Chapter 6
Chapter 6
tana matse kwalla tawuce ta shiga bayin, nafila tafarayi kafin tai sallan asubahi ta cire hijabin tabama Ihsan din tana matsawa gefe tana azkar, Ihsan ta karba tasaka takabbarta sallan itama. Tana cikin lazimi Anty Lami tabude kofa ta shigo, hada ido sukayi hakan yasa tai dan murmushi akunyace tace "ina kwana Anty Lami" hararanta tayi tace "dole kiyi murmushi tunda kin gudo nan kin kwana baki kwana cikin jama'a ba, itakuma wanan data biyoki duk kuka kwana anan kun kyauta ai, tunda kun tashi in kugama kufito mukarasa jeren komi" maida kofan tayi tarufe tafice. Ihsan na idar da sallan suka fita daga dakin, aiki suka farayi suna gyara gidan dan karfe hudu ne boat cruise party su, babban boat abokanan ango sukai hiring na Nire prest company, Zainab da kawayen Ayush din sai maganan party suke dan a arewa basu tabajin anyiba, sai wuraren one suka gama da sauri ta gudu dakinsu Ihsan ma tabiyota salla sukayi Ihsan ta debo musu abinci suka ci dan bataso takara fita dan gidan yacika da baki matan abokanayen shi ga makeup artist din da aka dauko dazata musu makeup suna gamaci tahau gado Ihsan tabi bayanta sai bacci. Wuraren uku na rana Anty Lami ta shigo dakin taci gayu cikin wani hadadden lace baki daja dayay mata kyau sosai, baki tabude tana kallonsu yanda suke bacci abinsu kafin ta karaso wajen gadon ta daka musu duka a firgice dukansu suka tashi bayi ta nuna musu cikin fushi tace "tashi kije kiyo wanka right dis minute kisa ashobin ki ki fito amiki makeup, ke Ihsan tafi bathroom din dayan dakin kiyi wanka" da sauri Ihsan ta sauka daga gadon ta wuce dan bataso tai missing party nan for anything bata taba ganin party da akeyi a jirgin ruwaba ba kuma akan ruwa ba, kallon Hamida tayi dake sosa ido tace "wuce kema" ahankali kaman zatai kuka tace "Anty Lami ni bazani ba zan zauna gida tareda ke" cikin tsananin fushi Anty Lami ta nunata da yatsa tace "koki tashi kije kiyo wanka yanzun nan kiyi la'asar kije amiki makeup ki shirya kutafi ko wlh na saba miki Hamida, yanzu nafara yarda da maganan mamanki iskancin ki is too much stand up and get out of my sight my friend" da sauri ta tashi sabida tsawan data daka mata, bayi ta shiga tayo wankan tadauro alwala Anty Lami tagani a zaune ga trolley ta ta shigo mata dashi ahankali ta tsugunna tadau hijabin ta tasaka tai la'asar tana idarwa Anty Lami ta nuna mata sea blue ashobi ta wanda shine theme din party anmata wani hadadden gown, daukan rigan tayi tasaka Anty Lami ta tasata agaba takaita falo inda mata kenan dayawa anata makeup sunnar dakai tayi Anty Lami tasa aka fara mata, raurau tai da ido zatai kuka da kyar ta iya hadiye hawayen har aka gama mata makeup din, duka matan falon kafeta da ido sukayi sabida wani irin shegen kyau da tayi kaman ita tai kanta, hadadden takalmi Anty Lami tabata navy blue tasaka tabata glasses dinta tasa bakaramin kyau tayiba yanda ake kallonta yasa jikinta yafara rawa, horn da aka fara musu ana cewa su fito dan abokan ango tun uku da rabi suka taho yasa ta mike da sauri zata tafi daki hanunta Anty Lami tarike tana hararanta tace "wuce dan ubanki saikinje wlh, Zainab" ta kwalama Zainab dake kokarin sa hill dinta taci gayu sosai kaman itane amaryan kira, da sauri takarasa sa takalmin taje inda Anty Lami take tace "gani Anty Lami" murmushi Anty Lami tamata sabida kyan datayi tace "samomin gyale ta yafa dan bazata saka hijabin nanba yau" fashewa da kuka tayi jin ance bazata sa hijabi ba, bakaramin kular da Anty Lami abin yayiba tace "wai ke lamarin nan naki baza'a kaiki asibiti ba kuwa?" tabe baki Zainab tayi tace "Anty Lami wlh haka take ni dama kinbarta ta zauna a gidan inba hakaba wlh kuka zataje tana mana tana sunnar dakai tana neman inda zata labe saikace barauniyar datai sata a kasuwa, yar kauye kawai" hararanta Anty Lami tayi tace "kekuma dena cemata yar kauye wuce ki samo gyalen danace" ta kalli Hamida dake share hawayen cikin muryan lallashi tace "haba Hamida na, mai kama da mamanta, kinga kyan da kikayi kuwa? Bama wanan ba bakiso kije kiga jirgin ruwa yau, kintaba ganin jirgin ruwane ai saidai a tv a film irinsu tatanic, amma yauko zaki shiga cikin jirgin ruwa akan ruwa za'ayi party jirgi na tafiya, dena kuka kinji kije abinki inkin dawo kibani labarin abinda yafaru, kinga karma kibata kwalliyan ki" tai maganan tana share mata hawayen datakeyi daidai lokacin Zainab tafito dawani hadadden navy blue gyale ta warware ta yafa mata a one side aiko tai masifar kyau, murmushi Anty Lami tayi tace "iyye Allah nagode ma wanan kyau irin na yarana haka muje na rakaku wajen" rike hanunta tayi suka fita har wajen tasasu a mota Hamida kaman zatai ihu sabida tashin hankali gabanta har faduwa yake tsabagen tsorata sai sunnar dakai take tana kare fuskarta da gyalen jikin nata, daga musu hannu Anty Lami tayi tana dariya dan abin Hamidan ma looks funny dan yanzu yaga maganan zainab datace tana abu kaman barauniyar datai sata akasuwa. Tashi motar tayi itakuma ta koma cikin gida tana girgiza kai tace "Hamida, Hamida hmmm Allah dai ya kyauta". Gabaki daya she's not comfortable, gashi sai tafiya suke kaman bazasu kaiba chan lekki sukaje sukai parking a parking lot na Nire prest Boat activities, suka fiffito kafin su karasa waterfront din dukansu suna kallon katoton baban Boat din da akai decorating da flowers seablue, ga mutane maza damata suna kida na tashi, karasawa sukayi suka shiga kirjinta wani irin bugawa yake kaman zai tsage da sauri tarike hanun Zainab hakan yasa zainab ta kalleta daidai lokacin dayake duk angama shiga jirgin yafara gudu a ruwan, da sauri ta rike Zainab gam bakinta har rawa yake tace "An..Anty Zainab wlh am scared, please banaso wanan katon jirgin I don't like water" hararanta Zainab tasake yi dan sosai take jin haushin halin Hamida tace "aisai kiyi tsalle kifada ruwan, look back kiga yanda mukai nisa da wurin da muka bari yanzun nan, jirgi tafiya yake, idan kuma you can swim back there bismilla" girgiza mata kai tayi hawaye zai zubo mata tace "to please hide me kinji, am shy and am feeling somehow, mutane sunyi yawa" tsaki Zainab tayi kafin tajata by fire by force sukai sama jirgin asalin party floor din, ihu Zainab tayi ganin wurin yanda yahadu taciro wayarta zatai selfie tace "Omg this is paradise" Ihsan ma ihu tayi tana tsalle karasawa inda akai arranging kujeru sukayi kida natashi yan mata suka fara rawa, janta Zainab tayi tace "dalla chan zomuyi rawa yar kauye kawai karki kofsani" fizge hanunta tayi da karfi dan sosai kanta yafara juyawa yanda taga mutane dayawa awurin ga karan kida dake tashi ga duman music dahar kwanyanta takeji suna wani irin cika mata kunne kunenta yay wani dumm, duk inda ta juya saita hada ido dawani ko wata ana kallonta, cikin tsananin tashin hankali ta iya bude baki bama tagani da kyau tace "Anty Zainab" sosai idanunta suka fara juyawa hakan yasa ta daura hannayenta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128