Chapter 51
Chapter 51
su suka sakani a tsakiya suna hirar su anan naji cewa wai Gwaggo Aisha da taji labarin taron d'aurin auren ta yanki jiki ta fad'i yanzu haka tana asbiti ba lafiya. Har muka karasa gidan Zafar da ya amsa sunan shi gida ko ince Aljannar duniya dake can bolori lay out hawaye bai kara zubo min saboda mamakin halin Baban mu dana Gwaggo Aisha. A maidaicin compound din gidan da fitilu da flowers suka ma ado drivern yayi parking ,Aunty Fatima dake zaune a gefe na dama ita ta fara fita sannan ta kama hannu na tace in fito da kafar dama, hakan kuwa nayi na fito kaina a kasa dan rabin fuskata a rufe yake tana rike da hannu na har entrance din parlour nan ma cewa tayi inyi Bismillah sannan in shiga da kafar dama. Ni dai tafiya kawai nake ban san inda nake jefa kafa ta ba har naji mun shigo wani d'aki kuma naji an zaunar dani akan wani tattausan gado, sai a lokacin naji sabon kuka ya zo min na fara ina rike a jikin Aunty na, sauran yan rakiyan kuwa suka bazama duba gidan suna ta santi tare da yaba kayan d'aki da Inna ta min wanda ni ban san ma yaushe akayi su ba kasancewar naji Baba na cewa ba za'a min komai ba dan sun ce basa bukata komai daga gare mu. Allah sarki Inna ta na san tayi hakan ne dan samo min martaba da Kuma daga gare su, bamu fi minti talatin da zuwa ba naga sun fara shirin tafiya dinner nima kara shirya ni sukayi cikin wani Indian material mai dan karan tsada da kyau, net suka saka min a tsakiyan kai suka kama da pin ana ganin kitson da aka min na gaba sai suka saka min sarkan kai wanda yazo min har goshi sarkan set ne da dan kunne da sarkan wuya da warwaro masu bada sauti mai dad'i. Kamin su gama min duk sun tafi sai Maryam da wasu cousins dina 2 su suka tsaya Jira na da kuma Aunty Fatima har bakin wata arniyar mota da ko sunan ta ban sani ba suka rako ni tare da bud'e min kofa na shiga, ina jira inga ta shigo kaman dazu sai naga ta mayar da kofan ta rufe suka nufi wasu motoci guda 2 daya a gaban mu yake daya kuma a baya ya kasance sun saka mu a tsakiya. Har motan ya fara tafiya naji motsi a gefe na a firgice na juya dan a zato na Ni kad'ai ce a cikin motan sai ganin mutum nayi a kishind'e kaman wani basarake yana latsa waya ko kallon inda nake baiyi ba, ni kuwa kasa d'auke ido nayi a kansa ganin sa cikin arniyar suit ko dan ban tab'a ganin ya saka bane sai naga ya masifan yi mishi kyau, "Bana son kauyanci ki daina kallo na da wayan nan idanun naki" naji muryan shi ya katse ni. Cike da jin haushin kaina na murkud'a mishi baki nace " da wani idon kasan ana kallon ka..." Ko rufe baki na banyi ba naji ya dalle min baki da yatsan shi a take naji hawaye sun cika min ido dan ba karya naji zafi sosai, a zuciya ta naja masa Allah ya isa cikin kwando na cigaba da murza lebe na can dai na kasa hakura dan abin na cizo na a rai ace kullum shi yake ha'in ta na ni bana ramawa. Cike da tsiwa nima na bud'i baki zan rama naji mutumin da yake gaban motan yana ce mishi mun iso, bari yayiwa sauran magana su zo yace, kamin ma ya rufe baki su Sadeeq suka zagaye motan tare da bud'e mana, shi ya fara fitowa sannan ya zagaya ta bangare na ya kama hannu na ya fito dani yana wani murmushi kaman ba shine ya gama cin zalina yanzu ba. "Come on wifey walk gently" yace min cikin wani murya da ban san shi da ita ba, a zuciya ta nace lalle wannan ya cika dan drama toh bai sani ba gidan ta yazo. Cike da yanga da fari nima na amsa mishi da " yes husby". A dan zabure ya juya ya kalle ni na second 5 ya d'auke kai yana murmushi, tafiya cikin hall din muka fara su Maryam suna watsa mana wasu abubuwa masu kyalli gefe daya kuma turaren wuta Hamra take bin mu da shi a baya. Hannun mu sakale dana juna kaman masoyan gaske har muka karasa wajan zaman mu, tunda muka shigo mc ya saki wakan bikin da Ali jita ya rera mana mai taken Zareefa ta Zafar. Sai da kowa ya zauna aka natsu sannan Mc ya fara gabatar da event cikin burgewa da wayewa, da aka nemi abokin ango ya bada tarihin ango Sadeeq ne ya fito ya bayar sannan Maryam ta bada nawa,daga nan aka bukaci mu fito mu yanka 🍰 kaman ince ba zan fito ba amma sanin duk abinda ya wakana anan zai je kunnen Inna yasa na fito muka tsaya a gaban tangamamen cake wanda ya kusan tsayin mu after d count of 3 muka yanka a tare, cikin wani salo ya gutsuro cake din ya saka min a baki da gangan na had'a da yatsun shi 2 na dalla mishi cizo wanda har ya saka shi saurin janye hannun shi yana yarfewa. Dariya na tintsere dashi cikin tsananin farincikin nima na rama muguntan da yayi min, suma yan hall din dariya suke su a tunanin su wata salon soyayya ce haka. Ina kallon shi sai harara ta yake ta kasan ido yana jiran in bashi shima ya rama bai san cewa na gama gano shi ba. Maimakon in gutsuro cake din in bashi a baki sai lakato shi nayi a yatsana na shafa mishi a hanci nan ma dariyan yan hall din suka kwashe da shi ni kuwa ganin ya harzuka kaman ya shake ni yasa na juya da sauri zan bar wajan, har nayi step 2 naji anyi sama dani. Tafi da ihu sosai ne ya cika hall din wanda ya ankarar da Zafar inda muke yayi saurin ajiye ni dan idon shi ya rufe burin shi ya min muguntan da nan gaba in muka had'a hanya da kaina zan gudu, lakace min hanci yayi yana yaken da yafi kuka ciwo, ni kuwa harda yi mishi gwalo muka koma wajan zaman mu raina fari tass yayin da shi kuma yake jin kaman ya had'iye zuciya ta mutu saboda haushi. Ali jita shi ya baza basirar sa a wajan anyi rawa an cashe anyi barin nairori harda daloli , anci an sha sannan mun samu gift ba adadi zuwa 10 aka tashi kowa yayi inda ya fito, a mota daya muka dawo da kawaye na nayi musu karyan zai sallami abokan sa basu san guduwa nayi ba dan in na shiga mota daya dashi ban san kalan muguntan da zai min ba. Muna zuwa gidan Aunty Batool ta had'a min ruwan turare ta sani a gaba nayi wanka ta shirya ni cikin wani dogon riga na material pink ta min light make-up ta zaunar da ni akan gado bayan ta min barin humra kala kala a jikina ta lulluba min katon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99