Chapter 37
Chapter 37
yi ƙwanan nan tunda dai yanzu na samu wadda na keso". sunkuyar da kaina ƙasa na yi,kaf duniya ina tunanin babu macen da za tace bata son Ahmad don babu abinda baagi dashi,ƙyau,kuɗi,addini,ilimi,tarbiyya,kamala,sanin ya kamata,kai har dama waɗansu abubuwan. Ganin na yi shiru sai ya ce"a gaskiya ni ada na fitar da yin aure arayuwata saboda bazan ɓoye miki ba na taɓa yin aure acen baya sai dai gaskiya ko kusa banji daɗin auren ba,saboda banyi dacen mata ba,zanso inji sunanki baiwar Allah don naga kamar wayo ki ke son yimin ina ta zuba ba tare da kin faɗa min sunanki ba?". a hankali na ce"sunana Rahma amman ana kirana da khairat". "Wow nice name,sunan mahaifiyata ne da ke gaskiya naji daɗi,ammsn ina son ki faɗamin kina da ra'ayina ko kuwa?Don gaskiya ni arayuwata bana magana biyu,kawai idan har ina son abu to babu tabbas shi ɗin na keso babu mai canjamin tsari na,don Allah khairat inason ki faɗamin gaskiyarki akaina?Ni dai har ga Allah kin tafi dani baki ɗaya,na sadaukar da aikina na awa kusan huɗu saboda ke,wanda atarihi na ban taɓa yin hakan ba". Sunkuyar da kaina na yi don a gaskiya bazan ɓoye masa komai ba,don ayanzu an bada ni kuma ma gaskiya ko da ba'a bada ni ba,maƙalalliyar zuciyar nan ta wa tana wajen Yaya Bilal,duk da babu abinda Yaya Bilal zai nunawa Ahmad ɗin sai dai kawai fari,amman banda wannan babu abinda zai nuna masa. A hankali na ce"kayi haƙuri C/M ayanzu haka har an saka ranar aure na nan da sati uku masu zuwa za'ayi bikina,amman ka yi haƙuri gaskiyar daka baƙata ita na faɗa maka".na faɗi hakan ina sunkuyar da kaina ƙasa. Wani mugun jiri yaji yana ɗibarsa duk da jikinsa yadda ya ke kamar rainon ƴan rastling amman sai da ya kusa faɗuwa,ya buɗe kyawawan idaniyarsa sannan ya ce"khairat haƙiƙa kin burgeni da faɗamin gaskiya da ki ka yi amman ko babu komai inason ƙulla zumunci da gidanku,idan an tashi ɗaurin aurenki zanzo,ga wayata sakamin number ɗinki".?Ya faɗi hakan yana jin adadin zafin zuciyarsa na ƙaruwa,ciwon kansa nasan tashi masa ƴan awanni da haɗuwa da yarinya yaji kamar zai mutu idan bai aure taba,gaskiya wannan yarinyar tana da sa'a sosai don matan da suka amsa sunansu mata masu ji da kuɗi da komai,sunsha zuwa wajensa da furucin soyayya amman ko kallon ƙurarsu baiyi yanzu gashi kan yarinya ƙarama wacce a ƙiyasinsa bata fi 17 zuwa 18 ba. Samun kaina na yi da murmushi na amsa na saka masa na bashi,ya yi murmushi sai naga kawai hawaye suna zubo masa ya ce"khairat Allah yasa albarka acikin wannan auren na ki,idan babu Albarka Allah ya wargazar ko ƴata Inaas ta samu uwa tagari kamarki". Buɗe idanuwana na yi sanna na ce"au daman kana da ƴa ne?".Murmushi ya yi sannsn ya ce"ina da ƴa shekararta biyar amman yanzu mun rabu da mamanta tana hannun mahaifiyata,kullum burinta in samo mata momi amman na kasa hakan tunda bab haɗu da wacce na keso ba,sai yanzu Allah ya yi gashi kuma wani mai sa'ar ya rigani,to shikkenan ni zan tafi khairat saduwar Alkhairi". Tafiyarsa ma kaɗai abin kallo ce ina tsaye naga sun tsaya akusa dani ya ce"khairat idan babu damuwa shigo mu sauke ki agida?wannan titin babu kowa kuma bai kamata ki tsaya ke kaɗai ba,alhalin kuma kina amatsayin mace,macen ma mai daraja". Samun kaina na yi da yarda dashi na shiga muka tafi,har mukaje bai ƙara ce wa komai ba nima kuma bance ƙala ba,da zan fita har na saka ƙafufuwana awaje ya ce"khairat"!. Juyowa na yi cikin mamakin jin kirana da ya yi,na juya ina kallonsa na sunkuyar da kaina don bazan iya kallon cikin idaniyars ba,don yana da ƙwarjini sosai. Ya ce"khairat idan na yi miki ƙyauta zaki amsa"?.Ya kunnomin wannan tambayar na ce"zan amsa C/M tunda daga hannun mutum mai alfarma ta fito kuma mai mutunta mutane". Ɗan murmushin jin daɗi ya yi sannan ya ɗakko wani envelope ya miƙomin,amsa na yi cikin nutsuwa sannan na ce"na gode!ka gaida min da Inaas". Sosai naga murmushi ya bayyana akan fuskarsa saboda aduniya yana son mai son nasa,musamman ma kuma Inaas ƴarsa ya ce"naji daɗi khairat insha Allah zan kai gaisuwarki wajen Inaas". Nima murmushin na yi sannan na ce"to na gode sai anjima".ina faɗar hakan na juya zan tafi gida sai naga Yaya Aliyu da Anty khadija zasu fita. Tsoro ya kamani don nasan sun riga da sun ga C.M don haka na sunkuyar da kaina,ganin hakan yasa M.C fitowa suka gaisa da Yaya Aliyu sannan ni kuma na yi cikin gida kunya duk ta isheni. ina shiga Anty Khadija ta shigo ita ma sai naga tana wani washe min baki ta biyo ni har ɗakina lokacin ina cire kaya da ɗaurin ƙirji ajikina, sai kuwa ta ce"am daman khairat tambayarki zanyi"?.Ɗan ɗaure fuska na yi kaɗan don nasan tambayar daza ta yi kenan na ce"uhm ina jin ki"?. Sai ta nemi waje ta zauna ta ce"yauwa me ye kuma haɗinki da Commisioner of police"?.Tambayar ce tazo min abaza ta sai na ce"babu komai sai zumunci". Sai kuwa ta ce"a'ah fa khairat bana son ƙarya ni dai a iya sanina kaf ƴan uwanmu ban taɓa jin ance ɗan uwan mu bane,sai dai idan saurayinki ne?Ammsn gaskiya kuwa idan haka ne kin more saurayi mutum har mutum a tsaye kamar shi ya yi kansa,ga kuɗi ga komai,kuma naji ma ance ɗan sarauta ne ko"?.Ta faɗi hakan tana washe baki. Ban kula taba sai kuma ta ce"amman khairat yanzu sabida Allah ai an kusa bikinki sai dai ya yi haƙuri,amman wallahi ni dai da so samu ne ki aureshi don ni har yafi min yaya Bilal wanda a kullum ya ke wulaƙanta ki". Banza na yi mata sannan na yi shigewa ta banɗakin dake manne ajikin ɗakina ina mamakin shegiyar gulma irin ta anty khadija. Ganin banyi magana ba yasa ta tashi ta fita,babu abinda M.C ya ɓoye wa Yaya Aliyu a game da haɗuwarmu,ya amshi number yaya Aliyu ya ce"idan auren Khairat ya tashi ku faɗa min".sosai Yaya Aliyu yaji daɗi sannan suka yi sallama da M.C ya shige mota. Bai dawo gidan ba ya shige mota don ɗakko mama a filin jirgi da ƴan uwanta har uku,saboda bikin khairat don Yaya Aliyu ya yi mata bayani sosai amman fa mama ta yi baƙin ciki sosai,don gani take ai itama uwa ce kuma ya kamata ayi mata uzuri a nemi shawararta don za'ayi wa ƴar ta aure ba tare da saninta ba,badon Aliyun ya faɗa mata ba sai dai taji a gari kuma ga auren Salim da kuma Auren Aliyu ɗin,mama ta dinga yi wa Aliyu faɗa akan ƙarin auren nasa,amman sai Aliyu ya yiwa mamansa bayani sosai na abinda yasa zai ƙara auren,itama maman tasan wasu daga cikin halin Khadija ɗin, ta yi musu fatan alkhairi da samun zaman lafiya mai ɗorewa. *** "Ahmad lafiya naga yau duk idanuwanka sun kumbura kamar ka yi kuka?me ya faru da kai"?.Hajiya Ramatu ce ke yi wa ɗanta C.M wannan tambayar?. Babu abinda ya ɓoye wa mahaifiyarsa akan Khairat,ya ƙara da faɗin "Hajiya yanzu mata nagari sunyi ƙaranci acikin wannan al'ummar tamu,za kiga mata suna shiga ba-ga matan aure ba ba-ga ƴan mata ba,haƙiƙa babu abinda yasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87