Skip to content

Chapter 80

Chapter 80

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,282 words 0 views Progress saved
Download Book

kamar zai yi kuka ya ce"mamy wai ya ce ba jai jo ba.wai tunda bakyason dadynmu". Sosai na waro ido waje abin irfan yanxu mamaki ya ke bani,wato shi yafi son babanshi ko?abin ya tsayamin arai na gashi duk wajen da mutane,shahid ma yaji komai amman da ya ke shi mutum ne me haƙuri sai ya ce"Arman kada ka damu kaji Irfan zai xo shima zanxo in ɗaukesa".ya faɗi hakan yana mimmiƙa musu sweet da ya ke sun sanshi sai suka bishi suna ta bashi labarin dadynsu kaza da kaza. Abin ya tsayamin araina wato shi Bilal har yanzu ba zai daina son kansa ba ko?duk ya koyawa ƴaƴansa hali irin nashi,na ƙullatar mutum,na goge hawaye na waɗanda har sun fara zubowa.Anty halisa wacce tazo yanzu taji abinda ya faru ta dafa kafaɗa ta ta ce"don Allah khairat ki zama me dauriya mana.kome aka yi sai ki hau kuka?ai wataran ma sai ka nemi hawayen karasa ko?". Handcachep ta miƙomin wai in goge hawaye na,na saka na goge a hankali,na ɗaga idanuwa na kai tsaye suka sauka akan shahid wanda duk mode ɗinsa ya canja ganin halin dana ke ciki,ɗaga min gira ya yi yana murmushi nima murmushin na mayar masa. Anci ansha sosai walima ta yi daɗi sai dai fatan samun zaman lafiya.Maryam ce babu lafiya tana ta amai Shahid ya ce bari ya kira likita ya duba ta.gwajin farko ya tabbatar Maryam na da ciki har na tsahon wata uku.sosai wajen ya ruɗe da murna Allah kenan yau shekara uku kenan da aurenta har da ɗoriya.don tare aka yi mana auren farko. Sosai yaya Aliyu ke murna kamar zai komar da maryam ɗin cikinsa.Anty khadija ma yanzu cikinne da ita yaranta biyu yanzu da cikin na uku,bata san Maryam nada ciki ba,don sosai takewa maryam gori wai Aliyu ya auro juya shekara uku ko ɓatan wata,sai gashi yanzu Allah ya kawo lokacin wanda ita da kanta bata san ma tana da cikin ba. Kafin yamma kowa ya watse daga ni sai Anty Halisa sai maryam wacce ke ɗan hutawa kafin su tafi,sai ƴar uwar Ammi wacce da kaɗan ta fimu ƴar yayar ammin ce. Anty Halisa ta sakani agaba sai da na sake wanka,da ya ke har wankan tsarki zanyo tare da wasu sirrika waɗanda na har haɗa kuma ya kamata duk wata mace wacce ta gama al'ada ta yi sa. Ki dinga tsarki da ganyen magarya da kaninfari baysn gama al'ada yin hakan yana sakawa ki koma dai dai bayan gama haila,sannan ki samu misk ɗan asali da audiga ƴar kaɗan kina goge duk inda jinin ya taɓa.wannan yana ƙarawa mace kima sosai awajrn mijinta.kuma wannan ba sai matar aure ba hatta bazawara ko budurwa za ta iya yinsa. Zuwa dare kowa ya watse daga ni sai halina na kimtsa cikin doguwar rigar bacci wacce ta amsa sunanta na taje gashi na wanda yasha gyara da mai na gashi masu daɗin ƙamshi,da sanyaya zuciya. Fara ce ƙal rigar wacce ya ƙwantamin sosai kamar daman anyi tane saboda ni,na sanya hijabina na tada sallar magrib na ɗaga hannaye na sama ina godewa Allah da wannan ni'imar da ya yimin.na aurar salihin bawa irin Shahid na roƙi Allah ya rayamin yara na da al'ummar musulmi baki ɗaya,Allah kuma ya dawo da hankalin ɗana kai na don abin ya razanani sosai a ƙananan shekaru irin na Irfan wai har yasan ya ƙullace ni.na shafa addu'ar sai naji shahid ya ce"Amin". Da sauri na juyo ina kallonsa,yana sanye cikin pakistan irin wanda ƴan idia ke sakawa irin fari ƙal ɗinnan ya yi kyau sosai.na shagala a kallonsa sai kawai naji ya janyoni baki ɗaya na.ya ce"ni dai adaina kallona haka ƴan mata".ya faɗi hakan cikin salon yaudarata. Wani yarrr naji tun daga ƙafata har ƙwaƙwalwata na ce"ni ba kallon ka na ke ba.to ma da wani idon kasan ina kallonka"?.sosai na burgesa yadda na yi maganar cikin yana yi shagwaɓa ya lakato gefen kumatu na ya ce"Hayatee yaya ki keji da ki ka ganmu a matsayin mata da miji"?. Harararsa na yi nima cikin tsoka na ce"ni babu komai".ƙara janyo ni ya yi har muna jin numfashin juna daga nan fa salon ya canja. Sam Shahid bai da takura kuma yana da matuƙar haƙuri da bi da mace yadda ya kamata.bai matsamin akan komai sai abinda na ce,sosai muka raya darenmu cikin so da ƙaunar junanmu.kuma gaskiya jarumi ne sosai don ba ƙaramin gajiya na yi ba,shi kuwa har kuka ya yi saboda wani irin mugun daɗin dana jiyar dashi. Sai sakamin albarka ya ke,yana ganin babbar wautar da Bilal ya yi na saki na,don shi gani ya ke babbar wauta ce a saki mata iri na don na haɗu ta ko'ina,sosai Shahid ya mori kayarsa,nima sosai naji daɗin kasancewa dashi,don bashi da takura kamar yaya Bilal,shi shahid dai dai buƙata ne gashi da tausayi sai lallaɓani ya ke yana bani haƙuri kamar ya yimin laifi.ni abin nashi ma dariya ya bani. Rayuwa da shahid ya nunamin menene daɗin aure,menene shi kansa auren,ashe daman haka aure ya ke da daɗi?ashe ni da acen baya ba aure na yi ba?haƙiƙa sai yanzu shahid ya lasamin zumar aure.bani da matsalar komai agidansa don Ammi ma mutuniyar kirki ce babu ruwanta ko kaɗan. Na zaɓi in dinga yiwa miji na girki tare da gyara masa ɗakinsa,don ko ina na gidan ma'aikata na shiga su gyara ammanfa nan na yi musu iyaka ciki kuwa har da ɗakina. Na yi wani irin mugun kyau da fari,ashe dai nima farar ce ba baƙa ba?to me ya hanani yin fari dacen ɗin?".sosai na ke tambayar kai na musamman ma yanzu yadda na yi wata iriyar ƙiba musamman ma hips ɗina kamar an bubbuɗa ni. Ranar daren farko na Shahid ya yimin kyautar danƙareriyar mota,da kuɗi wanda kawai sai jin alert na yi,na duba na zaro ido alokacin shi kuma yana wajen amminsa na murza idona sannan na duba wani saƙo da ya turomin. "Hayatee dafatan kin tashi lafiya kada kiga ban tsaya awajenki ba.Ammi ce babu lafiya tun jiya da daddare.ilove u too my wife". Shafa saƙon na yi ina jin mugun ƙara son shahid har rai na. Na tashi kenan xan shiga banɗaki ya turo ƙofa ya shigo gabana ya yi mugun faɗuwa.tuno abinda ya faru na sunkuyar da kaina kunya ta isheni.ya ce"ayya meye kuma na kunya?munfa zama ɗaya kenan komai nawa ya zama naki.kin zama ni na zama ke don haka ni gaskiya bana son kunyar nan tana cutar dani. Ya faɗi hakan yana sungumata sai banɗaki,duk yadda naso wajen hanasa amman bai haƙura ba da kanshi ya ɗakkomin kayan dazan sanya wata doguwar rigace ta atamfa wacce ta yi matuƙar yimin kyau sosai. Da ya ke shahid na mugun son atamfa sosai,atare muka tafi dashi wajen Ammi ta rungumoni ina yi mata ya jiki ta ce"kai son yanzu sai da ka gaya mata?"ta faɗi hakan tana harararsa. Sosai rayuwarsu tak burgeni don su basa ɗaukar rayuwa da zafi gashi dai suna da kuɗin amman kuma babu ruwansu da wani saka ido ko wani abu. Ana cikin wannan ɗan yanayin ne na fara laulayi sosai,wannan karan tun watan farko ya nuna kansa,don ba kaɗan na sha wahala ba duk na yi sanyi babu yadda baiyi

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87