Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ciki na kama kuka kaman rai na zai fita ji nake kaman rayuwa ta tazo karshe ji nake shikenan nayi ban kwana da farinciki a rayuwa ta ji nake kaman na yanki ticket na shiga kunci na har abada. Ban san iya adadin lokaci da na d'auka a bathroom d'in ba sai knocking da naji ana yi a kofan yasa na d'an tsagaita kukan tare da maida hankali na kan mai bugawan. "Zo ki bud'e kofan nan Zareefa" naji muryan Inna daga waje, goge hawaye na na shiga na nufi kofan na bud'e tare da komawa gefe kai na a kasa naki yarda mu had'a ido da ita, shigowa tayi ciki tana bin fuska ta da kallo. "Rufe kan ki kikayi kina kuka ko?" Ta tambaye ni still tana karantar yanayi na ta maida kofan ta rufe, maimakon in bata amsa fad'awa nayi jikinta ina mai kara rushewa da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro balle ita da take mahaifiya a gare ni. Rungume tayi itama tana kokuwa da nata hawayen dan kada su zubo da kyar tayi nasaran maida su sannan ta dago ni tana share min hawayen fuska ta tanayi wasu na kara zubowa. Murmushi d'auke a fuskata ta take kallo na sannan ta fara magana " toh menene abin kuka anan kuma uhum? Yakin matan kenan muma haka aka rabo mu da gidajen zuwa inda bamu saba kuma muka d'auki hakuri da juriya muka saba kema hakuri zaki yi wata rana sai labari. Aure bautan ubangiji ne a gare mu mata shine kuma mafi saukin hanyan shiga aljanna in min bi Allah kuma kika yiwa mijin ki biyayya kaman yanda Allah ya umarce da muyi toh tabbas zaki rabauta, miji a duk yanda kike tunani a musulunci ya wuce nan miji babban jigo ne a rayuwar 'ya mace tunda da zaran an kai mace d'akin mijin ta shikenan komai nata ya koma hannun shi ko iyayen ta basu da iko a kanta ko kad'an misali koda mutuwa akace nayi in yace ba zaki zo jana'iza ta ba dole ne kiyi hakuri ki zauna kiyiwa mijin ki biyayya...." A razane na dago jajayen ido na da kuka ya rina ina kallon ta ina son yin magana amma na kasa sai baki na da yake ta karkarwa. Gyad'a min Kai tayi tana mai cigaba da murmushin " irin wannan biyayyan ake son mace tayi a gidan mijin ta, nasan yanda kike ji na san abinda kike tunani amma ina mai baki shawara a matsayi na na mahaifiyar ki, ki cigaba da hakuri kiyiwa mahaifin ki biyayya insha Allah gaba ba mu ba ke da kan ki sai kinfi mu alfahari da wannan aure zan cigaba da yi muku addu'a insha Allah komai zai dai-dai ta . Yanzu kiyi wanka ki fito ga masu miki kwalliya suna jiran ki a d'aki" tana fad'an haka ta wuce ta fita ta ja min kofa bata tsaya a ko ina ba sai bathroom din ta,ta fashe da kukan da take ta dannewa tun d'azu " ya Allah ka taimake ta ka kare ta kada ta fuskaci irin rayuwar da nayi a cikin gida na ya Allah ka sanyawa rayuwar auren ta albarka". Haka ta cigaba da kukan ta tana sumbatu domin a kullum daurewa kawai take ace a aurar da 'yarka ga wanda baka san daga inda yake ba balle ayi bincike a san halin shi babban tashin hankalin ta shine bata da daman cewa komai akai saboda mahaifiyarta ta gargad'e ta tun farko, amma ba zata daina fad'awa Allah ba ya bani ribar biyayyan da nayi musu. Da kyar ta rarrashi kan ta ta daina kukan ta fito jin hayaniya na kara yawa alamun mutane suna karuwa kenan. Ko da ta fito sai ta aro jarumta ta daurawa wanda take dashi a baya ta cigaba gaggaisawa da yan uwa da abokan arziki amma taki yarda ta kalli gefen da Maa take balle su had'a ido ta fahinmci tayi kuka, sai dai bata sani ba ta makaro domin Maa ta riga da ta gane halin da take ciki, murmushi kawai tayi tana yaba jarumtar 'yar tata. Bayan fitan Inna daga bayin sabon babin kuka na bud'e inayi ina mai tausayin kaina ta yaya zan iya yin biyyan nan da Inna take Fadi ga wannan azzalumin? Da kyar na rarrashi kaina na daina kukan na fara wankan sanadiyan takura ni dasu Maryam suka yi. Koda na fito na kasa kallon kowa a d'akin sai kan stool na gaban mirror naja na zauna kai na a kasa ba dan komai ba sai dan bana son yawan magana, su kuma masu make-up suna ganin na fito suka iso dan yin aikin su, ban hana su ba kuma banyi musu gardama ba suka fara min sai dai yau light make up sukayi min amma duk da haka ba karamin kyau nayi ba, Maryam da jikin ta duk yayi sanyi ganin yanayi na ta d'auko musu trolley da aka saka kayan da zan saka yau da safe ta kawo musu. Su suka taimaka min na shirya cinkin wata expensive lace fari sol dashi yasha diamond stones, ni dai tunda nake a rayuwata ko labarin irin lace din ban tab'a ji ba balle gani, headtie na wani yadi mai sheki suka nad'a min shima fari ne sai set na dan kunne da sarka harda zoben shi na pure diamond suka saka min. Ba zan iya kwatanta muku yanda ni Zareefa nayi kyau a wannan rana ba just imagine it urself sai dai ko kad'an babu abinda ya burge ni a ciki in na tuna sabon rayuwan kunci da zan shiga ma sai inji kuka na neman kwace min. Kawaye na suma sun fito cikin wani hadadden atamfa da sukayi anko kowacce sai zuba kamshi da haske suke zubawa ana jiran su angwaye su karaso dan karfe goma sha d'aya ne daurin auren. A can gidan su Zafar suma haka suka tashi da shirye-shiryen gaske ba irin na jiya ba dan Baawa jiya bayan dawowar su daga gidan mu ta kai karan su Mom akan yaja musu kunne kada su zubar mishi da kima gidan surukai, aiko bata ji da dad'i ba wajan Abba dan sosai ya nuna mata b'acin ran shi sannan yaja mata kunne tayiwa 'yan uwanta magana kowacce ta kama kanta in ko ba zasu kama ba kofa a bud'e take duk su watse bayan son harkan k'ananan mutane, dole ta nuna tayi nadama a gaban shi da alkawarin babu wata b'araka da zata taso daga gare su sannan ya kyale ta ta koma ciki cike da tsana ta. Sadeeq shine yazo ya tada Zafar daga bacci dan har tara saura yana kwance yana bacci cikin kwanciyar hankali abin shi, ya shirya tsaf cikin hadaddiyar shaddar shi ash color sai kamshi yake zubawa kaman shine angon,Koda ya farkan ma fad'a sukayi tayi shida Sadeeq din kan me yasa zai tashe shi yana cikin baccin shi mai dad'i. Ganin yana son yaja hankali sauran abokanen su da suke parlour yasa shi yayi shiru yace toh yayi laifi kuma ya amsa ya tashi yayi wanka ya shirya ga Abba da sauran abokan su suna jiran shi su tafi wajan daurin auren. Jin ya ambaci sunan Abba yasa ya mike

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99