Skip to content

Chapter 45

Chapter 45

In Bani Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

da saurayi ko daya, shiru tayi tadan tabe baki dam bataso tasaka lamarin Hamida arranta da sassafen nan dan zata tashi da ciwon kaine abanza ta maida kofar ta rufe tai dakin yaranta maza danta tasosu subi Abban su masallaci. Baki kawai ta wanke tafito daga bayin ahankali danji tayi cikinta namata ciwo sosai, drawer Anty Lami taja nanko taci karo da pad, guda daya ta dauka takoma bayi wanka tayo ta shirya tsaf sanan ta dauro alwala tafito daga bayin, adaddafe ta shafa mai tasa riga tahau gado ta kwanta dan sosai taji zazzabi na neman kadata, wajejen 7 Anty Lami takara shigowa dakin ganinta dukunkune kan gado yasa ta maida kofar ta rufe takaraso ciki da sauri dantasan Hamida bata komawa baccin asuba saitai karatun Al Qur'ani, ahankali ta yaye bargo data rufa dashi hakan yasa Hamida tabude jajayen idanunta ta kalli Anty Lami dake wani irin kallonta, ahankali tace "ina kwana Anty" dasauri Anty Lami takai hanunta kan wuyanta ganin yanda take maganan arude ta janye hanunta daga kan wuyanta tace "bakida lafiya Hamida, meke miki ciwo?" dan yamutse fuska tayi tace "cikina ke ciwo" da sauri Anty tace "kin fara kenan kinga pad a drawer na?" gyada mata kai tayi tana goge hawayen dasuka zubomata na wahala, maida bargon tayi ta lullubeta tace "sannu kinji bari nakarasa breakfast nakawo miki kici kisha magani anjima idan ya lafa saimu je gida" gyada mata kai tayi hakan yasa Anty lami ta shafa fuskarta tawuce tafita daga dakin. Fashewa tayi da kuka sosai tarasa meke damunta deep down jitaje kawai so take taga Aadil, she miss his innocence dakomi ma nashi, ko hanunta ta daga saita dingajin kamshin shi, hakanan ma saita dingajin kamshin shi kaman yana wurin, gashi batada waya balle yadan rage mata kewa kokuma wani abun, kasa dena kukan tayi har Anty Lami tadawo dakin da sauri ta share hawayen fuskarta gudun karta gani tafara mata masifa, karasowa ciki tayi rike da tray tana kallon fuskarta tace "kuka kike ko? Kodai muje asibiti ne" girgiza mata kai tayi ahankali, ajiyen abincin tayi akan rug tayaye bargon jikinta ta miko hannu ta dagata ta sauko da ita tace "ga kunun nan kisha da chips kisha magani saiki kwanta wuraren shadaya zamu je gidan, yanzun nan ma muka gama waya da maman ki" kallonta tayi ahankali tace "Mama" "eh maman ki tace nagaishe ki" murmushi tayi tadau kopin kunun takai baki hakan yasa Anty Lami tai murmushi tawuce tafita ta shiga kitchen ta kwaso lunch box din yaranta ta mimmika musu tace "kuje ku gaishe da Antyn ku saiku tafi driver na jiranku" da sauri sukai dakin Hamidan fadawa jikinta sukayi ta washe baki sosai dan tanason yara ta shafa kansu tace "byee ayi karatu da kyau" da gudu suka fita ta cigaba da shan kokon taci chips din kadan sanan ta tatatara ta kwashe tafita daga dakin ta shiga kitchen ta wanke duka kwanukan data gani a wurin ta share kitchen din tsaf konina na kyalli. kwala mata kira akayi. "Hamida jeki shirya Abban ku zai tafi aiki yanzu" ahankali tace "to" ta dauraye hanunta a sink tawuce tafita daga dakin ta shiga dakin Anty Lami kayan data gani anty Lami ta ijiye mata akan gado ta shirya acikin su bakin gown ne mai kyau tadau hijabin tasaka daidai nan Anty Lami tashigo dakin tace "iyye mai kama da mamanta kinyi kyau, mutafi to" murmushi tayi ta sunnar dakai tana wasa da yatsunta ta, tabi bayan Anty Lami suka fita tsakar gida motan Abban ta shiga bayan sun gaisa yatada motar suka shiga hanya dashi da Anty Lami sai hira suke gwanin ban sha'awa har jan bulo, ganin kofar gidansu yasa gabanta yawani irin fadi, akofar gidansu Abba yay parking suka fiffito daga motar, Anty Lami takama hanunta ganin takasa shiga jikinta sai wani rawa yake suka shiga cikin gidan, Abban su Ra'is biye dasu, agaban falon su Anty Lami ta kwada sallama ta shiga Abba da Mama dake zaune kan kujera ne suka amsa su Zainab da Ihsan kuma nakan dining suna gyaran wake a tray, Tashi Mama tayi tai murmushi jin muryan Anty Lami tace "shigo Yaya" shigowa Anty Lami tayi Hamida biye da ita abaya kanta akasa, ta kalli Abba dayawani irin kafe Hamidan da manyan idanu tace "ina kwana Abban su Ayush" dan murmushi yayi yace "barka da zuwa ga wuri" kokarin zama tayi tana mikama Mama jakarta tace "tareda Abban su Ra'is muke yana tsakar gida" da sauri Abba yamike tsaye yace "la shine kika barshi waje" yafita dan shigo dashi, wani irin kallonta Mama tayi yanda kanta ke kasa takasa dago kai sai wasa take da yatsunta yasa Mama buga uban tagumi, da gudu Ihsan ta sauko daga dining tazo tafada jikinta tace "oyoyo Anty Hamida naaa" Zainab kuma ta balla mata harara tacigaba da gyaran wakenta dan lamarin Hamida yanzu haushi yake bata, Sallaman su Abba yasa Ihsan tasaketa tai dining Anty Lami ta nuna mata gefen ta hakan yasa taje ahankali ta zauna akasa kusada kafarta, Abba kuma ya shigo tareda Abban Ra'is Mama kuma tadawo gefen yar uwan ta ta zauna, su Ihsan suka taso suka gaishesu ya amsa cikin fara'a Zainab tawuce kitchen tafito da tray da drinks ke ciki da snacks takawo ta ijiye sanan tadau tray din tawuce itada Ihsan suka wuce dakinsu. Ruwa kawai Abban su Ra'is ya dauka yasha sanan ya ijiye ya fuskanci Abba da kyau zaiyi magana saikuma yajuyo ya kalli Hamida dake zaune akasa kusada matarshi kanta akasa gabanta sai wani irin faduwa yake yace "tashi kiwuce ciki Hamida, tafi dakinku" ahankali ta gyada kai tana goge kwalla tawuce ciki Abba yabita dawani irin kallo harta shige corridor, sake kallon Abba yayi sanan ya kalli Mama dake dan murmushi cikin tattausan murya yace "haba, haba, haba dan Allah, a gaskiya raina yay matukar baci saisa nazo har gida namuku fada sanan nadawo da Hamida, ko kadan bakuma yarku adalci ba wlh, kuma nan gaba karku kara yankema yara mata irin hukuncin nan dan irinshi ne ke jafa yaro ga halaka, karuwai da sauran su dakuke gani duddaga haka aka fara daga koransu daga gida ne, to ina amfanin wanan? kome yaro yayi afara bashi damar bayani tukunna kafin a yanke hukunci, sanan adena yankema yaro hukunci cikin fushi, hanunka ai baya rubewa ka yanke ka yar, kai yanzu idan ka kalli Hamida fisabillahi bata baka tausayi?" yay maganan yana karkada kafa yana kallon Abba dake kallonshi asanyaye sanan ya cigaba."yarinyar nan ta shiga duk bala'in data shigane daga taimako, taimako fa jama'a, taimakon da annabin mu shiyace muyita, jiya har gida iyayen yaron nan sukazo suka mana godiya wlh idan kaji labarin yaron ma saika zubda mai da hawaye abin tausayi......" nan yafara bama Abba labarin da Hamida ta bayar na yanda ta taimakai dana Mami data bayar na Aadil din, dakuma labarin rashin lafiyan shi, sanan yace "yanxu abinda kukayi kun mata adalci?" dan ajiyan zuciya Abba ya sauke yace "nima nasan bamu kyauta ba kuma tun jiyan hankalina yaki kwanciya, naba Kaka hakuri, nabata hakuri harna gaji da bata hakurin amma taki fahimta ta tsaya akan bakanta, abinda yakara batamin rai shine yanda bata attending lectures ko kadan

Table of Contents

Chapters

128 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128