sannan ta bar labarin nashi muka shiga wata daban. Sai bayan azahar su Inna suka iso baki na ya kasa rufuwa da gudu na fad'a jikin ta na kenkeme ta ina hawayen farinciki, ajiyar zuciya Inna take ta saukewa akai akai na kwanciyar hankali dan bata ga alamun tashin hankali a tare da ni ba. Sai a lokacin ta samu kwanciyar hankali ganin gida tana ta jero min addu'oi a zuciya na samun farinciki mai daurewa a gidan mijina, duk wani abu na tarban baki maman Yasmeen ta aiko mana har manyan kuloli na abinci dan haka bamu nemi komai ba aka shiga serving din baki mu dai muna can ciki muna ta hayaniyar mu. A daidai wannan lokacin Momyn Zafar da gayyar ta suka iso ,sai huhhura hanci suke suna kallon mutane a d'age su Inna basu kula su suka karbe su da hannu 2 har ana ce musu ga wajan Zama budan bakin wata daga cikin su tace; "Yau naga ikon Allah mu da gidan dan mu wasu bare ke kokarin nuna mana iko" ta karasa harda rike haba irin abin ya bata mamakin nan, Aunty Batul da bata da hakuri kaman gudawa ta yunkura zata basu amsa Inna da take kusa da ita tayi saurin rike hannun ta Maa da suke zaune opposite da ita ta girgiza mata kai alaman kada tayi magana. Haka ta koma ta zauna tana ta girgiza kafa bala'i na cinta, su Kuma sai da suka gama dariyar su na wulakanci sannan suka nemi waje suka zauna suna zama cikin ikon Allah ko sai ga Maman Yasmeen da wasu mata 3sunyi sallama sun shigo da fara'ar su a take fuskar Momyn Zafar da mutanen ta ya kuntata dan basuyi tsammanin zuwan ta a wannan lokacin ba sun so su gama tsula tsiyar su kamin ta iso ba dan wai suna tsoron ta ba sai dan sun san duk abinda da sukayi zaije kunnen Abba kuma bata manta warning din da yayi mata ba akan bikin ba. A mutunce suka gaggaisa dasu Maman Yasmeen har suna tambayan ina 'yar su take basu ganta ba , Aunty Fatima ce ta shiga ta fito dani bayan ta nada min laffaya ta kara bulbule ni da humra. A kunyace Kuma kaina a kasa na gaishe su suka amsa da kulawa banda su Momyn Zafar da suke amsawa kaman anyi musu dole ko masu ciwon baki, ina gama gaishe su ko minti 1 ban kara ba na koma ciki daman gaba daya a takure nake jina a wajan. Zuwan Baawa duk ya rusawa Momy badget kuma zaman su a inuwa daya babu riba dan haka suka mike da niyyan tafiya Baawan taso tsaida su amma suka ki tsayawa suka Kara wuta, suma ba wani jimawa sukayi ba suka ce zasu tafi aka rabu cikin mutunci. Karfe 3 su Inna suma sukayi haraman tafiya suka saka ni a gaba da nasihu sosai masu ratsa jiki sannan suka tafi suka bar ni ina ta kuka, su Maryam dasu Yasmeen suna ta bani baki suka taya ni gyara gidan sannan suma suka wuce suka bar ni. [6/16, 9:20 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *37&38* A hanyar su ta komawa gida sauran mata suna ta hira da santin gida na amma banda Inna da tayi jigum duk abin duniya ya ishe ta dama shiyasa bata son zuwa Maa ta tilasta mata dole tazo gashi ta ga abinda ya tayar mata da hankalin, alamu ya nuna cewa ni da Zafar babu matsala a zamanta kewar mu amma mahaifiyar shi itace babbar kalubele a cikin rayuwar aure na. Duk yanda miji ya Kai ga son matar shi in har dangin shi basa kaunar ta toh fa babu zaman lafiya balle ace mahaifiyar shi ce sukutum bata son ta ai babu kwanciyar hankali, ajiyan zuciya ta sauke mai nauyi har Maa da

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99