Chapter 81
Chapter 81
da muje asibiti ba naƙi,daya gaji ya kiramin likitansu yazo har gida. Likitan yana murmushi ya ce"congrat matarka nada ciki amman ƙarami ne sosai,sai kuma an kula da ita don ulcer nason kamata saboda bata cin abinci." Ya rubuta magunguna yana tafiya ya ɗagani sai yawo ya ke dani yana murna,ni ma sosai naji daɗin hakan don gaskiya inason in haihu musamman dana daɗe ban haihu ɗin ba.Ammi har kyauta ta yimin na gwal shi kuwa gogan wai har ya fara yi wa ɗansa tanadin wani campaninsa wanda ya keji dashi a ƙasar dubai.ni mamaki ma suka dinga bani kamar basu taɓa ganin haihu ba.? ********* Rayuwa kenan alhaji damas har gidan yari yasa akaje aka fito da Jidda sai dai daga baya akaji labari mara daɗi ya kashe ta har lahira,saboda kada ta tona masa asiri. *Miss green ce* [23/09, 16:31] Miss Green🍀: *🏮ABIN CIKIN ƘWAI🏮* littafi na 3 *by✍🏿* Ummu maher(miss green)🍀 Wattpad user name Rabiatu333 Arewabooks rabiattu0444 *SIRRINKI👂🏻* 1 *Yadda ake maganin ƙurajen fuska.* Daga ummu maher Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haɗa arinƙa gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15. 2 ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ƙwanta bacci idan ya tashi ya wanke. by ummu maher 99. . . . . . .100 . . . .sosai abin ya ɗagawa mutane hankali ba iya su Bilal da captain ba,Bilal da captain suna cikin motar Bilal ɗin ya nisa cikin tunani ya jiyo captain na ce wa"kai Bilal nifa abin Damas yanzu mamaki ya ke bani,tun bayan daya gudu ƙasar waje bamu sake jin ɗuriyarsa ba,ya yi tafiyarsa abinsa ya koma cen yana cigaba da harkokinsa na masha'a da lalata yaran mutane ashe abin yana nan aransa shine ya dawo ya kashe jidda?gaskiya Damas shu'umine ba nawa sa ba." Ya faɗi hakan yana girgiza kansa,Bilal ya ce"captain ita rayuwar nan cike take da darasi sosai,duk wanda kuma ya yi me kyau zai ga me kyau,ni dai yanzu kaga Jidda ita ce ta yi sanadin rabani da khairat,rabuwa ta har abada wallahi captain zuciyata gab take da bugawa,ina ji ina gani khairat ta yi aurenta,ko kallon arziƙi bai haɗani da ita idan ta ganni ma captain yadda kasan taga wani dodo,Allah kamarin khairat har mamaki ya ke bani" Ɗan murmushi captain ya yi sannan ya ce"Tabbas Bilal nima da kaina na yadda rayuwa cike take da ƙalubale,Bilal aƙwai wani laifi wanda ka yi wa khairat wanda aduk sanda ta ganka sai taji bata son ko haɗa ido da kai saboda girman laifin da ka yi mata. Na farko shine ka zargeta da laifin da ba ita ce ta aikata sa ba,na biyu kuma shine rashin binciken da baka yiba alokacin da abin ya faru,wanda Darasin daya kamata ka fuskanta anan shine shi saurin fushi yana haifar da dana sani,don haka shiyasa ya ke da kyau duk abinda zamuyi mu dinga bincike kafin mu aikata,koma koda mutum yana cikin fushi bai kamats ace ya saki matarsa har saki uku ba,ai addini bai ce haka ba Bilal." Idanuwan Bilal sunyi jawur ya juyo ya ce"Hmm captain baza ka gane abinda naji alokacin ba,duk abinda zan ƙwatanta maka dashi to tabbas ya wuce hakan,ina da matsanancin kishi sosai,musamman ma akan khairat,yarinyar da tun tana cikin mahaifiyarta na ke azabar sonta,amman dubi abinda khairat ta yimin yanzu". Yana faɗar hakan ya dafe sai tin zuciyarsa ya ce"captain ina jin wani abu acan cikin zuciyata yana yimin yawo,tabbas zuciyata saura kaɗan ta buga,captain ka kaini gida yanzu bazan iya zuwa ba".ya faɗi hakan yana dafe saitin zuciyarsa wanda ya kejinsa kamar zai fito waje,ga wani irin zafi da ya keji acan cikin zuciyar tashi. Sosai Captain ya tsorata ya koma mazaunin Bilal ɗin ya tuƙa motar cikin gaggawa,asibiti ya kaisa don a halin daya ga Bilal bazai iya kaisa gida ba,shima captain ɗin hawaye ne ke fitowa daga cikin idanuwansa,yana riƙe da hannun Bilal ɗin guda ɗaya,Allah ne dai ya kawosu asibiti lafiya. Likitocin suka amshesa suma duk hankalinsu a tashe don tuni har ya sume ma,aka shiga dashi emargency.Captain sai hawaye ya ke da sauri ya kira wayar Alhaji Abdullahi mahaifin Aliyu,ya sanar masa duk abinda ke faruwa shima hankalinsa ya tashi sosai,tuni ya sanarwa da ƴan uwansa suka taho tare,amman ba'a gayawa Hajiya kaka ba,harma da mahaifiyar Bilal ɗin bata sani ba. Sosai hankalinsu ya tashi da jin abibda likita ya faɗa,cewar jininsa ya yi mugun hawa wanda idan ba'a basa abinda ya keso ba komai zai i'ya faruwa,sosai hankalinsu ya tashi to me Bilal ɗin ya keso wanda ba'a yi masa ɗin ba?suka zauna jigum jigum.Baba Usman ya ce"to yaya ko kasan abinda ke damunsa ne?wanda mu bamu sani ba?". Kaɗa kai Alhaji Abdullahi ya yi sannan ya ce"wallahi Usman ni kai na bazance maka ga abinda ke damun Bilal ba,amman ni dai naga yanzu idan ya dawo sai kaga duk ya rame,ko alokacin ma na tambayesa ko ba shida lafiya ne?amman sai ya ce min babu komai.kasan shi Bilal ba mutum ne me magana ba,ga miskilanci shiyasa ni ban gane konai ba". Ko da suka ga rashin faɗan rashin lafiyar Bilal zai iya janyo wata matsalar sai suka yanke shawarar kawai gwara su faɗa agida,don haryanxu bai farka ba,wai numfashinsa ne bai koma normal ba. Sosai gidan kowa ya ruɗe da rashin lafiyar Bilal,sai gasu sun cika asibiti kowa hankalinsa atashe Hajiya kaka sai kuka take tana ce wa"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Bilal sai da ka saka wannan damuwar aranka?yanzu gashi nan har ta kaika ga ƙwanciya a asibiti"?. Baba na ya ce"a'ah umma daman kinsan abinda ke damunsa"?.da sauri ta ce eh ƙwarai nasan abinda ke damunsa saboda ɗiyar wajenka khairat shiyasa duk hakan ta faru,to wallahi tallahi ka faɗawa ƴarka ta fitar min har jika na,tun kafin ranta ya yi masifar ɓaci". Da sauri baba na ya ce"a'ah Umma kin kullemin kai baki ɗaya?don Allah ki faɗamin wata ɗiya ta ce"?.da sauri ta kallesa sannan ta wurga masa harara ta ce"ban sani ba khairat ƴar wajenka ita na ke nufi,rannan da ta zo da mijinta tana da ciki ya riƙe mata jaka,kamar akanta aka fara ciki shine taga ɗan wajenta Audu Irfan kenan shine ta-yi ta-yi yazo wajenta ya ƙi zuwa,to shine fa daya ƙi zuwa ta ce wai ubansu ne ya zugasa,shine yaje ya gayawa uban nasa yazo,wallahi yarinyar nan khairat babu ko kunyar ƴan uwantaka ta buɗe bakinta ta zagesa tsaf zagi na rashin mutunci.har da ce wa wai ta tsanesa tsana mafi muni.to sai me don ta tsanesa ai muma muna sonsa don haka taje ta ƙarata.tabar ganin mijinta na bani kuɗi to duk ta banzar don ni a'i jika na yafi min wannan farar fatar wacce ke ruɗar ƴarka". Sosai abin ya yi wa kowa ciwo akan abinda khairat ta yi wa Bilal,Rashida taji nan da nan khairat ta sare mata akai,don ita tun kan yadda take zaginsu irfan ta fake da zaginsu alhali kuma Bilal ɗin take zagi sai taji duk ta sare mata aranta. Mamana da ke wajen ta sumkuyar da kanta don har zuciyarta ba taji daɗin abinda khairat ɗin ta yi wa Bilal ba,don ko babu komai ai ɗan uwanta ne uban ƴaƴanta,da ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87