Chapter 28
Chapter 28
a ce wai Hajara ke kare mu bayan a baya ta san yanda tafi kowa tsanan mu. Da washe gari da sassafe Gwaggo Aisha ta fita tasha dan tafiya Gwaza domin cika nufin su akan mu. ************************** A cikin wani tsadadden Hotel Zafar yayi parking motan na shi ba tare da ya cewa Sadiq ci kan ba ya kwashi wayoyin shi tare da bud'e murfin motan ya fita. Fitowa shima Sadiq d'in yayi suka nufi hall da ake partyn tun kamin ka shiga zaka ji cool music na tashi ga wajan ya matukar tsaruwa komai cikin tsari da aji akayi shi. Angon yana ganin su ya karaso da sauri ya tare su fuskar shi cike da farinciki, ricewa wajan yayi da hayaniyan zuwan nashi, ya d'an sake fuska kad'an yana amsa gaisuwan abokan shi bayan ya zauna a mazaunin shi. Hankali kwance aka fara party shima Zafar ya saki ran shi sosai akayi shagali dashi tsab'anin wasu parties da yake guduwa saboda 'yan mata masu takura mishi amma wannan har aka tashi yana nan dan babu mace ko d'aya . Yau tunda na tashi sai shirye-shiryen zuwan Yaya na nake saboda yau kwanan shi kusan 3 kenan baya gari yayi tafiyan nan nashi da na tsana dan yanzu sosai wannan tafiyan nashi yake bani haushi ko wani sati sai ya ciri tafiya har ta kai ina yawan fad'a mishi kan wallahi in munyi aure babu inda zai tafi ya barni kafa ta kafar shi ko kuma ya daina tafiyar gaba d'aya, dariya kawai zai min a duk lokacin da na fad'i haka baya ce min komai. Tun kamin sha biyu tayi na gama girkin da zanyi mishi harda su drinks na adana su na shiga wanka,ko da na fito azahar tayi,alwala nayi na tada sallah. Light makeup nayiwa fuska sannan na kama kalaba da Inna tayi min da ribon dan gashi na baya kitsuwa sam. Riga da skirt na wani material peach color na saka kayan sun zauna a jikina duk da ba wani matse ni suka yi ba,ban saka hijabi ba rolling kawai nayi da gyalen mai d'an fad'i sannan nabi jikina da turaruka kusan kala hud'u amma duk masu sanyi ne wanda sai ka zo kusa dani kamin kaji kamshin sa. Ina gama shiryawa kiran sa na shigowa cikin tsantsan farinciki da zumud'i na daga cikin tsigar shagwab'a da zallan so na ce" Yaya naaaaa" Ina jin shi ya sauke nannauyen ajiyan zuciya ya kasa magana sai can ya samu daman cewa " pls Baby ki fito mana in gan ki ko zan samu natsuwa I'm damn missing you " Dariya na kyakyale dashi tare da make kafad'a kaman yana gani na nace" ni fushi nake da kai dan haka ko gobe ba zaka ganni ba ina gama fad'a na kashe wayan gaba d'aya ina mishi dariyan muguta. Dariya shima yayi yana girgiza kai ya san fad'a kawai nayi ko baiga fuskata ba ya san na fishi zumud'i. Na share kusan minti 15 sannan na d'auki karamin basket dana shirya mishi abinci a ciki na fita, fuskata a d'aure tam na fito tsab'anin da, da nake fitowa daga gida kuma ko kad'an naki yarda mu had'a ido dashi. Ciki-ciki nayi mishi sallama ina kawar da kaina gefe ni a dole ina fushi, amsa sallaman yayi da murmushi akan fuskar shi yana leka fuskata, cikin tsigan tsokana yace"wannan duk fushin ni kad'ai akewa,ban san me zai biyo baya ba in nace miki gobe da safe zan koma wajan aiki." A wani dame na juyo ina kallon shi da ido duk a waje hannu na na dama kuma dafe da kirji na. Dariya ya kwashe da shi har yana rike ciki ganin yanda duk na rikice lokaci 1 yace "nima na rama munyi one-one kenan,ba ni kika shanya ba har na minti 15 ba". Kukan shagwaba na saka mishi har da bubbuga kafa a kasa rarrashi na ya fara tare da cewa inyi hakuri ya daina da kyar ya samu na daina kukan shagwaban na gabatar mishi da abincin da nayi mishi, asual yaci sosai har da santi kaman yanda ya saba yace yayi missing d'in abinci na. "Kaine kake ja mana lokaci da kaso da anyi komai ya wuce abinci kuma sai ka ture" nace ina hararrar shi ta kasan ido. Murmushi kawai yayi ba tare da ya tanka ba, ni dai kwana 2 nan wannan abin nashi yana damu na sai dai ban nuna mishi ba a duk lokacin da zanyi maganan auren mu ba zai tab'a ce min komai ba. Haka yau ma na daure zuciya ta mukayi hirar mu da zai tafi ya kwaso tsaraba ta harda na 1su Inna da Baban mu ya bani sannan mukayi sallama ya wuce. Karfe tara da kusan rabi sannan su Gwaggo Aisha suka d'auki hanyan Gwaza bayan sojoji sun tabbatar musu da hanya lafiya babu wani abin tsoro,shiru motan nasu kake ji tunda suka bar gari suka shigo cikin jeji kaman babu kowa a ciki sai karan engine motan, mafi yawan mutane dake ciki sai addu'an Allah ya sauke su lfy suke banda Gwaggo Aisha data rufe ido tana ayyana yanda zata taka kowa a gidan son ran ta sannan ta shimfid'a mulkin ta har yafi na baya. Kiiiiiiiii karan kama buriki da taji da karfin gaske shi yasa ta bud'e ido a firgice tana dube-dube, salati da taji 'yan motan suka fara yasa ta kalli gaban ta ba shiri. Kululuuuu taji cikin ta ya bada wani kara a take taji guduwa na son zubo mata hannaye duka 2 ta d'aura akai ta zunduma ihu tana " wayyoo Allah na shiga uku yau me zan gani haka ni shatu?" Mutane ne sun kai kusan su hamsin fuskar su a rufe kowanne d'auke da bindiga su tare gaban motan nasu sai muzurai suke. Kowa na cikin motan jikin shi sai karkarwa yake masu kuka nayi masu addu'a nayi Gwaggo Aisha kuwa sai ihu take zunduma musu iya karfin ta gaba d'aya ta fita hayyacin ta yau ga ita ga boko haram. A fusace wani daga cikin su ya d'aga AK47 din dake hannun shi ya fara harbin sama ba shiri kowa yayi tsit, Gwaggo Aisha ko harda sake fitsari saban rud'ewa da firgita da tayi. Su kaman 5 suka matso gaban motan suka bud'e kofan motan suka ce kowa ya fito kuma duk wanda ya musu wani rawan kai ko kuma taurin kai yanzu zasu aika shi barza'u. Tsimi-tsimi duk suka fito matan su da mazan su aka saka sukayi layi , su kuma sauka rabu kashi-kashi wasu suka tsaya nan dasu Gwaggo Aisha wasu kuma suka tafi taro sauran motoci masu wucewa. "Kowa ya kawo kudin da yake jikin shi da wayan ku gaba daya" cewar wani a cikin su gashi da babban murya kana jin hausan zaka san koya yayi. Layi sukayi suna jefa kud'add'e da wayoyin su a cikin wani katon kyale da suka shimfid'a a k'asa. Suna gama zuba duk abinda suka mallaka babban cikin su wato Amir din su yace musu saura suturan jikin su duk su ciro su kawo suma ba mata ba maza. Kallon kallo suka fara a tsakanin su dan basu fahimci me suke nufi ba. "Ku cire kayan ku duka ku
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99