Skip to content

Chapter 63

Chapter 63

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

rufe. Ganin akwai sauran time yasa nayi samosa da meat 🥧 suma nayi package din su a wasu containers masu kyau, duk na jera su a cikin yalwataccen basket sannan na lullub'e saman da tumakasa mai kyau na fito da shi kan dinning sannan na wuce dan shiryawa. Cikin atamfa super fari tas da adon flowers blue na shirya kaina na zauna na dan yi make-up dina sama-sama harda kashe d'auri duk da Ina jin ana kiraye-kirayen sallah magarib ban dakata ba saboda ina fashin sallah, jewelries da na saka duka pure gold ne hakan sai ya kara haskani nayi kyau sosai abina . Sai da na gama kwalliya na sannan na tuna ashe ban ci abincin ba, fitowa nayi kitchen na zuba rabo na a plate shima na zuba mishi komai da nayi harda su snacks din dan a tunani na ba lalle bane yaci abincin gargajiyan da na girka. Ina cikin cin abinci na naji motsin ya shigo Kuma na tabbata yana dinning yana kwasan gara sai dai shegen girman kan shi yasa ba zai tab'a admitting cewa yana ci ba sai dai yace masu gadi yake bawa. Muryan shi ne ya katse ni yana in fito mu tafi, sai da na kara shafe jikina da humra mai dad'in kamshi na yafa mayafi blue mai dan girma na saka takalmi flat shima blue da poss din sa wanda wayata ce kawai a ciki sannan na fito hannu na dayan d'auke da plate din da na gama cin abinci, a tsaye na same shi shima ya shirya cikin kananan kaya riga ash color da wandon jeans fari sol. Ta gefen ido na kalli kan table din ga mamaki na tass ya cinye abincin ko tab'a su snacks din baiyi ba, fasa shiga kitchen din nayi na tsaya na tattara kan table din na wuce dasu Ina kallon shi ta gefen ido dariya na cina ganin yanda ya wani tsare gida wai shi ala dole ba shine yaci ba. Naso in tsaya in wanke plates da muka bata sai dai gudun masifan shi yasa na bari kan sai mun dawo, koda na fito shi har ya fice nima ban tsaya b'ata lokaci ba na d'auki basket da na jera abincin a ciki nabi bayan shi, a dan tsorace na isa ga motan da yake ciki duk da kasan zuciya ta cike yake da farincikin yau zan fita in ga gari dan tunda aka shigo dani cikin gidan nan ko bakin gate ban tab'a lekawa ba. Koda na iso bakin motan sai nayi tsaye na rasa ya zanyi in shiga kada in shiga baya yace na maida shi driver sannan ina gudun shiga gaba yace na raina shi, shahada nayi na bude gidan gaban na shiga ganin ko inda nake bai kalla ba saima mayar da kan shi da yayi yana duba wani abu a cikin locker, sai da na zauna sannan na mayar da murfin na rufe tare da neman inda zan ajiye basket d'in. Basket d'in hannu nawa yabi da kallo kaman zaiyi magana ko me ya tuna oho naga kuma ya mayar da kanshi gefe tare da jan motan muka fita a gidan ba tare da ya Kara kallo na ba. Shiru cikin motan kaman babu mutane a ciki har muka iso wani tangamemen gida wanda ko ta waje kasan masu gidan sun jiku da naira, horn d'aya kawai yayi sai ga mai gadi ya taho da gudu ya zuge mana gate muka kutsa kai cikin hadadden gidan, baki sake nake bin gidan da kallo ashe da gaskiyan shi da yake cewa kada na mishi kyauyanci. Talle min baki dana sake yayi da yatsa yana harara ta yace" wato baki yarda da abinda na gaya miki ba ko?" Yace yana jefa min mugun kallo, b'ata fuska nayi ina shafa baki na dan ba karya naji zafi sosai. Bai bi ta kaina ba saima bud'e motan da yayi ya fita abin shi, shiri na saita natsuwa ta na bud'e murfin motan nabi bayan shi ganin yana son bace min, tun kamin mu karasa ma'aikatan gidan nasu suke ta durkusawa har kasa suna kawo mana gaisuwa amma maimakon ya tsaya ya amsa gaisuwan cikin mutunci sai dai kawai inga ya daga musu hannu ya wuce abinshi a zuciya ta nace wato shi ko ina yake sai ya nuna wannan girman kan nashi. Wata mata ce ta karaso gaba na cikin sauri zata karb'i basket din hannu na nace mata ta bar shi amma ta nace sai na bata,ni kuwa ganin zata kusan sa'a da Inna ta yasa naki sake mata, dago kan da zanyi naga ashe bai shiga ba ni yake jira wani mugun kallo ya watsa min mai kama da warning yasa na sake mata basket d'in babu shiri na karaso inda yake jira na. Hannayen mu ya tsarke waje d'aya sannan yayi sallama muka shiga cikin parlorn ,ashe abin kallon na ciki banga komai ba, ban san yanda zan kwatanta muku ba amma gidan yafi gaban had'uwa da kyar na shanye kauyanci na wannan karon na daina kalle-kalle na kalli gaba na, a can tsakiyan parlour Abba ne da Mom zaune kan wani lallausan rug sun saka warmers a gaba da alamu abinci suke shirin ci muka zo. Abba fuskar shi d'auke da fara'a ta musamman yake amsa sallaman yayin da Mom Kuma baka gane yanayin da take ciki gata nan dai fuskan nan nata ba yabo ba fallasa, sau d'aya kawai na dago daga nan ban kara gigin d'agawa ba saboda kunya duk ya gama lullub'e ni yanda muka shigo hannun mu sarke nayi ta kiciniyan kwacewa amma bai bani daman hakan ba. Kusa da Mom matan nan ta duka har kasa ta ajiye basket din sannan ta fice, sai da muka zo tsakiyan parlorn sannan ya sake min hannu ya karasa kusa da Abban shi ya zauna yana zuba musu shagwaba kaman karamin yaro suna biye mishi. Ni dai daga dan nesa dasu na tsugunna Kai na a kasa na fara gaishe su, cike da kulawa Abba ya amsa yana in karaso kusa Mom in zauna mana ya zan zauna a nesa sai kace wata bakuwa,cike da jin nauyin su na matso na zauna ina Kara gaishe ta ganin bata wani amsa min ba. Sama-sama ta amsa min tana kokarin fara serving din mijin ta amma sai ya dakatar da ita yana mai cewa " dakata mana da zuba abincin nan, ga surkuwar mu ta kawo mana kayan dad'i shi ya kamata muci yau ki maida naki gefe sai wata rana" ya karasa suna dariya shida Zafar ni dai murmushi kawai nayi na kasa dago da kai. Yake kawai Mum tayi tare da maida warmers din ta rufe zuciyar ta na kuna ta yaya zata kwashi lokaci tayi mishi girki amma wai dan yaga nawa yace ba zai ci ba, bata musa shi ba ta jawo basket din ta fara cire warmers da suke ciki , tana bud'ewa kuwa kamshi duk ya cika parlorn na girkin dana man shanu. Ranta duk babu dad'i haka ta zuba mishi abincin ta ajiye a gaban shi tana shirin rufe su yace mata " ya zaki rufe baki diba ba?" " Zan diba ba rufewa nake ba" ta bashi amsa

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99