Chapter 9
Chapter 9
uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇 +227 84 50 64 76 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* [23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_ 📃Littafi na 1 By🪶 *Ummu maher(Miss green)🍏* *GAWURTATTU 5* --------------------- masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi. *SIRRINMU* Mu kasance masu tsarkakkiyar zuciya,kada mu dinga hassada ko baƘin ciki. 9🟨10 . .. ."Rashida gaskiya irin wannan zaman da mukeyi a tsakaninmu dasu Nadiya bai kamata ba,ko da ace ma bamu san juna ba ai ya kamata ko gaisuwa ta dinga haɗamu?". "Hmm Khairat kenan ni ina mamakin hali irin na ki wallahi waɗannan mutanen fa babu abinda suka sani illa su zageki su baƙanta miki,to me ye amfanin zuwa wajensu?ranki ne kawai zai ta ɓaci a banza wallahi,amman ni bazan hanaki zuwa wajen ƴan uwanki ba,amman ni dai ba zanje ba idan kinga ke zakije ga ki gasu amman ni dai La-La-La ina da abinyi ne ni dai."tana faɗar hakan ta yi shigewarta banɗakin da ke jikin ɗakin ƙwananmu.wata ƙawarmu mai suna Hasiya tana zaune tana karatun wani novels ta juyo tana kallona ta ce"gaskiya ne abinda Rashida ta faɗa miki duk da ni ba ƴar'uwarku ba ce amman zan faɗa miki gaskiya ku fita daga harkarsu nadiya dasu iman saboda wallahi yanzu kaf ma skull ɗinnan babu wanda bai san grp ɗinsu ba,yanzu haka suna da grp mai zaman kansa a makarantar nan na ƴan lesbian so be careful da waɗannan duk da su Nadiya babanku ɗaya amman idan zan baki shawara idan har kun koma gida ki sanarwa da mahaifinku duk abinda ya ke faruwa idan da hali ma ayi musu aure kawai shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallona. Tabbas wannan abinda Hasiya ta faɗa min ya girgiza tunani na sosai,an daɗe ana faɗamin abinda su Nadiya suke a skull sam basa karatu yanzu,daman tunda muka shiga makaranta suka haɗu da ƙawaye suka hure musu kunne shikkenan suka ƙara tsanata da hantara ta tunda ni dai a kullum gaskiya na ke gaya musu. Jikina a sanyaye na tashi na cire kayana na faɗa banɗaki bayan Rashida ta fito,ko a wajen wankan ma tunani kawai na ke na yadda zan ɓullowa lamarinsu Nadiya don idan wani yaji wannan maganar a gidanmu to tabbas zasu shiga tsaka mai wuya don hatta kashi ma sai ya fisu mahimmanci a gidanmu. Bacci ma da ƙer ya ɗaukeni saboda tunani,ni mutunce mai saka abu arai musamman wannan abin daya kasa gogewa a zuciya ta,a duk tsahon rayuwata ban taɓa saka wani abu araina irin Yaya Bilal ba sai kuma wannan maganar tasu Nadiya. Da sassafe muka tashi muna shirin tafiya assembly don yau litinan(monday)uniform ɗinmu kalar baƙi da fari wato black&white riga da hijab duk fari wando baƙi kamar kalar kayan likitoci,munyi ƙyau sosai acikin kayan na mu muka jero mu uku ni da Rashida da Hasiya don daman mu uku ne acikin ɗakin. Ta ƙofar hostel ɗinsu Nadiya muka biyo abin mamaki su haryanzu basu fito assembly ɗin ba,na kalli Rashida cikin dakiya da nuna kulawa na ce"Rashida don Allah mu shiga wajensu Nadiya mana mu duba su".?kallon tsaf ta yi min sannan ta ce"Hmm gaskiya Khairat kina da matsala wallahi yanzu ko jiya ma fa sai da mukayi maganar nan,bana son ki jefa kanki acikin matsala garin gyara kuma ku ɓallowa kanki matsala,don kin san grp ɗinsu ɗaya da big girl kuma kin san daman tana harinki a skull ɗinnan don ki zama lalatacciya irinsu,to kinga idan kina zuwa wajensu komai zai iya faruwa da ke".ta faɗi hakan tana kallona sosai fuskarta alamun jin tausayina. Hasiya ta da fa kafaɗa ta ta ce"Khairat bama son abinda zai taɓa rayuwarki ki yi haƙuri don Allah ki taho mu tafi,ki dinga taya su kawai da addu'ah kuma ki yi amfani da shawarar dana baki jiya,ko da kun koma gida kada ki manta wannan shawarar dana baki". gyaɗa kaina na yi kawai na bisu don hankalina nima bai ƙwanta da zuwan na wa ba,abin mamaki sai da aka kusa gama assembly sannan suka shigo suna wani bubbuɗawa duk idanuwansu sun kumbura alamar basuyi bacci ba,Rashida ta ce"Allah dai ya shirya wallahi sun ƙwana suna lalacewarsu ai dole ido ya kumbura,iyayenmu na cen suna tattalin rayuwarmu da bamu tarbiyya amman su ƴan rashin kamun kai suna nan suna lalacewa." nima ganinsu da na yi sai da gabana ya faɗi saboda ganinsu a cikin wannan halin don ko da ba'a gaya maka ba kasan abinda ya faru,na ji wata ƙwalla mai zafin gaske ta zubomin na saka hannaye na na sharesu Rashida tana kallona ta ce"iska tana wahalar da mai kayan kara". rai na duk babu daɗi har aka gama assemly ɗin muka shiga aji,muna fitowa muka koma hostel ɗinmu muka fara girki ƴar ƙaramar wayar Rashida ta fara ƙara ta ɗaga tana ce wa waye?".shiru akayi kafin daga bisani taji ance "abdullahi ne don jakar ubanki".tsalle Rashida ta yi ta ce"Hajiya kaka daman kina duniya"?.da sauri na amshe wayar harda ƴar ƙwallah ta ka fin inyi magana ta ce a bawa ABIN CIKIN ƘWAI,in dai kaji kaka ta faɗi wannan sunan to tabbas dani take. Rashida ta ce"to ai tun kafin ma in ba ta ta amshe ita me kaka".ina jin kaka tana ce wa"to ke kuma da ba kakar ki ba ce sai ki siyo a kasuwa".riƙe kai Rashida ta yi Hasiya tana ta ɓaɓɓaka dariya don ita dai Allah ya saka mata son tsohuwar aranta. "Hmm Abin cikin ƙwai ni dai ina ganin baƙin ciki a gidannan wallahi?idan suka isheni wallahi tattara kayana zanyi in koma uman wajen ƴan uwan mahaifina ko kuma in tafi Bauchi".tana faɗar hakan ta tintsire da kuka. Haba ai Rashida dariya harda tsalle tana ce wa"Hajiya kaka yasin kin kusa margayawa ki yadda kawai,amman in banda tsufa ba'ayiwa mutum komai ba sai ya tattara kayansa yabar gida".? kaka na juyo ta ta ce"shegiya jinin fulani muguwa kawau to babu inda zanje sai inga ta dariya,daman uwarki ce ta ɓata min ran wai akan Sadiq ɗan wajen auwalu ya ce yana son nusaiba shikkenan tsohuwar ƴar bokon nan uwarku ruƙayya ta kafa ta tsare wai ita bata son auren dangi,yanzu don Allah idan banda baƙin hali ita da ubanku ba auren dangi bane?". Haƙuri na fara bawa Hajiya kaka ta ce"ai wallahi da ce wa na yi tafiya ta zanyi tunda ita dai bata san kara ba".Rashida da ke jinmu tana kallona alamun dai bata ji daɗin zagin da kaka take wa mahaifiyarta ba. Nima da ba uwata aka zaga ba tabbas banji daɗi ba,in banda abin kaka ai nusaibar nan dai ƴar ta ce ko?amman kuma ta ce bata so saboda nusaiba yarinya ce har ayanzu bata rufa sha 15 ba a s.s.1 take mu kuma muna da 17 aduniya yanzu kuma muna s.s.3 muna shekararmu ta ƙarshe. Nan dai Hajiya kaka ta gama faɗanta daga baya ta kashe wayar,muna gama wayar na kalli Rashida na ce"kai kaka aƙwaita da fi'ili wallahi kamar dole sai ta haɗamu auren dangi haka fa kema da yaya mohd ta da ge sai ya aure ki,don Allah yanzu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87