Chapter 4
Chapter 4
zama Hamida, bari zaki gani, kina dawowa daga legas dinan yinaki yinaki zaki tattaro ki dawo nan sasa na dazama ja'iran yarinya kawai, ga furanki chan a fridge inkin ga dama ki dauko kisha" tashi tayi ahankali tai hanyar fridge din ta dauko furan tadawo ta zauna tafara sha, kasama sha tayi sosai sabida yanda Kaka keta jifanta da mugun kallo kaman zata kasheta, ahankali ta ijiye cup din ta mike tsaye, hararanta tasake yi tace "ina zaki? Baki barin sasan nan harsai anshigo da Ayush namata fada sanan zan rike ki da kaina na tura ki a mota, ja'irar yarinya marason mutane, saisa haryau batada mashinshini ko daya, duk yayyinki sunyi aure ga Ayush nan itama tayi, ga Zainaba samarinta har kadasu nake tsabagen yawansu kullum dai kina ganin dakin nan nawa da yar bakan leda samarin su suke shigowa dashi, keko mai bakin jini ko mashinshini kwara daya baki dashi balle nasaran koyar dubu biyu wataran nasamu tasanadin ki, Hamida, Hamida wlh ki chanza hali inba hakaba zaki tsofe a gida ko mahaukaci bazaice yanayi ba balle namiji cikakke mai mutunci, macen dabata shiga jama'a ina zata taba samin mashinshini iyye?" tai maganan tana buga cinya, hawaye ta share tana turo baki tace "salla zanyi" mugun kallo tasake watsa mata tace "wuce ai kinsan hanyar pampon jekiyo alwalan kizo kiyi sallan bance kihadani da Allah ba" juyawa tayi tafita daga dakin ahankali tsugunnawa tayi gaban pampoo ta daura kai akan cinya tana kuka mara sauti tayi minti uku ahaka sanan ta dago kai tashare hancinta dayay jajir, ahankali tabude pampoo tafara alwala tana gamawa ta tashi ta shiga dakin, hanyar uwardakan Kaka tayi Kaka ta nuna mata dadduman dake kan kujera tace "dauko wanan kiyi sallan akanshi bazaki shigan min dakiba" komawa tayi tadau dadduman ta shimfida anan tsakar falon tahau kai tai sallan la'asar, bayan ta idar ta linke dadduman ta ijiye akan kujeran ta zauna akasa ta tankwashe kafa Kaka kuma na ballan namijin goro tanaci abinta, sallaman Mama yasa ta dago kai da sauri ta kalleta, shigowa Mama tayi dakin dauke da karamin trolley da handbag dinta ko inda take batayiba ta ajiye ta kalli Kaka dake kallonta tace "Umma ga kayan nan nata" washe baki Kaka tayi tace "yauwa Haleematu kokefa, kinga inmuna mata hakan kotanaso kobataso zata dena tsoro da shegen jin kunyan nan, haka zamu dinga chusata cikin mutane dan gaskiya bazan bari tamin kwantai agidaba sonake ayi bikinta tareda Zainaba, amma in kullum tana makale damu, makale a dakinsu bata shiga mutane tayaya zatai mashinshini, daga saman silin din dakinsu Allah zai jeho mata miji? Kidinga sata a jama'a Haleematu kinji" gyadamata kai kawai Mama tayi kaman ba Kakan data mata tatas bane dazuba tace "to Umma in sha Allah zan dinga sata, antashi tafiya yanzu za'a kawo Ayush wurinki kimata fada" sake washe baki tayi tace "to, to shikenan ai, a shirye nake dama dazu rashin ganin miskilan nanne ya konamin rai" juyawa Mama tayi zata fice Hamida takara binta da kallo idanunta sunyi raurau dan ta tsani taga Mama na fushi da ita, dan juyowa Mama tayi suka hada ido watsa mata mugun kallo tayi tasakai tafice daga dakin, nuna mata jakan Kaka tayi tace "zoki kwashesu daganan yanzu za'a kawomin amarya" tashi tayi ahankali tazo taja jakan takomar dasu gefe, matane dayawa suka shigo sasan ana waka ana guda ansaka amaryan datasha alkyabba a tsakiya aka shigo bangaren Kaka da ita, wata kawar Mama tace "kaka ankawo jika kimata fada kisamata albarka" fashewa da kuka Kaka tayi tana soka hannu a lalita tace "Ayush yarinyar arziki, yarinyar kirki ga kwakwalwa wlh ba irin wasu ba kullum nabayan kashi sukeyi a makaranta, Allah ubangiji ya baku zaman lpy da mai gidan ki Muhammadu yaron kirki, Allah yabaku zaman lpy kinji Ayush" kudi taciro yan dubu daidai har dubu ishirin ta kamo hanun Ayush tasaka tace "gashi kina zuwa chan legas din ko albasa ce ki saro kifara saidawa kinji" kashewa akai da dariya awajen sosai danhar Hamida data cusa fuskarta a hijabi saida tai murmushi, hararan su Kaka tayi tace "karki biyema rubabbun nan Ayush dake dariya, aure saida sana'a inka cika tambayan miji bani bani bani gajiya suke afarama wulakanci, zamanin mu babu abinda ban sayar ba, daddawa, kuka, wata tsiya wata tsiyace dukna siyar, Allah miki albarka kinji Ayush dita" gyadamata kai Ayush dake kuka sosai tayi, Kaka tace "to kutashi kutafi karkuyi lattin jirgin saman dazakubi" ta juya ta kalli Hamida data makale jikin kujera tana kare fuska da hijabi tace "tashi kidau jakan ki muje dakaina nan zan saki a mota" fashewa tai da kuka sosai kaman za'a yankata, Zainab taja tsaki tafice daga falon abinta, ta alkyabba Ayush da ake fitarwa waje ke kallon yanda Hamidan ke kuka rabon data sata a ido tun jiya dasafe, tsawa Kaka tamata ganin batada niyyan tashi tace "tashi nace kona kira ubanki nafadamai wlh" da sauri ta mike tsaye, hararanta Kaka tasakeyi tace "ina abin idanunki?" ahankali ta nuna mata handbag dinta, dauka tayi ta mika mata ciro glasses din tayi tasaka kaka tace "dau akwatin mutai" jan akwatin tayi Kaka takama dayan hanunta tajata suka fita daga dakin sukai waje sai sunnar dakai take jikinta narawa sosai ko kadan bataso tai tafiyan nan, har wajen motocin daukan amaryan Kaka ta kaita inda har anma saka amaryan, ihu tayi tana leka jeep din wanda daga Ayush amarya sai Anty Lami dawata kawar Ayush Amina, dawata kawar Mama sai Zainab, da Ihsan da hannu Kaka ta nuna Zainab tace "Zainaba ke da Ihsan ku fito kushiga dayan motan wanan ja'iran nakeso nasa anan dan asaka mata ido ga Lami nan inba hakaba zata iya guduwa tace bazata ba, ku fito nace" tai maganan tana hararan su tana kama kugu, fitowa Zainab da Ihsan sukayi sukai motar gaban su suka shige, Kaka ta kalleta yanda taketa share fuska da hijabi tace "wuce ciki yar tselen uwa" ahankali ta shiga ciki Kaka ta karbi akwatin datake shirin shiga dashi tace "wanan a boot za'a saka" Abokin angon dake sanye da Navy uniform ne ya karbi akwatin daga hanun Kaka ya bude boot ya saka, aka shishiga motar aka tada Kaka ta daga musu hannu, saida taga tafiyar su sanan takoma cikin gida tana murmushi ranta fess. Sosai take share hawaye a mota hanunta har rawa suke, ahankali Ayush dake zaune kusada ita ta mika hanunta ta daura kan nata ta rike, da sauri ta dago rinanun idanunta ta kalli Ayush din hada ido sukayi itama idanunta sunyi ja ta girgiza mata kai, da baki tamata alamun "stop crying" hakan yasa ta share hawayen ta damke hanunta gamgam ahaka harsukakai airport suka fiffito daga motan kanta akasa ta rike Ayush gam har suka shiga jirgi jirginsu yadaga jitake kaman zata kurma ihu. _Lagos_ Misalin 7:25 jirginsu ya sauka a Lagos, wasu manya manyan hadadun cars ne sukazo dukansu har lokacin tana rike da hanun Ayush kanta akasa kaman zatai ihu, suka shiga mota, abokanan ango suka kaisu gidan Ayush dake cikin Navy Barrack, gidane mai kyau hadadden gaske, sai alokacin hankalinta ya kwanta ta natsu ganin su kadaine agidan, barin musu dakin da aka aje Ayush din tayi tafito ahankali tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128