Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

In Bani Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

kano saukowa sukayi suka shiga taxi dazai kaisu gida. Sosai taji hankalinta yawani irin kwanta data gansu a anguwan su sai murmushi take tana kallon anguwan su, ta mirror Faruk ke kallon fuskarta yanda take murmushi tana kallon hanya, suna parking a kofar gidansu da sauri tabude kofan motar tafita, Mama ce kadai a tsakar gida da matan dake zuwa musu wankau, wani irin murmushi tayi ta kwala mata kira. "Mama" da sauri Mama ta juyo jin muryan Hamida, wani irin gudu Hamida tayi taje tafada jikinta tana dariya ahankali yanda takeyi, cikin jin dadi da tsananin farin ciki Mama tawani irin rungumeta tace "kedawa yene Hamida?" tai maganan tana cirota daga jikinta dan taji tsoro ganinta kaman an jehota, ko kadan batasan Abba yacema Faruk yaje yadaukota ba jiya da daddare ba, tana jikinta rungume da ita tace "Yaya Faruk yazo yadauko ni fa Maman mu" daidai lokacin Faruk ya shigo gidan rike da jakanta, murmushi Mama tayi tace "to aisai kije ki gaishe da Kakan ku kizo" tasaketa tana kallon Faruk dake karasowa wajen rike da jakanta tace "sannu soja shine ta barka da jakan ko" ahankali ya ijiye jakan agaban Mama kanshi akasa yace "ina kwana Mama" sakin Mama Hamida tayi tai hanyar sasan Kaka, ahankali ta turo kofan ta shiga tana kallon ko'ina tai sallama cikin daga murya Kaka tace "Hamida, Hamida, aini tun ranan dazaki tafi nace saikinsan mekika yi, sai kinsan me kikayi, me kika shirya, saikinsan kirsa da kisisina dazaki hada ki dawo garin nan, Hamida anya bazan kiramiki malamai azo amiki rukiyya ba inaga aljanu gareki fa" dan turo baki tayi tasami waje ta zauna nesa da ita tana wasa da bakin hijabin ta kaman bada ita ake magana ba, zaro ido Kaka tayi tace "nikika maida mahaukaciya ina magana kinmini banza" daidai lokacin Faruk ya shigo dakin, watsa mata harara yayi yace "ke tsohuwar nan kin cika ihu, please inada ciwon kai yau kiyi shiru pls" yay maganan yana karasawa wajen fridge din dake falon, binshi da kallo Kaka tayi baki abude hakan yasa Hamida tarufe bakinta da hijab tana dariya chan kasa kasa, juyowa Kaka tayi ta kalleta ranta abace tace "dan gidanku dariya kike mini" da sauri ta girgiza kai still tana dariya chan ciki gudun karta ji tana kare bakinta da hijabi daidai lokacin shima Faruk yadawo rike da bottle water ya zauna a gefen Kaka zai bude bottle water, duka ta dakamai abaya da sauri ya kalleta cikin fushi yace "auch waike old lady nan me haka kike dukana agaban yara" kaman Kaka zatai kuka ta nuna kanta tace "kafara kirana da wanan yaren yahudancin ko Faruku, to wlh bari ubanku yadawo saina fadamai cin mutunci dakuke shigowa har Sasa na kukemin, ku tashi kufita, kutashi kufita nace, kuma bani ruwan gorana saurayin Zainaba ya kawomin su kusan katan biyar, bani" tafada bacin rai tana mika hannu zata karbi ruwan, tsaki yayi yadaura kafa daya kan daya yanashan ruwan shi ahankali Kaka tasaki baki tana kallonshi tace "ai shikenan kasha wuta shege dan buhun uba" fashewa da dariya Hamida tayi dayasa Faruk saukar da ruwan daga bakinshi ya watsa mata wani mugun kallo da sauri ta tashi tafita daga dakin da gudunta yabita da kallo, hararan kofan Kaka tayi tace "ja'irar yarinya, ai wlh Faruk banso kaje ka daukota ba, so nayi jiya da Sama'ila nama maganan kace aiki zaka, baga tanan ba rass bataima kama da wacce tafada ruwaba" juyowa Kaka tayi ta kalleshi daidai ya ijiye ruwan akasa tace "kaje wurin Maman kane yau?" girgiza mata kai yayi yana yatsine fuska, yace "sai anjima da yamma yanzu aiki zan tafi" washemai baki tayi tana kara matsowa kusa dashi tana murmushi tace "Faruku na wai har yanzu ba'ayi albashin bane, kamin alkawarin dubu ashirin fa" hararanta yayi yace "jiya agabana Abba yabaki dubu talatin wai mekike yi da kudi ne haka?" sake matsowa kusada shi tayi kaman zatai gulma tace "na rantse maka Faruku adashi nakeyi, tara kudin bikin Hamida nake" wani irin kallo yamata yace "wace Hamidan?" baki tabude tace "kagamin iskanci munada wata Hamida agidan nanne bayan wanan hamidan data fita daga dakina yanzu?" cikin daure fuska yace "yaushe tai saurayi?" sake matsowa tayi kusa dashi kaman wacce ke shirin yin gulma tace "a'a kaima dai kasan ko mashinshini Hamida batadashi ko, amma so nake kabani kudin dukna hada naita zubin adashi ina tari, inama bikin ta tari, kasan Hamida yar wajena ce, itace mai sunana fa, kaga shegen fadan nan danake mata wlh sonake ta chanza ne dan batayi gadon halina ba, bataci sunana da aka bataba, amma dazaran ta chanza zamu zo mu fara shiri sosai, nama tuna bari naje sasan su hado kayanta zatayi tadawo shashin nan ma yau dinan" shiru tayi tana nazarin yanayin fuskanshi yanda yay kini kini darai, tace "kaikuma lafiyan ka naga kai wani iri" yatsine fuska yayi yace "am fine" ya mike tsaye yana gyara kayan jikinshi yace "natafi aiki" tashi tayi tace "muje na rakaka, kadan tahomin dayar bakan leda kaji inzaka dawo, tunda su Zainaba da Ayush sukabar gidan da yunwa nake kwana Faruku" hararanta yayi yanaji kaman ya bugeta kiri Kiri sai Kaka tabude ido tana karya, dariya tayi sosai ganin yanda yake kallonta tace "bawai yunwan abinci ba na kayan kwadayi, idan kadawo kaza bani kudin aiko? Bazanyi barci ba zan jiraka" hararanta yayi yajuya zai fita hanunshi da damke tace "dan ubanka saika bani danma ina lallabaka" kaman zaiyi kuka ya kalli yanda ta damke well ironed uniform dinshi yace "naji inna dawo zanbaki, ki saken to" sakinshi tayi tana dariya ta dungure mai kai tace "ja'iri barima ubanku yadawo yau zan mishi maganan aurenka ne, wlh koka fito da mata kona je kauye nahadaka dayar aminiyata Iyami" tsaki yayi tsabagen takaici baima tsaya yabata amsaba yawuce yafita daga sasan da sauri tabi bayanshi amma har yay wajen gate hakan yasa tai tsaki ta wuce part din su Hamida. Da sallama ta shiga falon su Hamida tagani zaune a falon tanacin indomie data dafa da boiled egg tana kallon zee world tana ganin Kaka tai murmushi tana sunnar dakai, hararanta Kaka tayi tace "aikin kenan ki zauna ke kadai awuri babu kowa shine burinki a duniya miskilan banza, ni ina mamarki?" daidai lokacin Mama tafito daga kitchen rike da tray data debo wake dan gyarawa zatayi tana ganin Kaka tai murmushi tace "yau Umma a shashin mu" da sauri Kaka tace "eh nazo ne, kihada ma yarki kaya sasana zata dawo" turo baki Hamida tayi tana tauna abincin dake bakinta ahankali Kaka ta kalleta tace "ahap ai saidai ki mutu ingayamiki yarinya, yaushe zasu koma ma makarantan yama sunan hutun da sukaje?" murmushi Mama tayi tana karasa shigowa cikin falon tace "mid semester break" da sauri Kaka tace "yauwa shi yaushe zaku koma ke?" tai maganan tana kallon Hamidan dakecin abincinta, dan turo baki tayi tace "ranan Monday" kwafa Kaka tayi tace "saura wanan karan ma ki kwaso zero zero a makarantan kaman na wanchan karan, wlh cema Sama'ila zanyi bazai kara kashemiki koda sule biyar a makarantan ba, aure zamu miki, inyaki kuma nida kaina zan aurar dake" da sauri ta kalli Kaka, gyada mata kai tayi tace "eh kinjini

Table of Contents

Chapters

128 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128