Chapter 39
Chapter 39
sirkata ta nemi wani abu kace mata babu" yace yana dariya. Shima dariyan yayi yana kara sadda Kai kasa. Cikin wani irin kwarin guiwa ya nufi part d'in iyayen nashi bayan yayi wanka ya sha gayun shi kaman kullum sai kamshin tsadaddaun turaruka yake, tsab'anin da in Abba yana gari da kyar yake iya zuwa saboda ya san in yaje ma ba zasu kwashe da dad'i ba. Da sallama ya shiga parlour amma babu kowa sai masu aiki da suke kai kawo, kowa na aikin da yake gaban shi, zama yayi kan d'aya daga cikin royal cussion d'in da suka lamushe kusan set 2 ya d'auki remote yana canza channel zuwa aljazeera sports yaji motsin saukowan su. Ajiye remote d'in yayi ya mike tsaye ya tarbe su basu tsaya anan ba direct dinning suka wuce kowa yaja kujera ya zauna banda Mom da sai da tayi serving din su sannan ta zauna suka fara cin abinci Basu dad'e da farawa ba Zafar yaga alert na zunzurutun kud'i har 10 million cikin tsananin murna bai san lokacin daya durkusa jiki na rawa har kasa ya fara godiya yana" Abba naga sako nagode Allah ya kara girma da nisan kwana" ba dan komai ba Abba yafi shekara rabon shi daya bashi kud'i sai dai Mom ce ke bashi a cewar shi ba zai bashi kudin shi yaje yana shashanci dasu ba. Abba kuma ya kalli Mom da take bin tilon d'an nata da kallon mamaki yace" da fatan kin fahimci abinda nake nuna miki kika kasa fahimta kinga tun kamin ayi auren ta fara canza mana shi ina ga Kuma anyi auren?" "Oh yanzu duk sun d'auka wannan village girl d'in ce ta canza ni..." Muryan Mom yaji tana cewa" na fahimta Alhaji ya tabbatar da alkhairi" "Ameen Ameen addu'an ki yake bukata dama, Kai kuma a yau d'in nan ka cewa 'yar Mallam gobe zamu je mu tsaida magana da Baban ta" Murmushi da bai shirya bane ya kwace mishi jin sunan da Abba ya kira ni dashi wai 'yar Mallam. "Ja'iri ji duk wannan washe bakin dan nace gobe zamu je ne, ina ga inda aka daura auren Kuma ya zakayi?" Dariya yayi kawai yana ficewa ya nufi part d'in shi yana kara dariyan sunan da kuma na Abban shi da yake ganin auren soyayya zaiyi bai san auren contract zaiyi ba. Direct bedroom d'in shi ya wuce yana cigaba da dariyan shi yayi dialing no Sadiq , saida ya gama ringing kamn zai katse sannan ya daga yana cewa " meye ya faru??" " Hey Ni ba fad'a yasa na kira ka ba, I just called dan in fad'a maka gobe Abba zai je nema min auren 'Yar Mallam" ya karasa yana dariyan da sai da yasa Sadiq ya cire wayan a kunnen shi ya kalli screen d'in ya kara tabbatarwa eh zafard'in ne sannan ya mayar kunnen shi. "Wacece da wannan sunan ko cikin relatives d'in ka na kauyen ne aka samo maka wata". Sadiq ya tambaya. "God for bid, bakin ka ya sari d'anyan kashi mugu kawai meya had'a ni da 'yar kauye, wannan village girl da kuka had'a ni da ita mana Abba ne ya saka mata wannan funny name d'in koda yake it suits her" ya karasa yana kara saka dariya dan d more zai fad'i sunan d more yake saka shi dariya. "Ikon Allah, amma ban san Kai cikakken d'an rainin wayo bane sai yau, yarinyan da ta sace maka zuciya at first sight shine zaka ce mu muka nemo maka ita?" "Damn it wai har sai yaushe zaka fahimta ni *BA SONTA NAKE BA* kuma kafi kowa sanin why I will marry her amma ba zaka daina fad'a min rubbish ba, anyway phone no ta nake nema in fad'a mata sakon Abba" yana kawo nan a zancen shi katse kiran yayi jifa da wayan kan gadon shima yabi shi ya kwanta ringine yana huci shi ala dole an b'ata mishi rai. Ko minti 5 baiyi da kwanciyar ba yaji karan shigowan sako wayan shi, sai da yaja tsaki sannan ya bude sakon ba dan komai ba sai dan yaga daga Sadiq ne. Number kad'ai ya gani babu rubutu hakan ya tabbatar mishi da number na daya nema ne ya turo mishi, sai da ya fara saving sannan ya kira ni lokacin muna zaune da Inna tana had'a min tea dan tace inzo mu karya nace bana jin yunwa, shine ta shiga had'a min wai ko shi kad'ai in sha. Inaji har tagama ringing ban d'auka ba ganin sabon no ce, kara kira yayi Inna ta dakata da had'a shayin tace min " Wai ke ba wayar ki ake kira bane?" "Inna sabon number ce babu suna" na amsa mata a sanyaye. "Ko ba suna ai zaki daga kiji ko waye ko?" Inna ta sake fad'a min. Koda na juya da niyan daukawa naji ya katse dan haka banyi magana ba nayi shiru Inna ma bata kara cewa komai ba ta cigaba da had'a min. Miko min tayi bayan ta gama harda 🍞 tace in gusura ko kad'an amma na ce mata sai anjima, sama-sama itama ta karya bata ci wani abu dayawa ba ta ture gefe duk gani na cikin rashin walwala yana hana ta sukuni itama. Gwaggo Aisha sai bayan fitan mu da kusan minti goma ta tashi ta zauna tana goge fuskan ta da hijabin da Hajara ta lullub'a mata ba hawayen amma duk ta jike da zufa. Harara ta zabgawa Hajara da take ta jera mata sannu tayi kana tace" ke dai Allah yayi magulmaciya da kinibibi in banda gulma waye yace ki gaiyato min wacan manufukar matan can da 'yarta fitinanniyan nan?" Baki a hangame hajara take kallon ta tace " haba Umma in baki gode musu ba ba zaki tsine musu ba, ihu fa kike tayi kina birgima kan an k'ona abinda kika binne dan su cutu ita da yarta amma matan nan ta zauna tana tofa miki addu'oi ita da yarta har kika samu lafiya, mutane nawa ne a gidan nan babu Wanda yazo kan ki sai su hatta Baba ma tafiyan shi yayi ya bar ki....." "Ki min shiru wawuya kawai mai fifita uwar wasu kan uwar ta koda yake ba laifin ki bane duk asirce ku tayi Kuma wallahi ba zan saduda ba sai na warware duka mugun kulli da tayi a cikin gidan harda Baban naku..." Shiru tayi tana wur-wurga ido kaman me neman wani abu, a zabure ta mike tana " kan bala'i in na yarda shigiya nake" tana gama magana ta fice fuuu zuwa tsakar gida. Cikin daga murya ta fara magana" ina kake ka fito shanyayye kawai wallahi na gaji da rashin adalci da kake nuna min a cikin gidan dole ne ayi abu d'aya ehe" "Ke Wai wace irin dakikiya ce mara hankali meya faru da zaki zo tsakar gida kinawa mutane ihu" cewar Abba kenan daya tsaya daga nesa yana kallon ta. "Eh dole ka kira ni da sunaye da kaga dama Amma kada ka manta ko rigar sakawa na kirki baka da ita lokacin da na aure ka sai yau dan ka samu abu zaka wukanta ni, ace Wai gini zakayi a gidan baka fara ta kaina ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99