Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

martanin murmushin. Ina ta jira inji ko zata min maganan auren amma naji tayi shiru sai jana take da hira tana bani labaran ban dariya, nima dan in kwantar mata da hankali yasa na saki raina nayi ta dariya amma can kasan raina cike ya tab da damuwa. Bayan sallah magarib sai ga Abban Zafar da tawagar sa a kofar gidan mu Kuma sun taki sa'a Baba yana nan bai tafi ko ina ba, Baba duk ya rikice ya susuce ganin manyan masu kud'in garin maiduguri a kofar gidan sa kuma da sunan sun zo had'a zuri'a dashi. Makotan mu biyu ya kira sannan ya kira Baban Dije wanda zance shi ya jagoranci komai ya hana Baban mu gudun kada ya kwafsa ko ya saki layi, hakan da yayi ya taimaka kuwa dan shi Abban Zafar tunda yaji ance Mallam ya zata Baban Mallamin ne da gaske. Wata 2 ciff aka saka na biki mu aka rabu cikin mutunci bayan sun sauke carton carton na minti da chewing gum da goro na rabawa yan uwa, Abba yaja Baba gefe ya bashi check na wasu kud'ad'e kan yayi hidimar biki da gida sannan ya d'aura da basa bukatan a kaini koda cokali guda d'aya su zasu tanada min komai su kawai surka suke bukata. Murna da Baba yake ji kaman ya daka tsalle amma ganin yanda Baban Dije ya kama kai yake musu magana shima hakan ya kwaikwaya har yayi mishi sallama ya shiga mota driver yaja suka tafi. Muna zaune sai gani mukayi anata shigowa da kwalaye kaman za'a bud'e shago, kowa kallon kayan yake tare da neman karin bayani sai dai babu mai bamu, sai da aka gama shigowa da kayan tass sannan Baba ya shigo yana jan banban rigan shi a kasa cikin d'aga murya ya fara magana yanda kowa na gidan zai ji. "Allahu yayi Allahu yayi!!! Ina kuke mutanen gidan nan kowa ya fito yaga abin arziki daya same mu, kayan saka rana ne na 'yar albarka, wata 2 kacal iyayen ango suka ce a saka dan suna bukatan ayi auren da wuri. Ba wayan nan kayan kawai ba har takardan karb'an kud'i na banki sirikin nata ya bani sannan yace basa bukatan mu kai ta koda cokali su zasuyi mata komai...." "Aaaaaaayyyyyyiiirrrrrrrr!!! Inna Asabe ce ta rangad'a wannan gud'a cikin farinciki tace" Masha Allah 'ya tayi goshi duk abubuwa daka lissafo duk na saka rana ne ina ga Allah ya nuna mana ranan auren ba magana....." "Aikin banza aikin wofi kowa yaga dama zaiyi ai tunda abin shige-shige ne" Gwaggo Aisha ta katse ta, Inna Asabe dai bata kula ta sai shewa suke da Allah ya sanya albarka suke da Mama Dije. Tashin hankali sosai na shiga da ganin kayan da muka maganan Baba duk da na san da zancen, kokarin dannewa nake saboda kada in karawa Inna tashin hankali amma na kasa daurewa,kuka na fashe dashi sosai har jikina yana rawa na shiga d'aki da gudu na fad'a kan gado ina mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro. . Jiki a sanyaye Inna ta biyo baya na ta zauna a gefena ta kura min ido itama idon ta na cikowa da hawaye amma ta hana su zubowa, tana rayawa a ranta inama zata iya dakatar da wannan auren da tuni ta dakatar da wanne zan ji cikin lokaci d'aya na had'u da jarrabawan rayuwa ga rad'ad'in rabuwa da Yaya na bai bar ni ba ace kuma ga auren da bamu san daga ina ya fito ba. Sai dai bata da zab'i dole ne ta karfafa min guiwa inyiwa mahaifina biyayya kaman yanda itama tayiwa nata mahaifin, gyara zama tayi tana gyaran murya sannan ta fara magana cikin rarrashi" wani lokacin kuka bashi ne waraka ba ga matsaloli na rayuwar mu ba,sai dai mu kanji sauki da rad'ad'in da zuciyoyin mu suka tsinci kan su a ciki dan haka ba zan hana ki kuka ba kiyi Zareefa kema ko zaki ji sauki. A al'adance da kuma addinin musulunci ya bawa mahaifi daman zab'awa 'yar shi miji daya ga ya dace da ita bi ma'ana ya yarda da addinin shi da kuma tarbiyan shi dan haka kada kiyiwa mahaifin ki mummunan fahimta domin ba zai tab'a Kai ki inda zaki wulakan ta ba kuma albarkacin biyayya da kikayi mana Allah zai saka miki da mafi alkhairi ko kuma da abinda baki tab'a zato ba balle tsammani. Abu d'aya da nake son ki tuna wannan auren ko dan Abdulbasit ya kamata ki rike shi da hannu bibbiyu saboda na san duk inda yake zai ji cewa za'a miki aure,kn ga kuwa kin nuna mishi zaki iha rayuwa ko babu shi sannan zai fahimci cewa kina da masoya ba shi kad'ai ne gare ki ba". Tun ina kuka kasa-kasa har na daina nayi shiru ina sauraron kalaman Inna, ya zanyi dole ne inyi biyayya in aure shi tunda ya biyo ta hannun Baba, baya ga haka in nace bana son shi waye nake dashi a yanzu, wanda na taso da son shi tun ban san kaina ba ya guje ni ya watsa min kasa a ido I don't have choice rather than accept this man domin na gama soyayya a rayuwata zuciya ta ta rufe kofa tayi ban kwana da soyayya harb abada. Sanyi sosai Inna taji a ranta na ganin kalamanta sunyi tasiri a kaina har na daina kukan sai ajiyan zuciya da nake akai-akai, matsowa nayi jikin ta sosai tare da d'aura kaina a kan cinyar ta na saka hannaye na duka biyu na rungumo kwankwason ta, itama tasa hannu ta dama tana shafa min gashin kaina na fara magana a hankali kaman mai rad'a. " Inna ku iyaye nane biyayya a gare ku ya zama wajibi a gare ni, kukan da kika ga inayi ba dan auren da Baba yace zai min bane kawai na tuna da Yaya nane" na karasa wasu sabbin hawayen na zubo min na tausayin kai na, na fad'i haka ne dan in kwantarwa Inna hankali ba wai da gaske ba. Cikin jin dad'in kalamai na Inna ta kara rungumo ni jikin ta tana shafa kaina tare saka min albarka da addu'oin gamawa da duniya lafiya. ****************** A kwana a tashi babu wuya a wajan Rabbi Izzati, mun cinye wata d'aya cikin watanni 2 da aka saka na bikina kuma gini da Baban mu yake yayi nisa sa dan har an gamawa Inna bangaren ta,2 bedroom da babban parlour sai kitchen da store sosai ginin yayi kyau, yanzu bangaren Inna Asabe da Gwaggo Aisha ake yi. Maryam ta dage sai rawan kai take akan bikin ni bata san haushi ma take bani ba, duk wasu frnds d'in mu na makaranta ta sanar dasu sai shirye-shiryen su suke ni dai na kawao na mujiya na zuba musu. A bangaren Zafar ma hakan take dan shi cewa yayi babu wani biki da zaayi sai ranan da zai auri love of his life sannan zasu sha bukukuwa ba biki bama. Sadiq ne yace bai isa ba dole ne su sha biki in ya tashi yin wancan yayi abinda ya ga dama, yaso yayi jayayya amma ganin yanda Abba da Mom suka dage suna shirye-shiryen auren yasa yaja bakin shi yayyi shiru tare

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99