Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

In Bani Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta shigo dakin wayansu masu aikin gidan biye da ita guda biyu suna dauke da tray a hannu, nuna masu gabanta Mami tayi tace "ku ajiye anan" ajiyewa sukayi suka wuce suka fita daga dakin sukamaida kofa suka rufe, ahankali Mami ta zauna a gefenta taidan murmushi ta kalli fuskar nata tace "twins ne wanan ne babba shine Hassan" ta nuna Aadil dake bacci tadan shafa kanshi tai shiru jin jikinshi da zafi, ahankali ta janye hanun tace "dayan kuma shine Aabid, dukansu haka sukeda zuciya barin ma wanan" ta nuna Aadil tace "yauma bansan meya faruba, dan Aabid dawuya kiga fushin shi, inata miki surutu ko baki fadamin ba ya sunanki?" ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun ta dan hakanan taji tanajin kunyan matan tace "Hamida" ahankali Mami tace "suna mai dadi amma asalin sunanki kenan?" girgiza mata kai tayi tace "sunana Amatullah" "masha Allah wat a nice name, wani mataki kike a karatu?" wasa ta shigayi da yatsunta tace "100 level Islamic studies" "masha Allah, oya ci abinci karya huce kinji daughter na" gyada mata kai tayi ta kalli uban tilin abincin tarasa mema zataci da kyar ta mika hannu tadau spoon ta dau plate hanunta na rawa takasa diba, ganin haka yasa Mami ta karba tace "kawo nai serving dinki tunda kunyana kikeji" zuba mata white rice din Mami tayi a plate tazuba pepper soup din asama ta mika mata ahankali ta karba tace "Allah amfana" murmushi Mami tayi dan taji dadin addu'an tace "Ameen Amatullahi" diban abincin tayi tai Bismillah takai baki duk Mami na kallonta tana yaba natsuwan yarinyar da kyar ta iya tai 5 spoon sanan ta ijiye ta dau ruwa tasha batare data taba juice din wurinba tace "nakoshi nagode zan tafi" "kai dan Allah daughter bakici dayawa ba" girgiza mata kai tayi tace "nakoshi" gyadamata kai Mami tayi tace "Tom ina zuwa bari nazo saimuje mu saukeki daganan mayima iyaynki godiya" gyadamata kai tayi gabanta na faduwa, fita Mami tayi daga dakin ba jimawa yan aiki suka shigo suka kwashe kayan abincin, juyawa tayi tasake kallon Aadil dake bacci hakanan taji bataso ta tafi ta barshi tasan idan yatashi saiya nemeta, kafeshi tayi da ido tana kallonshi daidai lokacin Mami tabude dakin da sallama ta shigo kallon Mami tayi, Mami takarso ta mika mata wani hadadden black gyale tace "gashi ki yafa" karba tayi kanta akasa tace "nagode Mum" murmushi Mami tayi batare datace komiba, ahankali tamike tsaye ta yafa gyalen kaman yanda taga su Zainab nayi sosai gyalen yamata kyau Mami tace "masha Allah yako miki kyau, muje" gyadama Mami kai tayi Mami tai gaba tana binta abaya harsunkai bakin kofa takasa daurewa saida tajuyo ta kalli Aadil din dake bacci sosai da sauri ta goge hawayen dake neman zubo mata tasakai tafice tarufo kofan ahankali suka fito tsakar gida sai sunnar dakai take Mami ta bude mata bayan mota ta shiga ta zauna Mami ta zauna agaba Abie yatada motar yaja sukabar gidan, sosai gabanta ke faduwa itato ina zata kaisu yanke shawara tayi gidan Anty Lami haka tadinga nuna musu hanya har zuwa gidan Anty Lami dake ta wuraren gwamna road har zuwa kofar gidansu suka sauko daidai lokacin ana kiran sallan magrib fitowa sukayi daga motan Abie yarufe motan ya kalli Mami yace "ku shiga ciki bari in shiga masallaci" ya mikama Mami key dan akwai abubuwa acikin boot din, yanda ta tsaya gefen Mami kanta akasa tana wasa da yatsunta yasa Mami tace "muje daughter" gyada mata kai tayi tabude kofar gate din ahankali ta shiga Mami biye da ita. Babu kowa a hadadden tsakar gidan sai tulin textbooks dake kan wani table da alamu yaran homework suke sun tafi masallaci, sallama tayi ahankali tabude falon ta shiga babu kowa ciki ta kalli Mami dake tsaye tana kallonta tace "ki shigo Mum" gyadamata kai Mum tayi tai sallama ta shiga ta zauna akan kujera hakan yasa tai ciki da sauri sallama tayi agaban dakin Anty Lami daidai lokacin anty Lami na sallame salla ta juyo da sauri ta ware ido tana kallonta daga sama har kasa takama haba cikeda mamaki tace "Hamida!" kasa amsawa Hamida tayi saima kasa datai da kanta tana wasa da yatsunta, cikin mugun takaici Anty Lami ta tashi daga kan dadduman tana gyara daurin zanin jikinta tace "ba magana nake mikiba kinyi shiru tun safe mahaifiyar ki ke kirana taji kokinzo nan bakizo ba Hamida, ina kikaje kodai mazan kika farabi da gaske? Ina kikaje Hamida" girgiza matakai tayi ahankali tasa bakin gyalenta ta share hawayen dasuka zubomata, tsayawa kallonta Anty Lami tayi ta rungume hanunta akan ciki cike da mamakinta tace "hala namiki wani abune dakike min kuka?" girgiza mata kai tayi ahankali. "to menene?" cikin muryan kuka tana goge ido tace "ana nemanki a falo" zaro ido Anty Lami tayi tace "wakika kawomin gida?" tai maganan tana zuwa hanyar falo da sauri ta yaye curtain ganin kamilalliyar mace cikin shiga ta alfarma zaune akan kujera tana fira da yaranta maza guda uku su Ra'is dasuka dawo daga masallaci tana murmushi yasa tasaki labule da sauri ta kalli Hamidan dake gefen ta tace "ke wacece wanan ni yatsu? A ina kika samo wanan hajiyan Hamida?" ahankali tace "nima bansan suba, maman yaron ne" da sauri Anty Lami tace "yaro? Au wai wanda aka ganku tare?" gyadamata mata kai tayi ahankali da sauri Anty Lami ta yaye curtain tafita fuskarta cikeda murmushi tace "barka da zuwa" dagokai Mami tayi da sauri ta mike tsaye, da sauri Anty Lami ta nuna mata kujeran tace "please sit, ki zauna dan Allah" zama Mami tayi ahankali tace "ina yini ina gajiya" cikeda fara'a Anty Lami tace "Alhamdulillah, maraba, sannu dazuwa, Hamida" ta kwalama Hamida kira ta kalli yaran nata dake kallon cartoon tace "kutashi kutafi dakinku, ku kiramin Hamida daga nan" tashi sukayi sukai ciki ba'a jimaba Hamida tafito kanta akasa Anty Lami tace "je kawo drinks da snacks mubama bakuwar mu ko" da sauri Mami tace "haba haba wlh bakomi dama har gida nazo namuku godiya akan karamcin da Amatullah daku kukama d'ana mara lafiya nagode, nagode, ubangiji Allah saka da alkhairi" daidai lokacin mijin Anty Lami ya shigo tareda Abie aka zazzauna ana gaggaisawa Hamida da kanta ke kasa ta kawo drinks ta ijiye da snack takoma ciki, ruwa kawai Mami tasha Abie kuma sai hira yake da mijin Anty Lami kaman sunsan juna nan Mami tabama Anty Lami labarin yanda Aadil din yafita daga mota haryasa tai hatsari, sosai Anty Lami ta tausayama yaron dudda bata ganshi ba sai bayan sallan Isha sanan sukai sallama Anty Lami ta kwalama Hamida kira. "Hamida" fitowa tayi kanta akasa Anty Lami tace "zasu tafi" dan dagokai Hamidan tayi ta kalli Mami a kunyace tace "Allah ya kiyaye hanya Mum" murmushi daga Mami har Abie sukayi sukace "mungode Hamida" suka wuce suka tafi har gate suka rakasu sanan suka dawo ciki ko minti daya basuyi da zama afalo ba wasu yara suka fara shigo da kaya niki niki wasu manyan ledoji ne guda uku na hadaddun turare da gyaluluwa, saikuma na atampopi guda uku da lace guda uku, dayan kuma na su chocolate da lot of cookies da sauri Anty Lami tace "inaa gaskiya bazamu karbaba

Table of Contents

Chapters

128 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128