Chapter 2
Chapter 2
ahankali tai picking one stone tana kallon railway ta sauke ajiyan zuciya mai sauti cikin wata irin siriruwan murya nai bala'in dadi tace "Kakan mu!" jefa dutsen tayi akan railway tabi dutsen da kallo harya sauka akasa dutsen ya hargitsa duwatsan wajen ahankali tace "dutsen nan is just like Kakan mu, duk inda take saita hargitsa komi, Kakan mu! Kaman zakaran dawaki ce kukanta ba na alheri bane, Kaka! she's the definition of Iska ba nauyi gare kiba sai kada itace" wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu ahankali tace "wanan ne Baba, duk inda Kakan mu take yana wurin, baya tsalleke abinda tace, in kana neman sa kanka a bala'i a wurin Abba ka batama Kaka rai, hausawa sunce, Allah ya sauwake wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa" wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu tace "Mama! Mamana! My everything" shiru, ahankali tace "Mama kaman rake take, tanada zaki amma batada tau..." shiru tayi sabida ringing din da wayarta yafara dake cikin jaka. [10/27/2019, 4:29 PM] Aishat Muhammad: _🌹IN BANI🌹_ 2.... Duka jikinta rawa yafara da sauri ta kalli jakan, kasa taba jakan tayi har wayan ya karasa ringing ya katse, yafara ringing akaro nabiyu, sosai hanunta ke rawa da sauri tajawo jakan tabude taciro wayar tata kirar Samsung A50, Anty Lami data gani a screen yasa kirjinta ya buga da sauri ta dau wayar ta kara a kunenta kafin ma tai magana Anty Lami tace "ina kike Hamida? Nace ina kike?" ta daka mata tsawa, sosai hanunta ke rawa, kirjinta na bugawa dan bamatasan mezatace ba, kasa magana tayi but tana iyajin Maman su nacewa "tamiki shiru halan ko? Ban wayan kigani Anty" karban wayan Mama tayi ta kara a kunenta cike da fushi da takaicinta tace "wlh Hamida inba kinaso ki gamu da fushina da kin dade bakiga irinshi ba ki kamo hanya kidawo gidan nan right this second, dan iskanci ana bikin yar uwan ki kin kama hanya kin gudu, kidawo gida yanzun nan kinajina Hamida?" gyada kai tayi bakinta na rawa sosai tace "t...to Mama" katse wayar sukayi hakan yasa tabi wayan da kallo gabaki daya hankalin ta yatashi cewa da akayi tadawo gida, jakar ta jawo ta saka wayan ciki kafin ahankali ta mike tsaye, doguwar mace ce kyaykyawan gaske, fara ce fat kana ganinta kaga Maman su kaman su harya baci da Mama, tana sanye da fararen eyeglass idanunta ba kawalli saidai eyeliner dataja a saman ido dayama idanun wani irin cool kyau, giranta acike da gashi, gashin bakin kirin, sai dogon hancinta da dan karamin bakinta daya bushe, black hijabi ne jikinta wanda hulanshi ya rufe goshinta sosai dan saura kadan ma yarufe giranta amma dudda haka kana hango kwantaccen gashi a forehead dinta, dogon hijabi ne ajikinta dahar kafafunta ya rufe bama ka hango asalin kayan datasaka, da sauri tadau handbag dinta ta rataya tafara tafiya a natse kaman batason taka kasa ahaka ma wai sauri take tafito wajen da sauri Baba mai gadi ya rage karan radio dayake ji ya juyo ya kalleta yace "har zaki tafi Hamida?" gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tana kakkare fuskarta da hijabi kaman wacce tai laifi tana kara sauri, murmushi yayi yace "shikenan sai gobe tunda baza amin magana ba, gobe ma zaki kawomin tuwon ne Hamida?" gyadamai kai tasake yi still batare datamai magana ba tafice daga wurin da saurin ta, murmushi Baba mai gadi yayi yakomar da kanshi ya daura akan filo yana murmushi ahankali yace "Hamida kenan" yasake yin wani murmushin ya kara karan radio shi yacigaba dasauraran shirin da ake. Da sauri take tafiya akan titi tana kakkare fuskanta da hijabi, keke napep ta tsayar ta shiga ciki da sauri tana kallon gefe daya batare data kalli mai keken ba tace "j...jan bulo zani" "naira dari uku ne kudin ki hajiya" gyadamai mai kai tayi tana kara rufe fuskarta da hijabi tace "to" tada keken yayi suka fara tafiya har zuwa jan bulo sosai gabanta yafadi dan sosai anguwan su yacika da manya manyan motoci, da mutane ga maza ko'ina, jitayi hankalinta yatashi tunanin ta shine yanda zata wuce mutanen ta shiga gidansu, ahankali tace "yayi nan" tsayawa mai keken yayi ta zage jakanta taciro dari ukun ta bashi sanan tafito tana kare fuskarta da hijabin ta saukar da kanta kasa tafara tafiya ahankali batare data bari sun hada ido da kowaba kirjinta kaman zai fashe zuciyata kaman zai fito waje, a kofar gidansu ta tsaya chak ta leka ciki uban mutanen data gani ciki yasa ta koma gefe jikinta na rawa duk ta birkice, wata yarinya ce kyakyawa da bazata wuce 10yrs ba tafito sanye da doguwan rigan ankon dayamata kyau sosai, ware manyan idanunta tayi ta kalli Hamidan dabama ta lura da itaba sai kakkare fuskarta takeyi tana sake mammanewa ajikin gate dinsu kaman wacce tai laifi ake shirin kamawa akaita ciki, cikin daga murya tace "laaaa Anty Hamida yaushe kika dawo? Ina kikaje anata nemanki? Kinga anma kusa kai Anty Ayush" dan janye hijabinta tayi back jin muryan kanwarta ta kalli kanwar tata dake kallonta, da idanunta dasuka cika da hawaye cikin rawan murya tace "I..Ihsan jeki fadama Mama nadawo ni bazan iya shigowa ba mutane sunyi yawa" juyawa Ihsan din tayi ta leka compound din saikuma ta dawo wurinta tace "wlh Anty Hamida babu wasu mutane fa, su kawayen Mama ne dana Kaka, saikuma su maman Rabi makotan mu, zomuje ki shirya kisaka ankon ki" tai maganan tana kamo hanunta, sake komawa baya tayi tana zaro mata idanu kaman zatai kuka da yar karaman cool voice dinta tace "Ihsan stop dan Allah kunyan shiga nake" daidai lokacin wata budurwa da bazata wuce sa'an Hamidan ba tazo zata wuce ta shiga gidan dan daga gidan Pharty su na kawayen amarya take taci gayu sosai cikin ankonsu na yan mata wani pink ashobi doguwan riga an mata dauri hadadde tadan yafa gyale a kafada, kwala mata kira Ihsan tayi. "Anty Zainab" da sauri budurwan ta juyo ganin Hamida tsaye tana kakkare fuska da hijabi tana komawa baya yasa ta rike waist takaraso wajensu cike da mamaki tana kallon Hamidan tace "Kinga daman dawowa Hamida?" da sauri Ihsan tace "Anty Zainab kinga wai bazata shiga cikiba, kumafa Mama na nemanta tun dazu dasafe, Kaka ma ta aikani nemota yafi sau dari uku" kallonta Zainab din tayi ta harareta tace "wuce mutafi" da sauri ta share hawayen dasuka zubo mata da hijabi tace "Anty Zainab mutane" "to uban me zasu miki? Cinyeki zasuyi?" kallon wajen tayi cikin tashin hankali tace "nidai zan tsaya anan kucema Mama nadawo" ganin kara makalewa take a bango kuma tasan halin ta tsaf inba ka tursasata ba wlh bazata shigan ba yasa zainab ta karasa wajen ta finciko hanunta tajata da karfi, fashewa tayi da kuka sosai tana waigen baya tana neman fizge hanunta daga na Zainab din, da sauri Zainab tace "rikemin dayan hanunta Ihsan mu shiga ciki" da sauri Ihsan din ta rike dayan hanun suka jata zasu shiga ciki, fashewa tayi da kuka duka hankalinta yatashi tanason kwace hanunta takasa dan zainab akwai shegen karfi, cikeda tsoron shiga gidan tace "Anty Zainab dan Allah no,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128