Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

In Bani Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

[10/27/2019, 4:29 PM] Aishat Muhammad: _🌹IN BANI🌹_ _DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI_ _Wanan littafin nakine Fauzy, you're very Special, I love you so much, Allah ya raya three plates_ . M. Shakur 1..... Mata ne makil a babban compound din gidan dayasha simenti duk sun sanya anko iri daya, yara da manya sai hayaniya ake anacin shinkafa, wasu nashan pate, wasu nacin tuwon shinkafa da miyan taushe, wasu nacin fried rice da zobo, daga gefe kuma wasu tsofaffi ne daketa rera waka suna buga kwarya, wasu mata na rawa ana shewa ana manna musu kudi, ana guda kana gani kasan gidan biki ne. Babban gidane mai fadin gaske wanda saika wuce inda ake bikin sanan kabi wata kofa kaje dayar sasan dasuke kira da sasan kaka. Kasancewar sasan kaka baida girma sosai babu mutane a tsakar gidan, saidai ko ina fess simentin kasa sai kyalli yake tsabagen neatness din wurin saikuma pampoo dayake diddiga da ruwa dil dil dil da alamu duk wanda yay amfani dashi na karshe bai rufe da kyauba, flat daya ne a sasan kaka dake dauke da wani babban fankacecen falo da akalla zai iya daukan mutane hamsin, falon na dauke da wasu irin hadaddun kujeru maroon color, sai ledan daki mai shegen kyau shima maroon, sai wayansu hadaddun kwaryaye da ake jera ajikin bangon dakin, kana ganin dakin kaga dakin tsohuwa. wani magidanci ne ke zaune yasha fararen shadda inda akamai malum malum sai wata tsohuwa wacce akalla zatakai 79 agefenshi taci atampa daketa gyalli kaman an shafa mai ajikinta, an mata rigan kayan buba da zanin data daura akan rigan, sai kafanta da gabaki dayanshi yasha jan lalli tai lallin da akafi sani da dungulmin tsohuwa, farace tsohuwar, gashin idanunta dana giranta sun koma fari sabida tsufa, sai hancinta daketa uban zufa, dudda tsufanta bai hana kamanninta da magidancin dake zaune kusa da ita bayyana ba alamun mahaifiyarshi ce, cikin muryanta na tsofaffi kuma cikeda masifa tace "Sama'ila, Sama'ila, Sama'ila kaga dai sau uku nakiraka ko, wlh to nagaji, kodai ka tsawatar wanan karan, kona tattara yinawa yinawa nabarma gidanka nakoma chan kauye abina, aikin banza kawai" yanda take masifan yasa mutumin data kira da sama'ila ya sassauta murya yace "kiyakuri Umma na" "bawani zancen na yakuri" ta mishi ihu akah tana nunashi da yatsa tace "iskanci Hamida yay yawa kuma uwarta ke daure mata gindi inba hakaba iskokai ne mutane datake jin tsoron taro iyye? Mayune jama'a? Cha nayi duk yan uwane da abokan arziki suka cika gidan, yau bikin yayarta, yayarta fa Sama'ila amma ace tun safe ba'aga yarinya ba tasaci hanya ta sabe tafice, yo kajimin yar bazan yarin..." shiru tayi sabida sallaman da akayi wata kyaykyawan mace mai jiki doguwa tasa hadadden paper lace doguwan riga pitch da akamai stone work, ta shigo dakin fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso ciki ta gaida tsohuwar. "sannu da hutawa Umma" hararanta tsohuwan tayi batare data amsaba hakan yasa matar ta dubi mutumin dake kallonta tace "gani Alhaji ka aiko akirani" cikin fushi yana girgiza kafa yace "ina Hamida?" shiru tadanyi tana kallonshi kafin ta sauke ajiyan zuciya cike da damuwa tace "Alhaji nima bansan inda take ba" "karya takeyi na rantse maka Sama'ila, matar nan makira ce, itake kara lalata Hamida, wlh, wlh Sama'ila kajini na rantse maka na sake rantsewa in bata nemo Hamida ba saina bar gidan nan nakoma kauye abina dama nafi samin kwanciyan hankali achan" takarashe maganan tana uban huci kaman tana filin yaki, kallonta mutumin yayi cike da takaici yace "haba Umma, to kibari nai magana mana, nace kiyakuri babu inda zaki, kiyakuri kinji" kwafa tayi tawani juya ido tana karkada kafa tace "nayi, yi maganan ka" kallon matar yayi datai shiru tana kallonsu, anatse yace "Halimatu ina Hamida taje?" ahankali tace "wlh Alhaji nima bansani ba, bansan inda tayiba, ina fama da jama'an biki ban masan bata gidan ba saida Ihsan tazo ta fadamin" cikin fushi da tsananin takaici yace "to kije koma ina take ki nemota kindaisan Umma tace da ita za'akai yayarta chan legas gidan mijinta ko, na fadamiki kinemota ta dawo gidan nan right away" dan ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi kafin ta girgiza kai kawai cike da takaici ta juya zata fita daga dakin saikuma ta juyo ta kalleshi da idanunta da sundan chanza kala tace "amma Alhaji kasan matsalan yarinyar nan batun yauba ko, batun yau mukasan matsalan Hamida na Agoraphobia ba, batasan mutane, tanada tsoron shiga taro, tun tana yarinya haka take, yanz..." cikin fushi ya katseta ta hanyar cewa "yanzu yarinya ce? Me amfanin ki amatsayinki na mahaifiyanta? Kinga kisan yanda zakiyi kinemo Hamida kindaiga ran Umma abace yake kina kara bata lokaci ne karfe biyar za'a zo daukan Habiba yanzu karfe uku harda kwata" juyawa tayi ahankali tafita daga dakin, da kyar ta iya saita fuskanta ta amsa gaisuwan da mutanen tsakar gida ke mata amatsayin ta na uwar amarya ta wuce ta shiga bangaren su inda falon ma ke cike da jama'a makil, corridor su tayi tabude wani daki ta shiga mace dayace a zaune a dakin tana hada kayan akwatin amarya data ciro kana ganin matar kaga kamaninta da matar data shigo, maida kofar tayi ta rufe ta shigo ta zauna kan gado dabas da sauri tasa hannu tana goge kwallan daya zubo mata, da sauri matar dake hada kaya a akwati ta saki kayan hanunta tazagayo tazo ta gabanta tace "menene kike kuka Maman Ayush?" share idanunta tayi tanadan nishi alamun kuka nacinta tace "Yaya narasa yanda zanyi da Hamida, kullum, kullum dakika sani saita jamin cin mutunci daga wurin Alhaji da Umma, laifinane Yaya? Nina hallice ta? Munanan dake ai inata trying number ta baya shiga, natura yan uwanta duksunje makota kiramin ita ba'a ganta ba, Yaya ya zanyi? Narasa yanda zanyi na chanza Hamida, narasa wace irin yarinya ce, imagine fa Yaya yau bikin yar uwarta ma ta gudu tabar gidan, ni yanzu a ina zan ganta, yaya zanyi da raina?" takarashe maganan cikin daga murya sosai hawaye na gangarowa daga idanunta, da sauri Yayar tata mai suna Yaya Lami wacce take her only sister a duniya ta rungumeta ta daura kanta acikinta tana shafa bayanta tace "ya isa, ya isa dena kukan, bari na gwada kiranta kozai shiga, is okay." _Kukkuruku old train station._ Babban train station ne that has been abandoned for years yanzu, ba'a amfani dashi sabida sabon da aka bude, wajen shiru babu mahaluki ko daya sai wani tsoho baba mai gadi dake kwance kan wata yar katifa yakafa babban radio dinshi a kunenshi yaja antenna waje yana sauraran labaran rana. Zaune take akan dan danddamalin dake kusada railway, tana sanye da bakin hijabi har kasa daya rufe har takalmin kafanta, gefen fuskarta nake hangowa, farace sosai tana sanye da farin eye glasses, gashin idanunta bakin kirin dogaye, lips dinta kananu sunyi pink sosai sun bushe danko mai bata shafa akansu ba, gefenta wani karamin black and white jakane na MK sai wasu duwatsu yan kanana dake gefenta da akalla zasukai guda hamsin, ahankali ta zare hanun damanta dake cikin hanun hijabi data kankame ajikinta ta daura hanun akan duwatsu, farine hanunta sol da dogon yatsun ta sirara inda farcenta ke dauke da jan lalli,

Table of Contents

Chapters

128 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128